Habasha da Somalia sun cimma matsaya kan taƙaddamar Somaliland
Ƙasashen Habasha da Somaliya sun cimma matsaya don kawo ƙarshen takaddamar da ke tsakaninsu bayan wata tattaunawa da suka yi a Ankara babban birnin kasar Turkiyya.
Shugaban Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud ya ce ƙasarsa a shirye take ta yi aiki tare da Habasha.
Ya ce ''Muna da damar haɗa hannu da juna don ci gaba tare da kuma biyan buƙatunmu''.
Somaliya za ta ba da gudummawa wurin cimma hakan kuma a shirye muke mu yi aiki tare da shugabanni da kuma al'ummar Habasha.
Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya yi maraba da yarjejeniyar mai cike da tarihi.
Firaiministan Habasha, Abiy Ahmed da shugaban Somalia, Hassan Sheikh Mohamud, sun amince za su mutumta ƴancin kowanne ɓangare.
Ƙasashen biyu maƙwabtan juna sun shiga taƙaddama ne tun a watan Janairu, lokacin da Habasha ta ƙulla yarjejeniyar alaƙa da Somaliland ta ruwa, yankin da Somalia ke yi wa kallon wani ɓangare na ƙasar ta.