Abin da muka sani kan 'sace mutum 160' a Kaduna
Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce babu gaskiya a rahotannin da ake yaɗawa na garkuwa da sama da mutane 160 a wasu coci-coci da ke ƙauyen Kurmin Wali a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.
Rundunar ta ce wasu marasa kishi ne ke yaɗa wannan labari da nufin tayar da hankalin jama'a.
A ranar Litinin jaridun Najeriya da dama sun bayar da rahoton sace mutane fiye da 100 a wuraren ibadah daban-daban na ƙauyen Kurmin Wali, inda suka ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi 18 ga watan Janairu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban ƙungiyar kiristoci ta Najeriya CAN, reshen jihar Kaduna Reberan Joseph John Hayab ya tabbatar mata da aukuwar lamarin, in da ya ce: "duk da cewa ban cika son ambata adadi ba, amma bayanan da na samu daga yankin na nuna cewa ƴanbindiga sun sace kusan mutum 172, amma guda 9 sun tsere sun koma gida, amma har yanzu ana neman mutum 163,"
Amma rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce har yanzu babu wasu bayanai da suka tabbatar da cewar an ɗauke mutanen.