Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/08/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/08/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi da Aisha Babangida

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen shafin a wannan rana.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Amma kafin nan muke cewa mu kwana lafiya.

  2. MDD ta buƙaci Isra'ila ta gaggata bari a shigar da agaji Gaza

    Kowane memba na kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya in-banda Amurka ya ce yunwar da ake fama da ita a Gaza ɗan adam ne ya ƙirƙire ta, tare da yin kira ga Isra’ila ta gaggauta bari a shigar da agaji zuwa yankin.

    A cikin wani taron manema labarai na ba-zata, jakadun ƙasashe 14 na kwamitin sun tsaya bisa ra'ayi guda, suna gargaɗin Isra'ilar cewa amfani da yunwa a matsayin makamin yaƙi ya saɓa wa dokokin duniya.

    Sun kuma yi kiran tsagaita wuta nan take wadda za ta ɗore, sannan a saki duka Isra'ilawan da aka yi garkuwa da su, tare da buƙatar Isra’ilar ta soke ƙudirinta na kwace birnin Gaza.

  3. Mataimakin gwamnan Taraba ya koma aiki bayan shafe watanni yana jinya

    Mataimakin gwamna

    Asalin hoton, Aminu Alkali/X

    Mataimakin gwamnan jihar Taraba, Aminu Alkali ya koma bakin aikinsa bayan shafe wata tara yana jinya.

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce Alkali ya koma bakin aikinsa kodayake ba su ambaci takamaiman ranar da ya koma aikin ba.

    Bayanai sun ce mataimakin ya tafi jinya ne tun cikin watan Nuwamban 2024.

    A lokacin dogon hutun nasa, gwamnan jihar, Agbu Kefas ya naɗa shugaban ma'aikatan gidan gwamnati a matsayin wanda zai kula da ofishin mataimakin, wani mataki da ya janyo ce-ce-ku-ce a jihar, inda wasu ke gain tamkar maye gurbinsa gwamnan ya yi.

    Sai dai cikin wani jawabi da gwamnan ya yi ya ce shugaban ma'aikatan na aiki e na wucin gadi a ofishin mataimakin gwamnan domin tabbatar da aikin gwamnati.

  4. Yara bakwai na cikin mawuyacin hali bayan harin Amurka - Likita

    Shugaban sashen masu buƙatar kulawar gaggawa na asibitin Hennepin, Thomas Wyatt ya ce bakwai daga cikin yaran da aka kai asibitin bayan hari kan cocin da suek na cikin mawuyacin hali.

    ''Cikin yara bakwai da ke cikin mawuyacin hali, huɗu na buƙatar tiyata,'' in ji Dakta Wyatt.

    Tun da farko ƴansanda sun ce yara biyu ne ke cikin mawuyacin hali.

    Dakta Wyatt ya ce yaran ƴan shekara shida ne zuwa 14.

  5. Yara biyu sun mutu bayan wani mutum ya buɗe musu wuta a Amurka

    Wasu ƴansanda uku

    Asalin hoton, Reuters

    Rundunar ƴansandan jihar Minnesota ta tabbatar da mutuwar ƙanana yara biyu, bayan da wani ɗan bindiga ya buɗe wuta kan wani coci cike da ƙananan yara.

    Babban jami'in yansandan yankin O'Hara ya ce maharin na ɗauke da bindigogi uku a lokacin da ya ƙaddamar da harin.

    "Ƙananan yara biyu sun mutu, kuma tuni aka sanar wa iyayensu.''

    Ya ƙara da cewa wasu ƙarin mutum 17 sun ji raunuka, kuma 14 daga ciki ƙananan yara ne, wadnada tuni aka garzaya da su asibiti.

    Tuni dai ƴansanda suka sanar da mutuwar maharin.

  6. Sojojin Isra'ila sun ce ba makawa sai Falasɗinawa sun fice daga birnin Gaza

    Wasu Falasɗinawa a cikin motoci biyu, wasu har a sman motocin

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Sojojin Isra'ila na son mutane su fice daga birnin Gaza, kafin su kutsa cikinsa

    Rundunar sojin isra'ila ta shaida wa Falasɗinawa cewa ''babu makawa'' sai sun fice daga Birnin Gaza, yayin da dakarunta ke cikin far wa birnin.

    Cikin wata saƙo da kakakin rundunar na harshen Larabci, Avichay Adraee ya wallafa a shafinsa na X, ranar Laraba ya ce iyalan da suka koma kudancin birnin za su samu ''gagarumar tarba ta fuskar tallafi''.

    Cikin dare tankokin yaƙin Isra'ila sun kutsa zuwa wasu yankunan birnin, lamarin da ya tilasta wa mazauna birnin tserewa, kamar yadda shaidu suka bayyana.

    Tuni dai dubban mutane suka fice sakamakon hare-haren Isra'ila na baya-bayan, a wasu yankunan birnin, inda kusan Falasɗinawa miliyan guda ke zaune.

    Kiran na sojojin Isra'ilar na zuwa ne a yayin da ake sa ran Shugaban Amurka, Donald Trump zai jagoranci wani taro kan makomar Gazan a fadar White House.

    A farkon watan Agusta ne, Isra'ila ta ayyana shirin mamaye ilahirin Zirin Gaza - ciki har da birnin Gaza, da ta bayyana a matsayin wuri na ƙarshe da ya rage wa Hamas.

    Majalisar Dinkin Dniya ta ƙuniyoyi masu zaman kansu sun yi gargadin cewa hare-hare kan birnin Gaza zai ƙara ''ta'azzara matsalar jin ƙai''.

  7. Iran ta gargaɗi Australia kan korar jakadanta

    ...

    Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi kira ga Ostiraliya da ta sake tunani kan korar jakadanta, tana kiran matakin da “ba bisa ƙa’ida ba kuma ya saba da al’adar diflomasiyya.”

    Firaministan Ostiraliya, Anthony Albanese, ya ce hukumar leƙen asirin ƙasar ta tattara “ingantattun” bayanai da ke nuna cewa gwamnatin Iran tana da hannu wajen “shirya hare-hare biyu kan Yahudawa” a ƙasar lamarin da ya sa gwamnatin ƙasar bai wa jakadan Iran, Ahmad Sadeghi, da wasu jami’an ofishin jakadancin kwana bakwai su bar ƙasar.

    Iran ta musanta zargin, tana mai cewa yunkurin na Ostiraliya ya samo asali ne daga siyasar cikin gida.

    Ta kuma yi gargaɗin cewa idan Ostiraliya ba ta janye matakinta ba, za ta ɗauki matakan ramawa, abin da zai iya shafar al’ummar Iran da ke zaune a can.

    Iran ta kuma ce idan gwamnatin Ostiraliya ba ta sake tunani ba, Tehran na ganin cewa “gwamnatin Ostiraliya ce za ta ɗauki alhakin tasiri da sakamakon wannan mataki, ciki har da matsalolin da zai iya haifar wa al’ummar Iran masu ilimin da ke zaune a ƙasar.”

  8. An haramta wa jagoran adawar Tanzaniya takarar shugaban ƙasa

    ...

    Asalin hoton, ACT

    Hukumar zaɓen Tanzaniya ta haramta wa jagoran adawa ta jam'iyyar ACT-Wazalendo, Luhaga Mpina tsayawa takara a zaɓen shugabancin ƙasar.

    Hukumar zaɓen ta kuma soke wasiƙar da ta bayar a baya dangane da dawo da fom ɗin takara tare da hana shi shiga ofishin hukumar, yayin da jam’iyyarsa ta tabbatar da karɓar wasiƙar.

    Hukumar ta bayyana cewa tsayar da Mpina a matsayin ɗan takara ta sabon jam’iyyarsa bai cika sharuɗɗan doka ba, bayan ƙorafin da wata mamba ta jam’iyyar mai suna Monalisa Ndala ta shigar.

    A hukuncin da aka fitar ranar 26 ga watan Agusta, 2025, hukumar ta bayyana cewa Mpina bai cika ƙa’idar zama ɗan jam’iyyar ba, domin ya shiga jam’iyyar ACT-Wazalendo ne bayan lokacin da aka ƙayyade, don haka bai cancanci tsayawa takarar shugabancin ƙasa ta wannan jam’iyya ba.

    A cewar korafin da Monalisa ta shigar, ɗan takarar ya karya dokokin tsarin mulkin jam’iyyar ACT-Wazalendo domin bai kasance memba a jam’iyyar ba tsawon kwana bakwai kafin a fara tsarin tantance ’yan takara.

  9. Firaministan Guinea-Bissau ya yanke jiki ya faɗi a wurin taro

    Firaministan Guinea-Bissau, Braima Camará, ya yanke jiki ya faɗi yayin bikin rantsar da sabon kwamitin majalisar jihar a babban birnin ƙasar ranar Talata.

    An garzaya da shi asibiti a Dakar a jirgin saman sojojin Senegal domin samun kulawar lafiya, inda ake cewa ba shi da matsala mai tsanani.

    Camará, mai shekara 57, ya fara aiki ne a watan nan, kuma naɗinsa a matsayin firaminista ya jawo ce-ce-ku-ce a siyasa.

  10. 'Yara 200,000 ka iya kamuwa da polio idan Birtaniya ta janye tallafi'

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar ONE ta gargaɗi gwamnatin Birtaniya da cewa yara 200,00 ka iya kamuwa da cutar mutuwar ɓarin jiki a kowace shekara cikin shekaru goma masu zuwa idan har ta dakatar da tallafin da ake bayarwa na yaƙi da cutar shan-inna wato polio a duniya.

    Tun daga shekarar 1980, aikin rigakafin shan-inna ya rage yawan yara da cutar ke shafar su da kashi 99.9 kusan an kawar da cutar gaba daya kenan.

    Cutar ta daina bayyana a Turai da Amurka tun shekaru da dama da suka wuce, amma a shekarar 2025, ana ci gaba da samun yara da ke samun mutuwar ɓarin jiki a Pakistan da Afghanistan da wasu sassan Afirka da Asiya, tare da ɓullowar cutar a wuraren rikici kamar Gaza da Sudan.

    Ko a Birtaniya, an gano kwayar cutar shan-inna a ruwan sharar birnin England a wannan shekara, abin da ke nuna cewa ci gaban da aka samu yana da rauni, kuma babu kasa da za ta iya jin dadin lafiya har sai an kawar da cutar a ko’ina.

  11. Tinubu ya haramta fitar da kaɗanya daga Najeriya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bayar da umarnin dakatar da fitar da ɗanyen man kaɗe daga ƙasar na tsawon watanni shida domin ƙarfafa sarrafa shi a cikin gida da bunƙasa harkar masana’antar man kaɗen wanda kashi 95 na masu sarrafawa mata ne.

    Tinubu ya bayyana kaɗe a matsayin 'arziƙin Najeriya da ke cikin daji'.

    Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ne ya sanar da matakin a wurin taron masu ruwa da tsaki daga ɓangarori daban-daban a Abuja' kuma shi ne zai jagoranci kwamiti na musamman da aka kafa domin faɗaɗa shirin sarrafa kaɗe cikin gaggawa

    Kashim ya ce wannan ba mataki ne na kawo cikas ga harkokin cinikayya ba, sai dai an ɗauki matakin ne domin samar da daraja ga ƙasar da ƙara samar da ayyukan yi da kuma ƙara kuɗaɗen shiga.

    Najeriya na daga cikin ƙasashe mafiya samar da kaɗe a duniya, musamman a jihohin Neja da Kwara da Oyo inda take samar da kusan kashi 40 na ɗanyen man kaɗe a duniya, amma tana da kashi ɗaya ne kacal a kasuwar da darajarta ta kai dala biliyan 6.5.

    Gwamnati ta kuma ce ana fitar da kusan tan 90,000 na kaɗe ba bisa ƙa’ida ba a kowace shekara, abin da ke sa masana’antun cikin gida gaza yin aiki yadda ya kamata.

    Mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa "Matakin zai iya samar da dala miliyan 300 duk shekara a nan gaba kaɗan tare da nufin nunka hakan nan da shekara ta 2027.

  12. Na ɗauki alhakin hatsarin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna - shugaban NRC

    ...

    Asalin hoton, BBC Hausa

    Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa, ya ce ya ɗauki alhakin hatsarin jirgin ƙasa da aka samu ranar Talata, wanda aka samu lokacin da jirgin ya kama hanya daga Abuja babban birnin ƙasar zuwa Kaduna.

    A tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels, Opeifa ya ce ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen binciken abin da ya sanya jirgin ya kauce daga kan layi.

    “Bayan neman gafarar ƴan Najeriya, a matsayina na shugaban hukumar, na ɗauki cikakken alhakin abin da ya faru,” in ji shi.

    Opeifa ya tabbatar da cewa duk da cewa hatsarin bai kamata ya faru ba, NRC za ta tabbatar hakan bai sake faruwa ba.

    Hatsarin ya faru ne a ranar Talata bayan jirgin ya tashi daga Abuja da misalin ƙarfe 11 na safe kan hanyar zuwa Kaduna da ke arewacin Najeriya, lamarin da ya jefa fasinjoji cikin da ruɗani da tsoro.

    Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya ta ce hatsarin ya jikkata mutum bakwai, waɗanda suka samu kulawar malaman lafiya.

    Jirgin saman Abuja zuwa Kaduna ya yi ƙaurin suna kan samu tangarɗa a kai a kai.

    A bara jirgin ya samu tangarɗa a kusa da garin Jere, sai dai babu wani fasinja da ya jikkata, haka nan ma an samu irin haka a 2023 a kusa da tashar jirgin ƙasa ta Kubwa.

    Tangarda mafi muni da jirgin ya samu a tarihinsa shi ne lokacin da aka tsayar da ayyukansa na tsawon wata shida a shekara ta 2022 bayan da wasu gungun yan bindiga suka kai masa farmaki tare da yin garkuwa da kimanin mutum 60.

    A shekara ta 2016 ne aka ƙaddamar da sufurin jirgin ƙasan daga Abuja zuwa Kaduna mai nisan kilomita 186 domin samar wa matafiya zaɓi daga bin hanyar mota, lokacin da ake fama da matsalar tsaro ta ƴan bindiga masu tare hanya suna garkuwa da mutane.

  13. Harsuna 10 da Hausa ke barazanar shafe su a arewacin Najeriya

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Harshen Hausa ya kusan mamaye duka fannonin sadarwa a yankin arewacin Najeriya.

    Ana magana da harshen a ƙauyuka da garuruwa da kasuwanni da makarantu da kafafen yaɗa labarai da sauran hulɗoɗin yau da kullum.

    Wannan ya sanya Hausa ta zama harshe mafi rinjaye da mutane daga ƙabilu daban-daban ke amfani da shi wajen mu'amala da juna wanda hakan ya saka wasu ƙananan harsunan asali da dama ke fuskantar barazanar ɓacewa daga gare shi.

    Dalilin haka ne BBC ta tuntuɓi Dakta Ibrahim Ahmed Birnin Gwari, malami a shashen nazarin harsunan Najeriya da kimiyyar harshe a jami'ar Kaduna domin samun ƙarin haske kan wannan batu.

  14. Shugaban Senegal zai ziyarci Faransa domin ganawa da Macron

  15. An fara bincike kan hatsarin jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna

  16. Hukumar IAEA ta sanar da shirin dawo da masu sa ido kan nukiliya a Iran