Iran ta sako wani ɗan Faransa da take riƙe da shi tun 2022
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce Iran ta sako wani ɗan ƙasar da ake tsare da shi tun watan Oktoban 2022.
An tsare Olivier Grondeau ne bisa dalilai na tsaro bayan kama shi da akayi a birnin Shiraz da ke kudancin ƙasar.
Shugaba Macron ya tabbatar da dawowar Mista Grondeau zuwa Faransa sai dai babu wasu cikakkun bayanai kan sharuɗɗan sako shi.
Mista Macron ya kuma buƙaci a sako sauran ƴan ƙasarsa biyu da ake riƙe da su a gidajen yari da ke Iran.
Ƙasashen yamma dai sun daɗe suna zargin Iran da tsare ƴan ƙasashen waje ba tare da dalili ba domin yin amfani dasu a matsayin wani abin yin yarjejeniyar diflomasiyya.