Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/08/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku bubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/08/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi da Aisha Babangida

  1. Ranar Hausa: Daga ina Hausawa suka samo asali?

    Hausawa mutane ne da suka yaɗu a wurare da dama na duniya, kuma suna daga cikin al'umma mafiya yawa a nahiyar Afirka.

    Mafi yawa daga cikin al'ummar ta Hausa na rayuwa ne a arewacin Najeriya zuwa kudancin Jamhuriyar Nijar.

    Sai kuma ƙasar Kamaru da Ghana da kuma sauran ƙasashen yammacin nahiyar Afirka.

    Sai dai wani fage da ake kai kai-komo a kai shi ne asalin al'ummar ta Hausawa.