Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/04/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Ahmad Bawage da Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Nan za mu rufe wannan shafi na ranar Talata.

    Mu haɗu da ku gobe domin samun sababbin rahotonni daga sassan duniya.

  2. Hamas ta ce ta kasa jin ɗuriyar wata rundunarta a Gaza da ke tsare da ɗan Amurka

    Hamas ta ce ta kasa jin duriyar mayakanta da ke tsare da Edan Alexander, wani ɗan Amurka da take rike da shi.

    Mai magana da yawun mayakan Hamas ya ce tun bayan da Isra'ila ta kai hari ta sama kan wurin da ake tsare da mutumin.

    Mista Alexander ya bayyana cikin wasu bidiyo biyu da Hamas ta wallafa inda aka gan shi cikin mawuyacin yanayi.

    Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ziyarci dakarunsa da ke Gaza a yayin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta kan 'yan Hamas.

  3. Faransa ta kori jakadun Aljeriya 12 daga ƙasarta

    Faransa ta kori wasu jami'ai 'yan kasar Aljeriya 12 tare da yi wa jakadanta a ƙasar kiranye.

    Matakin na zuwa ne bayan Aljeriya ta kori ma'aikata a ofishin jakadancin Faransa na ƙasarta, abin da ya kara jawo rashin fahimta a tsakanin kasashen biyu.

    Dangantaka tsakanin Faransa da Aljeriya ta fara tsami a bara sakamakon goyon bayan Morocco da Faransa ta yi a kan wani yanki da suke fada a kai da ke yammacin Sahara.

  4. Sojin Sudan sun ce sun fatattaki dakarun RSF daga el-Fasher

    Rundunar sojin Sudan sun ce sun tarwatsa matsugunar mayaƙan RSF da ke wajen birnin el-Fasher, babban birnin arewacin Darfur.

    Dubban mutane ne suka tsere wa sansanin 'yan gudun hijira na Zamzam, wanda dakarun RSF suka ƙwace iko a ranar Lahadi.

    Akwai damuwar da ake nunawa game da halin ayyukan jin ƙai a wuri na karshe da dakarun suke a Darfur.

    Kungiyar likitocin agaji ta Medicins Sans Frontiers ta ce dubban mutanen da suka bar sansanin na Zamzam sun yi tafiya kilomita 70 da kafa zuwa garin Tawila.

    Wakiliyar BBC ta ce akwai mata da yara da tuni suke a galabaice saboda tuni aka ayyana yunwa a sansanin na Zamzam a watan Augustan bara.

    Wani taro da aka gudanar a birnin Landan ya yi kira da a gaggauta tsagaita wuta a Sudan.

  5. Majalisar Wakilan Najeriya ta kafa kwamatin kula da mulkin jihar Rivers

    Majalisar Wakilan Najeriya ta kafa tare da rantsar da kwamatin da zai kula da harkokin mulki a jihar Rivers da ke kudancin ƙasar.

    Kakakin Majalisa Tajudeen Abbas ya ce kwamatin na wucin gadi mai mamba 21 zai yi aiki kai-tsaye da gwamnan riƙo "kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada".

    Majalisar ta kafa kwamatin ne bayan Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya saka dokar ta-ɓaci wadda ta dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da majalisar dokokin jihar saboda abin da ya kira "rushewar doka da oda".

    'Yan adawa na zargin cewa Tinubu ya kafa dokar ne saboda rikicin siyasar da gwamnan na jam'iyyar PDP mai adawa yake yi da Ministan Abuja Nyesom Wike, wanda ke ɗasawa da gwamnatin Tinubu ta APC.

    "Sakamakon dakatar da gwamna da majalisar dokoki...an naɗa Ibok-Ete Ibas mai ritaya a matsayin kantoma kuma yanzu zai dinga karɓar umarni kai-tsaye daga wajenmu kamar yadda kundin mulki ya tanada," in ji kakakin cikin wani saƙo a dandalin X.

  6. Masu zanga-zanga sun farfasa ofishin CBEX a jihar Oyo

    Masu zanga-zanga sun farfasa ofishin CBEX na birnin Ibadan a jihar Oyo da ke kudancin Najeriya, kamar yadda rahoton Channels TV ya ruwaito.

    A yau Talata ne masu zuba jari a kamfanin da ke karɓar kuɗaɗen mutane don kasuwanci suka dinga bayyana damuwa cewa an hana su taɓa kuɗaɗensu daga kan manhajar.

    Rahoton ya ce zanga-zangar ta yi ƙamari lokacin da mutane suka lura an kwashe duka kuɗaɗen da suka zuba a asusunsu na manhajar.

    Wasu rahotonni sun ce an lakaɗa wa wasu ma'aikatan kamfanin duka lokacin da masu zanga-zangar suka kutsa ginin.

    CBEX wani tsarin zuba jari ne ta intanet da ke ninka wa mutane kuɗin da suka zuba cikin wata guda, suna kuma samun ƙarin kudi idan suka kawo wani cikin harkar.

  7. Hamas ta yi watsi da tayin tsagaita wuta na Isra'ila

    Majiyoyi sun ruwaito cewa Hamas ta yi watsi da ƙudirin neman tsagaita wuta da Isra'ila gabatar na mako shida a Zirin Gaza.

    Daftarin da Isra'ilar ta gabatar ya nemi Hamas ta zubar da makamanta a matsayin sharaɗin dakatar da hare-hare.

    Wani babban jami'in Hamas da yake da masaniya kan lamarin ya ce daftarin bai yi bayani game kawo ƙarshen yaƙi baki ɗaya ba a madadin sakin rabin Isra'ilawan da Hamas ke riƙe da su.

    Isra'ilar na ci gaba da kai hare-hare a Gaza, inda ta kashe wani mai gadi da raunata mutum tara a harin da ta kai kan wani asibiti a yankin Khan Younis a yau Talata, in ji asibitin.

  8. An kai hare-hare gidajen yarin Faransa

    An kai wa gidajen yari da dama hari a Faransa a wani hari da aka tsara.

    An cinna wa motoci wuta a wuraren ajiye motoci na gidajen yarin da ke biranen Paris da Valence da kuma na yankin Aix-en.

    Kaza-lika an kai hari a mashigar gidan yarin da ke Toulon.

    Ministan shari'a na ƙasar Gerald Darmanin, ya kai ziyara Toulon, a wani ɓangare na nuna goyon baya ga masu tsaron gidan yarin.

    Ƙungiyar masu tsaron gidan yarin sun buƙaci a ƙara ba su kariya.

    Gwamnatin ƙasar ta ce hare-haren na da nasaba da ayyukan gaggan masu safarar ƙwayoyi waɗanda ke nuna fushinsu sakamakon kwararan matakan da aka ɗauka wajen daƙile ayyukansu na safarar miyagun kwayoyi.

  9. Farashin kayayyaki a Najeriya ya hauhawa a watan Maris - NBS

    Farashin kayayyaki ya hauhawa a watan Maris da ya gabata zuwa kashi 24.23 cikin 100 a sababbin alƙaluman da aka koma amfani da su a Najeriya.

    Rahoton da hukumar ƙididdiga ta ƙasa ta fitar a yau Talata ya nuna cewa an samu ƙarin hauhawar farashin da kashi 1.05 idan aka kwatanta da watan Fabrairu na 2024 daga 23.18 da aka samu a watan.

    Wannan ne karon farko da aka samu ƙarin hauhawar farashin a Najeriya tun bayan da hukumar National Bureau of Statistics (NBS) ta sauya ma'aunin da take amfani da shi wajen fitar da alƙaluman a farkon shekarar nan.

    "Bugu da ƙari, alƙaluman saurin hauhawaar farashin ya kai 3.90% a watan Maris na 2025 idan aka kwatanta da na Fabrairu, wanda yake 2.04%," a cewar rahoton.

    Ta ƙara da cewa bisa lissafin shekara-shekara, hauhawar kayan abinci kuma ta kai kashi 21.79 a watan Maris ɗin na 2025 idan aka kwatanta da Maris na 2024.

    Ta ce abubuwan da suka fi jawo hauhawar farashin sun haɗa da abinci da kuma lemukan sha na kwalaba (kashi 9.28 cikin 100), da kuɗaɗen hayar gida da na wuraren sayar da abinci (kashi 2.99 cikin 100), da kuɗin sufuri ((kashi 2.47 cikin 100).

    Sauran su ne kuɗin ruwa, wuta, iskar gas da sauran makamashi, ilimi, sai kuma harkokin lafiya.

  10. Ƴansanda na bincike kan sare bishiya mai shekaru 500

    Ƴan sanda a Birtaniya na bincike kan sare wani daɗaɗɗen bishiya a arewacin Landan.

    Ma'aikatan birnin ne suka gano abin da ya rage na bishiyar a makon da ya gabata, wanda aka yi kiyasin cewa ta kai shekara 500. Yanzu an sake dasa wani itacen gaggawa a wurin.

    Itacen mai tsawon mita 20 a Enfield, ya kasance yana da muhimmanci da kuma tarihi a ƙasar.

    Wani mazaunin yankin Enfield, Benny Hawksbee, ya ce "bishiyar mallakin Enfield ne kuma tana cikin al'adunsu - na kaɗu matuka da sare ta".

    Shugaban hukumar birnin, Ergin Erbil, ya ce sun ɗauki batun sare bishiyar a matsayin laifi, kuma sun kai rahoto wajen jami'an tsaro.

    An samu hatsaniya lokacin da aka sare bishiyar.

    An zargi Daniel Graham, mai shekara 39 da Adam Carruthers mai shekara 32, dukkansu da suka fito daga garin Cumbria, da janyo asarar fam 600,000 bayan sare bishiyar.

    Za su gurfana a gaban alkali a shari'ar da za a fara ranar 28 ga watan Afrilu a wani kotu a Newcastle.

  11. Su wane ne za su fafata a wasan daf da karshe na Champions League?

    Idan Arsenal da Aston Villa suka samu nasarar doke Real Madrid da Paris St-Germain a zagayen kwata-fainal a gasar Zakarun Turai, hakan zai sa a samu ƙungiyoyin Ingila biyu da za su buga wasan daf da karshe a bana a gasar.

    Hakan kuma zai bai wa ƙungiyar Premier ɗaya damar zuwa wasan karshe a Allianz Arena ranar 31 ga watan Mayu.

    Za a kuma iya samun ƙungiyoyin Jamus biyu da za su buga wasan daf da karshe a ɗaya gefen, sai dai da kamar wuya ganin cewa Barca ta ɗura wa Borussia Dortmund da ta kai wasan karshe a bara kwallo 4-0 a zagayen farko, Inter Milan kuwa ta doke Bayern Munich da 2-1.

    Har ila yau, za a iya kuma samun wasan 'El Clasico' a wasan karshe na Champions League, amma har sai idan Real Madrid ta farke kwallaye uku da Arsenal ta zura mata - ta kuma fitar da ita, sannan ta lashe wasan daf da karshe - ita kuma Barcelona ta samu nasara a ɗaya gurbin.

    Hasashen yadda wasan daf da karshe na Champions league zai kasance:

    • Arsenal/Real Madrid/ v PSG/Aston Villa
    • Barcelona/Borussia Dortmund v Bayern Munich/Inter Milan
  12. Ana taro a Birtaniya kan samar da zaman lafiya a Sudan

    Sakataren harkokin wajen Birtaniya, ya ce akwai buƙatar ƙasashen duniya su shawo kan ɓangarorin da ke rikici da juna a Sudan domin kare rayukan fararen hula da kuma barin a shigar da kayan agaji.

    Yayin wani taro a London, wakilai daga ƙasashen Turai da na ƙungiyar Tarayyar Afirka da na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da kuma Masar, sun yi alkawarin ƙara tallafi da kuma neman hanyar da za a samu zaman lafiya a ƙasar.

    Ba a gayyaci kowanne daga cikin ɓangarorin da ke rikici da juna ba a Sudan da ma ƙasashen da ake zargi suna taimaka musu da makamai.

  13. Amurka ta dakatar da tallafin dala biliyan biyu da take bai wa jami'ar Harvard

    Ma'aikatar ilimi a Amurka ta sanar da dakatar da tallafin fiye da dala biliyan biyu da take bai wa jami'ar Harvard don gudanar da harkokinta.

    Ma'ikatar ta ce ta ɗauki matakin ne saboda matakin jami'ar na kin amincewa da buƙatar fadar White House na rufe kwasa-kwasan koyar da daidaito da adalci ga kowa.

    Gwamnatin Trump ta ce ana buƙatar sauya shugabancin Havard, da yadda ake bai wa ɗalibai damar shiga jami'ar.

    Sai dai a sanarwar da shugaban jami'ar Alan Gava ya fitar, ya ce Harvard ba za ta taɓa miƙa wuya kan aniyar Trump ba.

  14. Shin Villa za ta iya farke kwallayen da PSG ta zuba mata?

    Aston Villa za ta karɓi bakuncin Paris St Germain a wasa na biyu zagayen kwata fainal a Champions League a Villa Park a yau da daddare.

    A makon jiya PSG ta doke Villa 3-1 a wasan farko a Faransa, kuma Villa ce ta fara cin ƙwallo daga baya PSG ta farke, sannan ta kara biyu a raga.

    Villa na sane da cewa farke ƙwallayen da PSG ta ɗura mata ba abu ne mai sauki ba.

    Emery shi ne kociyan PSG a lokacin da suka doke Barcelona 4-0 a 2017, amma da suka je Sifaniya aka farke su a Champions League.

    Emery ya buƙaci ƴan wasansa da su kafa tarihin kai wa zagayen daf da karshe, bayan sun zare ƙwallayen da PSG ta zuba musu a Faransa a makon jiya.

  15. Mutanen da suka zuba kuɗi a tsarin CBEX sun tafka asara

    Ƴan Najeriya da dama sun yi ta nuna ɓacin-rai a kafofin sada zumunta bayan asara da suka tafka a wani tsarin zuba kuɗi mai suna CBEX.

    Waɗanda suka zuba jari a tsarin sun ce sun ƙasa cire kuɗaɗensu na tsawon kwanaki, inda lokacin da suka zo cire kuɗin suka samu babu ko sisi a asusansu.

    CBEX dai wani tsarin zuba jari ne na dijital wanda yake ninƙa wa masu zuba jari da kashi 100 cikin wata guda.

    Masu zuba-jarin suna kuma samun ƙarin kudi idan suka kawo wani cikin harkar.

    CBEX ɗin wanda ya kasance yana hada-hadar kuɗin kirifto, ya fara aiki a Najeriya a shekara da ta gabata.

    Wani mai suna Ola, ya faɗa wa sashen BBC Pidgin cewa ya rasa kusan naira 450,000 bayan zuba-jari a tsarin na CBEX

    Lamarin ya kai ga wasu fusatattun matasa afka wa ofishin CBEX a Ibadan, inda suka wawushe kayayyaki a ofishin.

    Tun da farko dai, hukumar da ke kula da hannayen jari a Najeriya, SEC, ta gargaɗi ƴan Najeriya kan mu'amala da kamfanonin hada-hadar kuɗi ta intanet da ba a yi wa rajista ba.

    Ta ce babban laifi ne yin hulɗa da irin waɗannan kamfanoni.

  16. Karan-battar Barca da Dortmund a gasar Champions League

    Borussia Dortmund za ta kara da Barcelona a wasa na biyu a Champions League zagayen kwata fainal ranar Talata a Jamus.

    A makon jiya kafar Barcelona ɗaya ta kai daf da karshe a gasar zakarun Turai, bayan doke Borussia Dortmund 4-0 a Sifaniya.

    Raphinha ne ya fara cin na farko sai Robert Lewandoeski ya kara biyu a jere da kuma Lamine Yamal da ya zura na huɗu a wasan.

    Wannan shi ne karo na biyar da za su kece raini a tsakaninsu a Champions League, inda Barcelona ta ci wasa uku da canjaras ɗaya.

    Dortmund tana mataki na takwas da maki 42 a teburin Bundesliga, bayan kammala wasannin mako na 29.

    Saboda haka wannan kofin ne ke gabanta da zai ba ta damar buga Champions League a 2025/26, idan ta lashe shi.

    A bara Dortmund ta buga wasan karshe a Champions League, inda Real Madrid ta yi nasarar ɗaukar na 15 jmilla.

  17. Yaƙin Rasha da Ukraine: Trump ya ɗora wa Zelensky laifin soma yaƙi

    Shugaba Donald Trump na Amurka ya ɗora laifin soma yaƙi tsakanin Rasha da Ukraine kan Volodymyr Zelensky - kwana guda bayan wani hari mafi muni da Rasha ta kai wani ƙauye a Ukraine da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 35 da jikkata 117.

    Shugaban na Amurka ya ce shugaban Ukraine yana da laifi shi da takwaransa na Rasha Vladimir Putin kan 'mutuwar miliyoyin mutane" a yaƙin Ukraine.

    "Ba za ka fara yaƙi da mutumin da ya fi ka girma har sau 20 ba, sannan ka yi fatan za a ba ka makaman linzami," kamar yadda Trump ya faɗa wa manema labarai a fadar White House. Ya kuma ɗora laifin rikicin kan tsoho shugaban ƙasar Joe Biden.

    Kalaman Trump na zuwa ne bayan Alla-wadai da aka yi wa Rasha kan hari da ta kai birnin Sumy na Ukraine a ranar Lahadi, wanda shi ne hari mafi muni kan fararen hula a wannan shekara.

  18. 'Har yanzu akwai ƴan matan Chibok 82 a hannun ƴan Boko Haram'

    Yayin da ake cika shekara 11 da sace ƴan matan sakandaren Chibok da ƙungiyar Boko Haram ta yi a jihar Borno, har yanzu akwai ƴan mata 82 da ba su koma gida ba.

    An sace 'yan matan ne su 276 a ranar 14 ga watan Afrilun, 2014 - wannan mummunan al'amari na sace ƴan matan ya tayar da hankalin duniya a lokacin.

    Mai magana da yawun ƙungiyar masu fafutukar ganin an saki sauran ƴan matan, Jeff Okoroafor, ya ce har yanzu iyayen waɗanda ƴaƴansu ba su koma gida ba na rayuwa cikin kunci.

    Cikin abubuwan da ƙungiyar ke buƙata sun haɗa da; faɗa wa iyayen ƴan matan 82 da ƴaƴansu ba su koma gida ba ƙoƙari da ake yi na kuɓutar da su, da kuma fitar da rahoton Janar Ibrahim Sabo kan sace ƴan matan da kuma sanin irin matakin da gwamnati ta ɗauka ga waɗanda ke da hannu.

    Sanarwar da ƙungiyar ta fitar, ta ce abin kunya ne ga gwamnatin Najeriya ko kuma gazawar jami'an tsaro na ƙasa ceto sauran ƴan matan, shekara 11 da sace su - inda ta ce hakan ya nuna cewa gwamnati ba ta damu da ƴan ƙasarta ba.

    "Muna jin ciwo duk lokacin da muka tuna sace ƴaƴan mu. Muna buƙatar gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen ganin ta ceto sauran ƴan mata, samar da tallafi ga waɗanda suka tsira da kuma hukunta masu laifi," in ji sanarwar ƙungiyar.

    Gwamnatin Najeriya dai ta sha yin alkawarin ceto sauran ƴan matan na Chibok, sai dai har yanzu babu labarinsu.

  19. Tinubu ya yi Alla-wadai da harin ƴan bindiga a Filato

    Shugaba Bola Tinubu ya nuna ɓacin-rai da kuma kaɗuwa kan kashe mutane da wasu ƴan bindiga suka yi a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato.

    Shugaban ya yi Alla-wadai da lamarin, ya kuma miƙa ta'aziyyarsa ga al'ummar jihar - inda ya buƙaci a nemi hanyar warware rikicin da kuma samar da zaman lafiya.

    Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Bayo Onanuga ya fitar, inda Tinubu ya nanata muhimmancin haɗin-kai ba tare da nuna bambacin addini ko kabila.

    "Dole ne shugabannin al'ummomi da na addini da kuma siyasa su zo su haɗa-kai don daƙile waɗannan hare-hare da suka addabi jama'a," in ji Tinbu.

    Aƙalla mutum 50 ne suka mutu a harin da ƴan bindigar suka kai jihar a cikin daren Litinin.

  20. Mutane da dama na cikin mawuyacin hali bayan guguwa ta ɗaiɗaita Iraqi

    Ma'aikatar lafiya a Iraqi ta ce sama da mutum 1800 ne suke fama da matsalar numfashi, bayan guguwar da ta daidaita tsakiya da kudancin ƙasar.

    Wani jami'i a yankin Muthanna, ya ce mutum 700 daga cikinsu na cikin mawuyacin hali, haka lamarin yake a wasu yankunan ƙasar.

    Hotunan da aka yaɗa a intanet sun nuna yadda sararin samaniya ya turnuke da kura mai launin ruwan goro.

    An kuma samu katsewar wutar lantarki, yayin da aka soke tashi da saukar jiragen sama.

    Makarantu da kasuwanni sun kasance a rufe - sannan asibitoci sun cika maƙil da marasa lafiya.

    Hukumar hasashen yanayi a Iraqi ta ce an samu tashin guguwar ne sakamakon rashin zubar ruwan sama da ya janyo fari a ƙasar.