Saudiyya za ta biya wa Syria bashin da Bankin Duniya ke bin ta
Rahotanni na cewa Saudiyya na shirin biyan bashin da Bankin Duniya ke bin ƙasar Syria, a wani matakin farko na taimakon sabuwar gwamnatin Syria tsayawa da kafarta.
Bankin duniya na bin Syria bashin dala miliyan 50, biyan bashin zai bai wa ƙasar damar samun tallafin don sake gina ƙasar, ciki har da gyara wutar lantarkin da yaƙi ya ɗaiɗai ta.
A watan Janairun bana, Amurka ta ɗauke wa Syria takunkumin watanni shida - domin ba da damar kai agaji ƙasar, sai dai kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa wannan ba lallai ya yi tasiri ba.