Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Man City ta tabbatar da ɗaukar Reijnders kan fam miliyan 46.5

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman labarai na wasanni a faɗin duniya daga 9 zuwa 15 ga watan Yunin 2025.

Taƙaitattu

  • Real Madrid ta fara da canjaras a Club World Cup
  • Barcelona ta ɗauki golan Espanyol Joan Garcia
  • An fitar da jadawalin sabuwar kakar Premier League
  • An sake buɗe kasuwar saye da musayar 'yanwasa
  • Real Madrid ta sayi matashi Mastantuono daga Argentina
  • Italiya ta naɗa Gattuso sabon kocinta
  • Sabbin dokokin da Fifa ta ɓullo da su a gasar Club World Cup
  • Inter Miami ta Messi ta fara Club World Cup da canjaras
  • Abin da ya kamata ku sani kan Fifa Club Wold Cup 2025

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Inter Milan ta ɗauki Chivu sabon kocinta

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Inter Milan ta naɗa Cristian Chivu a matsayin sabon kocinta.

    Kocin mai shekara 44, tsohon ɗanwasan bayan ƙungiyar ne kuma kocin matasan tawagarta ne wanda shi ne ke jagorantar kulob din Parma a yanzu.

    Parma ta naɗa tsohon ɗanƙwallon na ƙasar Rmania kocinta a a watan Fabrairu lokacin da ya fara aikin horar da babbar tawaga, inda ya ci wasa uku da suka kuɓutar da Parma daga sauka daga gasar Serie A ta Italiya.

    Zai maye gurbin Inzaghi ne wanda ya bar Inter bayan kashin da suka sha 5-0 a hannun PSG a wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai ta Champions League a ƙarshen watan Mayu. Tuni kuma ya karɓi aikin horar da Al-Hilal ta Saudiyya.

    Chivu ya saka hannu kan yarjejeniyar da za ta ƙare a 2027.

  2. Tottenham na gab da ɗaukar Thomas Frank sabon kocinta

    Tottenham na gab da naɗa kocin Brentford Thomas Frank a matsayin wanda zai maye gurbin Ange Postecoglou.

    Brentford na sa ran karɓar tayi a hukumance daga Tottenham nan gaba kaɗan amma dai har yanzu babu tabbaci game da tattaunawa tsakanin ƙungiyoyin.

    Idan cinikin ya faɗa, ana sa ran za a bai wa Brentford fansar fan miliyan 10 domin raba ɗan ƙasar Denmark ɗin mai shekara 51 da aikinsa na ƙungiyar.

    Yarjejeniya tsakanin Brentford da Frank za ta kai har 2027 kafin ta ƙare.

    Kuɗin zai iya ƙaruwa wanda zai danganta ne da yawan ma'aikatan da Frank zai tafi da su zuwa Tottenham.

    Tottenham ta kori Postecoglou a ranar Juma'a kwana 16 bayan ya jagorance ta lashe kofin Europa League - kofi na farko da ta ɗauka cikin shekara 17.

  3. Yaushe za a rufe kasuwar saye da musayar 'yanwasa ta farko?

    A gobe Talata za a rufe kasuwar saye da musayar 'yanƙwallo ta farko da aka buɗe a wannan bazarar.

    An raba kasuwar ne kashi biyu a wannan karon, an buɗe ta farkon ne tun a ranar 1 ga watan Yuni domin bai wa ƙungiyoyin da za su buga gasar kofin duniya ta kulob-kulob damar yin cefane.

    Za a fara gasar a ranar 15 ga watan Yunin nan.

    Za a buɗe kasuwar karo na biyu ranar Litinin, 16 ga wata sannan a rufe ta ranar 1 ga watan Satumba da ƙarfe 19:00 a gasar Premier ta Ingila da Scotland.

    Dokokin Fifa sun ce kasuwar sayen 'yanwasa ba za ta wuce mako 16 ba a kowace shekara, abin da ya sa aka raba ta biyu kenan a wannan karon.

    Manchester City da Chelsea ne ƙungiyoyin da za su wakilci Ingila a gasar, amma kowane kulob zai iya yin cefane a lokacin.

    Real Madrid ta yi amfani da damar wajen ɗaukar Trent Alexander-Arnold daga Liverpool kafin fara gasar.

  4. Chelsea ta sayi Mamadou Sarr daga Strasbourg

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta ɗauki ɗanwasan baya Mamadou Sarr daga Strasbourg kan fan miliyan 12.

    Matashin mai shekara 19 ɗan Faransa ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara takwas kuma zai iya buga gasar kofin duniya ta kulob-kulob da za a fara a watan nan.

    Ƙungiyar ta Enzo Maresca za ta fara wasa da LAFC ta Amurka ranar 16 ga watan Yuni kafin ta kara da Flamengo ranar 20 ga wata, sannan ta kammala da ES Tunis ta ƙasar Tunisia ranar 25.

    Chelsea da Strasbourg sun cimma yarjejeniyar sayen Sarr a watan Janairu.

    Ya buga wasa 28 a dukkan gasanni na kakar bana, inda suka ƙare a mataki na 7 a gasar Ligue 1 kuma za ta buga wasan cike gurbi na gasar zakarun Turai ta Conference League.

  5. Ronaldo ya nuna alamun ci gaba da zama a Al-Nassr

    Da alama ɗanwasan gaba na Portugal Cristiano Ronaldo na shirin ci gaba da zama a ƙungiyar Al-Nassr ta ƙasar Saudiyya.

    Kwantaragin ɗanwasan mai shekara 40 zai ƙare a ƙarshen watan nan, kuma duk da cewa majiyoyi sun faɗa wa BBC cewa kulob ɗin na da ƙwarin gwiwar tsawaita zamansa har yanzu ana raɗe-raɗi kan makomarsa.

    Tsohon Real Madrid da Man United da Juventus ɗin ya wallafa wani saƙo a shafukan sada zumunta a makon da ya gabata da ke nuna alamun zai bar ƙungiyar da ya fara taka wa leda a Janairun 2023.

    Amma da yake magana bayan ƙasarsa Portugal ta lashe gasar Eufa Nations League, Ronaldo ya nuna cewa alamu ba zai bar Saudiyyar ba.

    "Makomata? Babu abin da zai sauya. Al-Nassr? Eh," kamar yadda ya faɗa wa manema labarai bayan wasan da ya ci ƙwallonsa ta 138 a Portugal.

    A ranar Asabar ne Ronaldo ya ce ba zai buga gasar kofin duniya ta kulob-kulob ba da za a fara a wannan watan.

  6. Nations League ne kofi na 34 da Ronaldo ya lashe a tarihi

    Tauraron ɗanwasa Cristiano Ronaldo ya cika da hawayen jin daɗi bayan lashe kofin gasar Uefa Nations League da ƙasarsa Portugal ta yi ranar Lahadi.

    Karo na 34 kenan da Ronaldo ya lashe babban kofi a tariihin sana'arsa ta ƙwallon ƙafa na sama da shekara 20 tsakanin ƙungiyoyi da kuma ƙasarsa.

    Portugal ta doke maƙwabciyarta kuma babbar abokiyar hamayya Sifaniya a bugun finareti bayan tashi wasa 2-2.

    Yana daga benci aka busa usur ɗin ƙarshe amma ba a yi canjinsa ba sai da ya zira ƙwallo a ragar su Yamine Yamal a minti na 61, wadda ita ce ta 138 da ya ci wa Portugal.

    Kuma ita ce ta takwas da ya ci a gasar ta bana cikin wasa tara da ya buga - Viktor Gyokeres na Sweden ne kaɗai ya fi shi yawan ƙwallayen.

    Ƙaramar gasar ta ƙasashen Turai da suka lashe a jiya ta zama babban kofi na uku kenan da Portugal ta ci a ƙarƙashin jagorancin Ronaldo mai shekara 40 a yanzu.

    • European Championship 2016
    • Uefa Nations League 2018-19
    • Uefa Nations League 2024-25
  7. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye daga duniyar wasanni.

    Umar Mikail ne ke tare da ku a wannan lokaci.

    Ku biyo mu domin sanin yadda take kayawa a duniyar wasannin.