Sai da safe
Mun zo ƙarshen rahotonnin na ranar Lahadi a wannan shafi.
Za mu kawo gobe da safe kai-tsaye. Amma kafin haka, ku duba ƙasa domin karanta waɗanda muka kawo a yau daga sassan duniya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 2/11/2025
Isiyaku Muhammed da Umar Mikail
Mun zo ƙarshen rahotonnin na ranar Lahadi a wannan shafi.
Za mu kawo gobe da safe kai-tsaye. Amma kafin haka, ku duba ƙasa domin karanta waɗanda muka kawo a yau daga sassan duniya.
Sakataren sufuri na Amurka ya yi gargadi ga matafiya da su yi tsammanin samun jinkiri a tafiye-tafiyensu na jirgin sama saboda ba a biya masu bayar da hannu a filin jirgi alashinsu ba har yanzu.
An shiga yanayin ne sakamakon har yanzu gwamnatin Amurka ba ta da kasafin kuɗi, wanda yaznu ya shiga mako na biyar.
Sean Duffy ya ce jami'an masu bayar da hannu na fama da rashin lafiya saboda haka zai rage tashin jirage kafin ya dauki matakin da zai iya jefa rayuka ko lafiyar jama'a cikin hadari.
Lamarin ya zo ne a yayin da ake shirin shiga lokacin hutu da ake yawan tafiye-tafiye. Babu alamun loikacin da za a kawo ƙarshen halin na rashin samar da kudi ga gwamnati, wanda ke neman zama mafi tsawo a tarihi.
Rashin samar da kudin ya shafi Amurkawa da ke aikin gwamnati ko kuma suke bukatar tallafin tarayya.

Asalin hoton, EPA
Kafar yaɗa labarai ta Iran ta ruwaito cewa madatsun ruwan da ke bai wa birnin Tehran na fuskantar barazanar ƙafewa cikin mako biyu masu zua.
Shugaban kamfanin ruwan sha na birnin ya ce ɗaya daga cikin madatsun ruwan na ɗauke ne da kashi 8 cikin 100 kawai na ruwan da ya kamata su ajiye.
Ƙasar na fama da fari mafi muni cikin tsawon shekaru. A kwanan nan, rahotonni na cewa an kashe ruwan a wasu unguwanni saboda a alkinta shi.
Kazalika, gwamnati ta bayar da hutu sau biyu a watan Yuli da Agusta da zimmar adana ruwan sha da makamashi.

Asalin hoton, Reuters
Farashin muhimman kayayyaki ya yi tashin gwauron-zabi a Tanzania sakamakon zanga-zangar da aka yi kwanaki ana yi kan zɓen shugaban kasar.
Farashin man fetur ya ninka kusan sau uku, yayin da farashin kayan abinci da sauran muhimman kayan bukata ya ninka sau biyu a yankuna da dama.
Wakiliyar BBC ta ce "wasu sun yi amanna da gangan aka kirkiri karancin domin takaita zirga-zirga da gangamin masu zanga-zangar".
An bayyana Shugaba Samia Suluhu a matsayin wadda ta ci zaɓen na ranar Laraba, nasarar da 'yan hamayya suka ce muzanci ce ga dimukuradiyya.
Da take magana a yau Lahadi kan rahotannin da ake ta bayarwa na kisan jama'a, babbar jami'ar harkokin waje ta Tarayyar Turai, Kaja Kallas ta bukaci hukumomin kasar ta Tanzania su kai zuciya nesa, su mutunta rayukan al'umma.
An takaita zirga-zirrgar jama'a, kuma yawancin sassan kasar na cikin duhu saboda hukumomi sun katse lantarki da intanet.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Birtaniya na "ƙoƙarin karɓe" lambar soja ta Andrew Mountbatten Windsor bayan Sarki Charles ya nemi yin hakan, a cewar sakataren tsaron ƙasar.
John Healey ya ce sarkin ya nuna "abin da yake so kenan".
Andrew wanda aka ƙwace wa takensa na yariman masarautar Birtaniya a ranar Alhamis, ya ci gaba da riƙe matsayin Vice Admiral a rundunar sojin ruwan Birtaniya bayan ya haƙura da sauran muƙamansa a 2022.
Healey ya faɗa wa BBC cewa: "Wannan mataki ne da ya dace. Shi ne abin da sarki ya nuna yana so mu ɗauka kuma muna aiki kan hakan yanzu haka."
Andrew ƙani ne ga Sarki Charles da ya shafe shekara 22 a rundunar sojan ruwa, amma an ƙwace matsayin nasa tare da korar sa daga gidan sarauta saboda alaƙarsa da Jeffrey Epstein - ɗan Amurka da aka kama da laifin safarar yara domin karuwanci.

Asalin hoton, NRC
Jirgin ƙasa na Warri zuwa Itakpe a kudancin Najeriya ya goce kwana huɗu bayan ya koma zirga-zirga.
Hukumar sufurin jiragen ƙasa Nigerian Railway Corporation (NRC) ta tabbatar da faruwar lamarin a yankin Agbor na jihar Delta cikin wata sanarwa a yau Lahadi.
Ta ce gocewar da ta faru da misalin ƙarfe 7:30 na yammacin Asabar, akwai yiwuwar masu satar kayan gwamnati ne suka haddasa ta. Ta ƙara da cewa biyu ckin bakwai na layukan dogon ne lamarin ya ritsa da su.
Sai dai sanarwar ta ce ba a samu asarar rayuka ba a lamarin, wanda ya sa aka dakatar da jigilar fasinja.

Asalin hoton, Rabiu Musa Kwankwaso/Facebook
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ƴanci da take da dokokin da take amfani da su wajen gudanar da harkokinta.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a matsayin martani kan bazaranar shugaban Amurka Donald Trump, inda ya ce zai iya amfani da ƙarfin soji wajen murƙushe ta'addanci a Najeriya matuƙar gwamnatin ƙasar ba ta hana abin da ya kira kisan kiyashi da ake yi wa kiristoci a ƙasar ba.
A wani jawabi da Kwankwaso ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, ya ce "ya kamata a fahimci cewa Najeriya ƙasa ce mai cikakken ƴanci wadda mutanenta suke fama da matsalolin tsaro daga masu tayar da ƙayar baya."
Kwankwaso ya ce matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta suna shafar kowa da kowa, "ba tare da bambancin addini ko ƙabila ko fahimtar siyasa ba," in ji shi.
Ya ƙara da cewa kamata ya yi Amurka ta taimaka wa gwamnatin Najeriya da kayan yaƙi na zamani domin yaƙi da matsalar, "ba wai ta riƙa yi mata barazanar da ka iya ƙara raba kan ƴan ƙasar ba."
Kwankwaso ya shawarci gwamnatin Najeriya ta naɗa wasu ƙwararrun masana diflomasiyya domin su tattauna da gwamnatin Amurka kan batun, sannan ya yi kira ga ƴan ƙasar da suka ƙara haɗa kai domin fuskantar matsalolin da ƙasar ke fuskanta.
"Kuma lallai lokaci ya yi da gwamnatin Najeriya za ta naɗa jakadunta domin wakiltarta a ƙasashen duniya."

Asalin hoton, Reuters
Shugaban ƙasar Iran ya ce cibiyar makamashin ƙasar za ta yi aiki tuƙuru domin inganta cibiyoyin nukiliyarta domin su koma da ƙarfinsu fiye da yadda suke a baya.
Shugaban yana wannan jawabin ne game da irin ɓarnar da hare-haren da Amurka da Isra'ila suka a kan cibiyoyin nukiliyar ƙasar a watan Yunin da ya gabata.
Masoud Pezeshkian ya nanata cewa duk da cewa an kashe wasu masana nukiliyar ƙasar, suna da wasu ƙwararru da za su ɗaura daga inda aka tsaya.
Hukumomin Iran dai sun ce hare-haren ba lalata dukkan cibiyoyin ba, inda suka ce ɓarna ce ƙarama aka yi mata.
Trump dai ya ce matuƙar Iran ta koma aikin nukiliyarta, shi kuma zai sake ƙaddamar da hare-hare a ƙasar, a daidai lokacin da Oman take kira ga ƙasashen biyu da su koma teburin tattaunawa.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Trump ya yi barazanar daukar matakin soji a Najeriya, yana mai zargin gwamnatin kasar da kyalewa ana kashe kiristoci.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Mista Trump ya ce Washington na iya shiga Najeriya da ƙarfin soji don kakkaɓe abin da ya kira ƴanta'adda masu kishin Islama da ke aikata ta'asa.
Ya kuma yi barazanar dakatar da duk wani taimakon Amurka ga Najeriya.

Asalin hoton, Sonora Public Security Secretariat
A kasar Mexio gobara a wani shago a birnin Hermosillo da ke arewa maso yammacin kasar ta kashe akalla mutum 20 tare da raunata wasu da dama.
Gwamnan lardin Alfonso Durazo ya ce gobarar ta auku ne sakamakon wata fashewa.
Shugabar kasr Mexio ta bayyana jimami tare da yin umarni ga gwamnatinta na bayar da taimakon da ya dace

Asalin hoton, ORTN
Firaministan Nijar Ali Mahaman Zeine ya gana da wakilan ƙasar Italiya a ƙarƙshin jagorancin ministan harkokin wajen ƙasar Antonio Tajani, inda suka tattauna batutuwan inganta tsaro da tattaliln arziki, kamar yadda kafar Air Info Agadez mai zaman kanta ta ruwaito.
A zantawarsu, sun mayar da hankali ne kan tabbatar da tsaro a yankin Sahel tare da samar da hanyoyin kasuwanci, inda Tajani ya nanata cewa akwai damarmakin da Jamhuriyar Nijar ke da su da ya ce ƙasashen turai za su amfana da su.
"Za mu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Nijar a dukkan ɓangarorin rayuwa, musamman haɗakar tsaro da noma da kasuwanci, sannan kamfanonin Italiya su zuba jari a ƙasar. Nijar da Italiy za su yi aiki tare," in ji shi kamar yadda rahoton ya bayyana.

Asalin hoton, AP
Tsohon shugaban Amurka Barrack Obama ya caccaki gwamnatin Donald Trump a taron gaggamin siyasa na yantakarar gwamna a Virginia da New Jersy.
Ya bukaci masu kada kuri’a a zabuka masu zuwa da su yi watsi da abin da ya kira rashin bin doka da sakaci da hauka da ake yi a fadar White House.
Obama ya shaida wa Amurkawa cewa Trump da 'yan Republicans na son su yi tunani domin wasu tsiraru ne kawai a mulki ke daukar mataki amma kuma a bar 'yan kasa da wahala.
Mista Obama ya yi jan kunne ga 'yan Republican kan gazawarsu na taka wa Shugaba Trump burki Obama, ba kasafai yake tsoma baki a harkokin siyasa ba amma har yanzu yana da farin jini a tsakanin 'yan Democrat.

Asalin hoton, Sputnik/Aleksey Babushkin/Kremlin
Hukumomi a Rasha sun ce wani harin jirgi marar matuki na Ukraine ya lalata wata tashar mai da ke bahar aswad.
Wasu hotuna a intanet sun nuna yadda wuta ke tashi yayin da sojoji ke kokarin kakkabo wasu jirage marar matuka da ke zuwa.
Matatun mai da tasoshin ruwa na Rasha na cikin wuraren da Ukraine ke kai wa hari a yakin da take yi da Rasha

Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar lafiya ta Najeriya ta ce gwamnatin ƙasar za ta biya likitoci basussukan da suke bi, sannan za a ɗauki sababbin likitoci domin magance matsalolin da suke yawan jefa likitocin cikin yajin aiki.
Minista a ma'aikatar lafiyar ƙasar Dokta Iziaq Salako ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya sanya wa hannu, inda a ciki ya ce shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya amince da kuɗin da za a biya kuɗaɗen da ake magana.
Gwamnatin ta ce za ta biya naira biliyan 11.9 a cikin kwana biyu domin biyan basukan albashi da alawus-alawus da ma'aikatan na asibiti suke bi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ministan ya ce gwamnati ta fitar da naira biliyan 10 a watan Agusta domin a fara biyan cikon albashin ma'aikatan na wata bakwai bayan ƙarin kashi 25 zuwa 35 da aka yi wa ma'aikatan lafiya na ƙasar a baya.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin ƙasar ta amince a ɗauki ƙarin likitoci a ƙasar, wanda ministan ya ce hakan zai rage yawan aikin da likitocin suke yi.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Ana kula da lafiyar wasu Fasinjojin jirgin kasa mutum tara da suka ji mummunan rauni bayan wani hari da aka kai a jirgin kasa a gabashin Ingila.
Ƴansanda sun kama mutum biyu da ake zargi a tashar Huntingdon, inda jirgin ya yi tsayawar gaggawa bayan fasinjoji da ke ciki sun sanar da ma’aikatan jirgin.
Shaidu sun bayyana yadda jini ke kwarara bayan da maharin dauke da wata babbar wuka ya daba wa mutane, inda ya razana fasinja suna ta gudu - wasu suka abka cikin ban-daki na jirgin.
Ƴansanda sun ce mutum 10 ke kwance a asibiti. Firaministan Biritaniya, Keir Starmer, ya kira al'amarin a matsayin mummuna.
Jama'a barkanmu da safiyar Lahadi, barkanmu da sake saduwa a wannan shafin na labaran kai-tsaye.
Za mu ɗaura daga muka tsaya a jiya Asabar.
Da fata za ku kasance tare da mu.