Ga wasu daga cikin ra'ayoyin ku kan yunƙurin Manchester United na ɗauko ɗan wasan tsakiyar Brighton, Carlos Baleba, bayan sun yi ƙoƙarin sayensa tun bara:
Dave: "Wannan dai kamar yanke shawara ne a mintinan ƙarshe! Na san an dade ana magana a kai kusan shekara guda, amma a cikin wannan shekarar bai yi wani abin a zo a gani ba. A ganina zaɓi ne mara kyau. Myles Lewis-Skelly ya fi Baleba a kusan dukkan fannoni, ko na ƙwallo ko na kuɗi. Kuma mafi muhimmanci, yana cikin ƙoshin lafiya. Baleba bai kai Andrey Santos ba, amma kuma ya fi shi tsada."
Howard: "Ina farin ciki da wannan. Muna buƙatar ƙarfin tsakiya kuma zai iya samar mana da hakan. Haka kuma yana son zuwa Manchester United, wanda abu ne mai kyau. Bai kamata mu mayar da hankali sosai kan rashin kyakkyawan kakar wasansa ta bara ba, domin hankalinsa ya rabu ne sakamakon batun canjin kulob. Ina ganin zai yi mana amfani sosai. Mu yi fatan yarjejeniyar ta tabbata, domin muna buƙatar ƙwararren ɗan wasan tsaron tsakiya irinsa."
Thomas: "Akwai 'yan wasa masu hazaka sosai da suka gaza a Manchester United, sannan akwai wasu da ba a yi musu wani tsammani ba amma suka yi fice. Abin da muke buƙata shi ne 'yan wasa masu ƙwarin hali da tunanin zakara. Idan yana da wannan, to yana da cikakken goyon bayana."
Mark: "Babban abin da ke damuna game da Baleba shi ne ko zai iya jure matsin lambar da ke Manchester United. Wasansa ya ragu sosai a kakar da ta gabata. Idan hakan ya faru ne saboda canjin da bai tabbata ba, to abin zai sa a yi tambaya kan ƙarfin halinsa. Idan kuma ba haka ba ne, to dole a tambayi dalilin da ya sa hakan ya faru da kuma ko zai iya dawo wa irin wannan bajintar."
Coops: "Na yi matuƙar mamakin wannan labari. Wani matsakaicin ɗan wasan tsakiya ne kuma, alhali muna matuƙar buƙatar sake gina tsaronmu. Maxence Lacroix, Ezri Konsa da Jan Paul van Hecke duk sun koma ƙungiyoyin hamayyarmu. Wata kasuwar saye da sayarwa mara kyau ce, duk da alkawuran da aka yi mana, kamar yadda aka saba!"