Kwamitin gudanarwa na Jam'iyyar PDP ya tabbatar da Udeh-Okoye a matsayin sakataren jamiyyar na kasa

Asalin hoton, PDP
Kwamitin gudanar wa na Jam'iyyar PDP ya tabbatar da Sunday Ude-Okoye a msatyin sakataren jam'iyyar na kasa.
Jarridar The Punch ta ce hakan dai na cikin wata sanarwa da kwamitin gudanarwar ya fitar mai dauke da sa hannun sakatren yada labarai na jam'iyyar ta PDP na kasa Debo Ologunagba ya fitar a yau Laraba.
Sanarwar ta ce ta dauki wanna mataki ne domin yin biyayya ga hukuncin da kotun daukaka kara ta yi kan batun.
Haka kuma sanarwar ta ambato, cewar tuni ta aikawa da Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC, matsayar da suka cimma na tabbatar da Sunday Udeh-Okoye a matsayin halattacen sakataren jam'iyyar tasu na kasa, da sauran dukkan hukumomin da suka kamata, kamar yadda hukucin kotun daukaka karar ya bayar da hukunci.
"Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDp a zaman da muka yi a yau Laraba, 12 ga watan Fabarerun, 202, mun amince da wannan takarda mai kwanan watan 11 ga watan Fabarerun, 2025, ga shugaban jam'iyyar mu na ruko, kan dukkan wani batu da ya shafi dambarwar sakatren jam''iyyar PDP.


















