Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 04/09/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na 04/09/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Haruna Kakangi da Aisha Aliyu Ja'afar

  1. Haɗarin jirgin ƙasa a Portugal ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 15

    Aƙalla mutane goma sha biyar ne suka mutu, yayin da 18 su ka jikkata bayan da wani jirgin ƙasan fasinja ya kauce hanya ya kuma yi haɗari a Lisbon babban birnin kasar Portugal.

    Jirgin mai ɗaukar fasinjoji kusan arba'in ya lalace sakamakon yin karo da wani gida bayan ya sauka daga layin dogo.

    Wata mata da ta shaida faruwar lamarin ta ce jirgin ya faɗi ne kusa da inda su ke wanda ya sa su barin wurin a guje.

    Har yanzu dai ba a san musabbabin faruwar lamarin ba, sai dai tuni aka kaddamar da bincike.

    Magajin garin birnin na Lisbon ya bayyana lamarin a matsayin 'Mummunar rana' ga birnin da kuma gwamnatin Portugal.

  2. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a yau Alhamis

    Shafin na yau zai fi mayar da hankali ne kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta, da kuma sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kuma kallon bidiyo.

    Ku kasance da mu.