Rufewa
A nan muka kawo ƙarshen kawo muku labaran kai-tsaye. Da fatan kun ji daɗin kasance da mu.
Sai kuma gobe Juma' idan Allah ya nuna mana.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/12/2024
Haruna Ibrahim Kakangi, Abdullahi Bello Diginza da Badamasi Abdulƙadir Muktar
A nan muka kawo ƙarshen kawo muku labaran kai-tsaye. Da fatan kun ji daɗin kasance da mu.
Sai kuma gobe Juma' idan Allah ya nuna mana.
Sabuwar gwamnatin Siriya ta dakatar da majalisar ƙasar, da kuma jingine kundin tsarin mulkin ƙasar na tsawon wata uku.
Gwamnatin ta ce ta yi haka ne domin amsar mulki cikin sauƙi bayan da ta hamɓarar da tsohuwar gwamnatin Bashar al-Assad.
Mai magana da yawun gwamnatin ya ce, za a kafa kwamitin da zai yi wa tsarin mulkin garambawul.
Ya kuma ƙara da cewa babbancin al'adu da addini na Siriya ba zai zama barazana ga ƙasar ba.
Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce mayaƙan Boko Haram da iyalansu 129,417 ne suka miƙa wuya a tsakanin 10 ga Yuli zuwa 9 ga Disamban 2024.
Babban hafsan ya bayyana hakan ne a wani taron ƙasashen Afirka mai alaƙa da tsaro da ke gudana a Doha babban birnin Qatar.
Rikicin Boko Haram dai ya daɗe yana cin mutane, musammn a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Majalisar dattawa ta Zimbabwe ta kaɗa ƙuri'a, inda ta amince da ƙudurin hana yanke hukuncin kisa a ƙasar,
Yanzu ƙudurin na jiran sa hannun shugaban ƙasa Emmerson Mnangagwa ne domin zama doka.
Kafin wannan dokar, kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanadi hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Duk da cewa hukuncin kisa na ƙarshe da aka tabbatar a ƙasar shi ne a shekarar 2005, har yanzu kotuna na ci gaba da yanke hukuncin kisa.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam sun yaba da matakin, inda suka ce hakan ya nuna yadda ake mutumta ɗan'adam a ƙasar ta Zimbabwe.
Majalisar dokokin jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya ta amince da ƙudurin dokar kafa masarautu uku masu daraja ta ɗaya a jihar.
Amincewa da ƙundirin - wanda a yanzu ke jiran sa hannun gwamnan jihar, Ahmadu Finitiri - na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan gwamnan ya sa hannu kan wata dokar ta ƙirƙirar sabbin gundumomin hakimai 84 da aka yi ranar 4 ga watan Disamba.
A wata wasiƙa da gwamna da aika wa majalisar, a farkon mako ya buƙaci ƴanmajalisar su amince da ƙudirin naɗawa da cire sarakuna a jihar, wadda za ta ba gwamnan damar ƙirƙirar sababbin masarautu da naɗa sarakuna ko kuma cire su.
Oborevwori ya soki cire tallafin man fetur da shugaban ya yi, idam ma cire fetur ɗin na da, to karya darajar naira ta lalata komai, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin watsa labari, Felix Ofou ya fitar, a matsayin mayar da martani ga tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege.
A wani taron APC da aka yi a jihar ne Omo-Agege ya yaba da matakan gyara tattlin arziki da gwamnatin Tinubu ke ɗauka, inda ya ce hakan ya sa jihohi sun samu ƙarin kuɗaɗe daga asusun tarayya.
Shugabar jam’iyyar Conservative a Burtaniya Kemi Badenoch, ta ce ba abin da ya sauya kan kalaman da ta yi a baya game da Najeriya, bayan da mataimakin shugaban ƙasar Naijeriya, Kassim Shattim ya zarge ta da tozarta ƙasarta ta asali.
Shugabar jam’iyyar, wacce haifaffiyar Birtaniya ce amma ta tashi a Najeriya, ta sha bayyana ƙasar a matsayin ƙasar da ke tattare da abubuwan da suka shafi rashin tsaro da rashin tabbas sakamakon matsalar cin hanci da rashawa.
A ranar Litinin, mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya ba Badenoch shawarar "ta cire Kemi daga sunanta" idan ba ta alfahari da ƙasarta ta asali.
Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanar da gyare-gyare a majalisar zartarwar jihar, inda ya cire wasu, sannan ya sauya wa wasu ma'aikatu.
A wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar, ya ce gwamnan ya soke ofishin shugaban ma'aikatan gidan gwamnati, wanda Alhaji Shehu Wada Sagagi ke riƙewa, sannan ya cire sakataren gwamnatin jihar, Dokta Baffa Bichi saboda rashin lafiya.
Sanarwar ta ce gwamnan ya cire kwamishinoni guda biyar: Ibrahim Jibril Fagge na ma'aikatar kuɗi da Ladidi Ibrahim Garko ta ma'aikatar al'adu da yawon buɗe ido da Baba Halilu Dantiye na ma'aikatar watsa labarai da Shehu Aliyu Yammedi na ma'aikatar ayyuka na musamman da Abbas Sani Abbas na ma'aikatar raya karkara.
Sanarwar ta ce gwamnan ya yi sauye-sauyen ne domin inganta aikin gwamnati, da kuma taimaka wa gwamnan wajen kai romon dimokuraɗiyya ga ƴan jihar.
Haka kuma gwamnan ya yi wa wasu kwamishinonin sauyin ma'aikatu, waɗanda suka haɗa da: "mataimakin gwamnan jihar, wanda aka sauya masa ma'aikata daga ƙananan hukumomi zuwa ma'aikatar ilimi mai zurfi, da Mohammad Tajo Usman daga ma'aikatar kimiyya da fasaha zuwa ma'aikatar ƙananan hukumomi, da Dr Yusuf Ibrahim Ƙofar Mata daga m'aikatar ilimi mai zurfi zuwa kimiyya da fasaha."
Sauran sun haɗa: "Hajiya Amina Abdullahi daga ma'aikatar jinƙai da rage talauci zuwa ma'aikatar mata, da Nasiru Sule Garo daga ma'aikatar muhalli da sauyin yanayi zuwa ma'aikatar ayyuka na musamman da Haruna Doguwa daga ma'aikatar ilimi zuwa ma'aikatar albarkatun ruwa da Ali Haruna Makoda daga ma'aikatar albarkatun ruwa zuwa ma'aikatar ilimi da Aisha Lawal Saji da aka mayar m'aikatar al'adu da yawon buɗe ido."
Sai dai gwamnan ya buƙaci waɗanda aka cire ɗin su je ofishinsa domin a ba su wasu ayyukan daban.
A ranar Talata, 17 ga watan Disamba ne shugaban ƙasa Bola Tinubu zai gabatar da kasafin kuɗin Najeriya na shekarar 2025 a gaban ƴan majalisar dattawa da wakilai.
Shugaban majalisar dattawa,Sanata Godswill Akpabio ne ya sanar da hakan a zauren majalisar, a ranar Alhamis, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito
Akpabio ya ce za a gudanar zaman sauraron gabatar da kasafin ne a zauren majalisar wakilai na ƙasar a Abuja.
Ma'aikatan lafiya a Gaza sun ce hare-haren Isra'ila na baya-bayan nan sun kashe Falasdinawa masu gadin kayan agajin da ake shigarwa.
Ma'aikatan 12 na cikin Falasdinawa 35 da aka kashe cikin daren jiya a Gaza.
Suna bayar da kariya ne ga manyan motocin kayan agaji daga ɓarayi da Majalisar Dinkin Duniya ta ce na haifar da tsaiko wajen shigar da kayan zuwa gabashin Gaza.
Wakiliyar BBC ta ce ministan tsaron Isra'ila ya shaida wa takwaransa na Amurka cewa akwai yiwuwar cimma yarjejeniyar sakin wadanda aka yi garkuwa da su ciki har da Amurkawa.
Jihar Quesland ta Australai ta zartar da wata doka da za ta bayar da damar aiwatar da hukuncin ɗauri a gidan yari kan ƙananan yara ƴan shekara 10, idan aka same su da aikata manyan laifuka kamar kisan kai da mummunan hari.
Gwamnati ta ce ta amince da dokar ne domin yin tanadin hukunci mai tsauri ga ƙananan yara ake yawa samu da aikata irin waɗannan laifuka.
Amma ƙwararru sun ja hankali cewa bincike ya nuna yadda zartar da hukunci mai tsauri a kan ƙananan yara da matasa ke ƙara kangarar da su, a madadin gyara masu hali.
Majalisar Dinkin Duniya ma ta yi allawadai da gyaran dokar, inda ta ce ya saɓawa tanadin dokar ƙasa da ƙasa a kan kare ƴancin yara da matasa.
Jam'iyyar Liberal National Party (LNP) wadda ta lashe zaɓe a watan Oktoba ta yi yaƙin neman zaɓe da ƙudirin dokar, tana mai cewa tana fifita ƴancin wanda aka yi wa laifi fiye da na masu aikata laifi.
Jim kaɗan bayan zartar da dokar a yau Alhamis, Firimiyan yankin, David Crisafulli ya ce dokar ci gaba ce ga duk wani ɗan Queensland wanda ke zaman zullumi saboda tsaron kada matasa su aikata laifi a kan su.
Gwamnatin mulkin soja ta Nijar ta musanta rahotannin da ke cewa an kashe sama da sojoji 90 a yankin Tera na ƙasar, inda ta bayyana cewa sojojinta 10 ne aka yi jana'iza.
Sai dai a sanarwar da aka karanta ta kafar talabijin ɗin ƙasar da yammacin ranar Laraba, ba ta bayyana ainahin yawan sojojin da suka rasa ransu ba a lokacin harin.
Tun farko rahotanni sun ce harin na Tera ya haifar da asarar sojojin ƙasar sama da 90 da kuma fararen hula kimanin 50.
Inda rahoton ya ce ƴan bindiga sun kai hare-hare biyu a ƙauyen Chatoumane da ke Tera a yankin Anzourou a ranar Talata, inda suka kashe sojoji da kuma fararen hula.
Jamhuriyar Nijar na ci gaba da fuskantar harin ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.
Hare-hare kan fararen hula na ci gaba da yawaita, inda suke yaɗuwa daga jihar Tillaberi zuwa Dosso da kuma Tahoua.
A ranar Laraba wasu da ake zargin ƙungiyoyin mayaƙa ne sun kai hari ka ƙauyen Mountseka, inda suka afka wa mutane a kan babura.
A wani lamarin kuma, wasu da ake zargin masu iƙirarin jihadi na ƙungiyar IS ne sun kai hari a kan Libiri, wani ƙauye da ke kusa da garin Samira a yammacin ƙasar.
Rahotanni sun ce an ƙona ƙauyen kuma an kashe fararen hula da dama.
Sai dai hukumomin mulkin sojin Nijar basu tabbatar ko musanta wannan rahoton ba.
A lardin Arewacin Sumatra na ƙasar Indonesiya, al'ummar Batak na yin taron Mangongkal Holi, wata al'ada inda mutane ke taruwa su haƙo rage-ragen ƙasusuwan iyaye da kakanni tare da sauya musu waje domin ɗorewar tarihin tsatsonsu.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Human Rights Watch ta zargi sojin Mali da kuma sojojin hayar Rasha da cin zarafin fararen hula bayan ficewar dakarun Majalisar Dinkin Duniya daga Malin a bara.
Ƙungiyar ta ce sojojin sun kashe fararen hula 32 da gangan a lokacin da suke yaƙi da ƙungiyoyi masu tsautsauran ra'ayin Islama.
Human Rights Watch ta ce sojin Malin, da kuma sojojin haya na Wagner da fadar Kremlin ke goyon baya sun kashe fararen hula, ciki harda ƙananan yara a wasu hare-haren jirage marasa matuƙi, da garkuwa da mutane da kuma ƙona gidaje da dama a Mali.
Ƙungiya ta kuma zargi ƙungiyoyi masu alaƙa da Al-Qaeda da kisan gomman fararen hula da ƙona dubban gidaje a Malin.
Shugaba Biden ya yi sassaucin hukunci a kan mutane 1,500 a wani mataki da ba a taɓa yin irin shi ba a tarihin Amurka.
Mafi yawan su mutane ne da aka saki daga gidan yari a lokacin annobar korona, kuma ake ci gaba da yi masu ɗaurin talala a gidajensu.
Akwai kuma Amurkawa 39 da aka ƴanta daga zaman gidan yarin.
Daga cikin su akwai mutanen da aka samu da ƙananan laifuka, ciki harda waɗanda aka kama da tabar wiwi.
Akwai tsofaffin jami'an soji da aka kama da karya tsoffin dokokin aikin soji da suka haramta luwaɗi.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken ya isa Jordan domin tattauna yadda za a kafa gwamnati a Syria bayan hamɓarar da gwamnatin Bashar al-Assad.
Kakakin Mr Blinken ya ce yana ziyarar ne domin jaddada goyon bayan Amurka ga shirin kafa gwamnatin da za ta yi tafiya da kowa da kuma cikin gaskiya da adalci.
Ƙungiyar Hayat Tahrir al-Sham da ta ƙwace mulki a Syria ma tana cikin ƙungiyoyin da Amurka ta sanya sunansu a jerin ƙungiyoyin ta'addanci, kuma kimanin shekara 10 kenan dakarun Amurka na gudanar da aiki a arewa maso gabashin Syria.
Mr Blinken zai gana da sarki Abdallah na Jordan kafin ya zarce Turkiyya.
Ana sa ran batun Syria da goyon bayan Ukraine za su mamaye taron ministocin harkokin wajen ƙungiyar tarayyar Turai da za a yi a Berlin.
Shugabannin ƙasashen Turai sun bayyana kawo ƙarshen mulkin Assad a Syria, a matsayin labari mai kyau ga ƙasar amma sun buƙaci a yi taka-tsantsan game da batun.
Ministocin za su mayar da hankali kan yadda za a ci gaba da taimakawa Ukaine da kuɗi da kuma makamai a yaƙin da take yi da Rasha.
Akwai fargabar cewa Amurka za ta janye daga matsayin ta na wadda tafi bai wa Ukraine tallafi a yaƙin, idan Donald Trump ya karɓi mulki a wata mai zuwa.