Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya, Litinin, 03/03/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sassan duniya kai tsaye, na Litinin, 03/03/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Umar Mikail

  1. Jihar Rivers za ta sake zaɓen ƙananan hukumomi bayan hukuncin kotun ƙoli

    Gwamnan jihar Rivers, Siminalaya Fubara ya ce za su yi amfani da hukuncin da kotun ƙoli ta yanke kan sahihancin shugabancin majalisar dokokin jihar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar.

    A ranar Juma'a ce kotun ƙolin ta rushe zaɓen ƙananan hukumomin jihar, sannan ta ce tsagin Martin Chike Amaewhule, wanda ke tare da Ministan Abuja, Nyesome Wike ne sahihin shugaban majalisar, inda ta buƙaci babban bankin Najeriya ya dakata da ba jihar kasonta na tarayya har sai gwamnan ya gabatar da kasafi a gaban majalisar.

    "Muna bin doka da oda, duk da cewa za mu iya yin kuskure a matsayinmu na ƴan'adam. Kasancewar hukuncin kotu ya rushe zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumominmu, ina umartar dukkansu su miƙa aiki ga shugabannin aikace-aikace na ƙananan hukumomi, waɗanda za su yi riƙo kafin a sake gudanar da sabon zaɓe."

    Ya yi kira ga ƴan jihar su kwantar da hankalinsu, tare da cigaba da gudanar da ayyukansu ba tare da tashin hankali ba.

  2. Za mu yi ƙoƙarin sulhunta Kwankwaso da Ganduje da Shekarau - Zaura

    Tsohon ɗan takarar kujerar sanatan Kano ta Tsakiya, Alhaji Abdulsalam Abdulkarim Zaura ya ce za su yi duk mai yiwuwa domin ganin sun sulhunta tsakanin jagororin siyasar jihar: Rabiu Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje da Ibrahim Shekarau.

    Zaura ya ce haɗin kan manyan jagororin zai taimaka wajen gyara siyasar jihar, tare da samar da cigaba ta yadda jihar za ta yi gogayya da jihar Legas da wasu jihohin da suka ci gaba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Zaura ya ce, "irin adawar siyasa da ake yi a Kano ba ta da amfani. A shirye nake in shige gaba wajen samar da maslaha tsakanin Kwankwaso da Ganduje da Shekarau. Ya kamata mu fifita ci gaban Kano sama da son ranmu. Da zarar an samu wannan nasarar, Legas da sauran jihohi sai sun yi koyi da Kano wajen siyasa ta hankali da ci gaba."

    A baya Abdulmumin Jibrin Kofa da Murtala Sule Garo da Baffa Babba Danagundi duk sun bayyana irin buƙatar a lokuta daban-daban.

  3. Ƙasashen Larabawa sun soki Isra'ila kan hana shigar da kayan agaji Gaza

    Gwamnatocin ƙasashen Larabawa da suka taimaka wajen shiga tsakani don tabbatar da tsagaita wuta a Gaza sun yi kakkausar suka ga matakin da Isra'ila ta ɗauka na hana kayan agaji shiga zirin Gaza.

    Qatar ta ce Isra'ila ta keta yarjejeniyar da aka cimma a watan Janairu ta kuma yi wa dokokin jin ƙai na ƙasa da ƙasa karan-tsaye.

    Wakilin BBc ya ce Isra'ila ta ce dole ne ci gaban tsagaita wutar ya ƙunshi sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.

    An rawaito cewa, tana shirin bai wa Hamas ‘ƴn kwanaki don gabatar da wani sabon tsari da za a amince da shi, ko kuma Isra’ila za ta ci gaba da yaƙi a Gaza.

  4. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu ɗaura daga inda muka tsaya na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya kai-tsaye.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.