Ana ci gaba da gudanar da zanga-zanga a harabar ofishin firaministan Isra'ila
Asalin hoton, Reuters
Ana ci gaba da zanga-zanga a Isra'ila a wajen ofishin Firaminista Benjamin Netanyahu.
Ƙungiyar ta 'Hostages and Missing Families Forum' ce ta shirya zanga-zangar, wacce ke neman gwamnati ta samar da yarjejeniyar sakin mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza.
Ana iya ganin mutane suna tafiya cikin dogon layi, ɗauke da alluna da ke da hotunan waɗanda aka yi garkuwa da su
Dubban masu zanga-zanga ne suka fito kan tituna a Isra’ila suna kira ga gwamnati da ta amince a cimma yarjejeniyar sakin fursunoni tare da kawo ƙarshen yaƙin Gaza.
A halin da ake ciki kafafen yaɗa labaran Isra'ila sun rawaito cewa a yanzu an kammala taron majalisar ministocin tsaro na Firaminista Benjamin Netanyahu.
Kamar yadda suka nuna an ce jami'ai za su tattauna mataki na gaba na farmakin da sojojin Isra'ila za su kai a birnin Gaza - amma ba batun tattauna sabon daftarin tsagaita wuta da masu shiga tsakani na yankin suka gabatar.
Kungiyar Hamas dai ta amince da shirin tun sama da mako guda da ya gabata.
Ukraine ta yarda cewa Rasha ta shiga yankin Dnipropetrovsk
Asalin hoton, EPA
Dakarun Ukraine sun amince cewa sojojin Rasha sun tsallaka zuwa yankin masana'antu na gabashin Dnipropetrovsk kuma suna ƙoƙarin kafa wani sansani a yankin.
"Wannan shi ne hari na farko mai irin wannan girman da aka kai a yankin Dnipropetrovsk," in ji Viktor Trehubov, na ƙungiyar dakaru na Dnipro Operational-Strategic Group of Troops ya shaida wa BBC, ko da yake ya bayyana cewa an dakatar da su.
Rasha ta daɗe ta na iƙirarin cewa ta shiga yankin tun da farkon bazara, yayin da dakarunta ke ƙoƙarin shiga cikin yankin Ukraine daga Donetsk.
A farkon watan Yuni jami'an Rasha sun ce an fara kai farmaki a Dnipropetrovsk, kodayake sabbin rahotanni daga Ukraine sun ce da ƙyar suka kutsa kan iyakar yankin.
Duk wani ci gaba da Rasha ta samu a Dnipropetrovsk zai zama wani rauni ga Ukraine, domin yunƙurin diflomasiyya da Amurka ke jagoranta na kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a kasar na ci gaba da fuskantar cikas duk da cewa Shugaba Donald Trump ya gana da Vladimir Putin na Rasha a Alaska.
Ouattara ya miƙa takardar neman tsayawa takarar shugaban ƙasa a Ivory Coast
Asalin hoton, Getty Images
"Na amsa kiran jam'iyyata, RHDP, da na ƴan Ivory Coast da dama da ke fatan mu ci gaba da tafiya tare a kan tafarkin zaman lafiya, kwanciyar hankali, da ci gaban da ƙasarmu ta samu a cikin shekaru da dama da suka gabata," in ji shugaban ƙasar mai ci Alassane Ouattara a ranar Talata, 26 ga watan Agusta.
Wannan bayanin na zuwa ne bayan da shugaba Ouattara ya miƙa takardar tsayawa takara a hukumance a hedkwatar hukumar zaɓe mai zaman kanta ta CEI.
Sanarwar tasa ta samu goyon baya daga dubban ƴan jam'iyyarsa ta RHDP, waɗanda suka taru sanye da rigunan da ke ɗauke da hotonsa suna rera taken "Ado President!"
Yunƙurin na Ouattara ya ƙara yawan mutanen da ke shirin fafatawa a zaɓen shugaban ƙasa wanda a halin da ake ciki ke fama da cunkoson jama'a, inda ƴan takara kusan 40 suka miƙa takardunsu ga hukumar ta CEI.
Daga cikin su akwai tsohon shugaban ƙasar Laurent Gbagbo da kuma tsohon shugaban kamfanin Credit Suisse Tidjane Thiam, waɗanda dukkansu ke ci gaba da kasancewa a cikin ƴan takarar duk da cewa hukumar ta bayyana cewa ba su cancanta ba.
Shugaban gwamnatin Jamus ya ce bai yarda Isra'ila na harin ƴan jarida da gangan ba
Asalin hoton, EPA
Shugaban gwamnatin Jamus ya ce bai yarda Isra'ila ta kai hari kan a asibitin Nasser da ke Gaza a jiya da nufin kashe ƴan jarida ba.
Ƴan jarida biyar na daga cikin mutane aƘalla 20 da aka kashe a wannan harin.
Da ya ke magana a wani taron manema labarai a Berlin, Friedrich Merz ya ce: "Ban yi imani a halin yanzu cewa wannan hari ne da aka kai wa ƴan jarida da gangan ba."
Da ya ke martani kan sharhin da rundunar tsaron Isra'ila ta yi kafin ta fitar da sakamakon rahoto kan binciken farko kan hare-haren na ranar Litinin, Merz ya ƙara da cewa "Rundunar sojin Isra'ila da gwamnatin ƙasar sun yi alƙawarin fara gudanar da cikakken bincike kan wannan lamari. Ina so in jira sakamakon binciken kafin yanke hukunci".
Birtaniya a soki harin da Isra'ila ta kai asibitin Naseer
Gwamnatin Birtaniya ta yi alla-wadai da harin da Isra'ila ta kai kan wani asibiti a kudancin Gaza ta na cewa ba lamarin abin takaici ne kuma babu wata hujjar da za .
Mai magana da yawun Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya ce ya kamata a kiyaye ƴan jarida a kodayaushe kuma harin ya nuna buƙatar tsagaita wuta cikin gaggawa.
Aƙalla mutane 20 ne aka ce sun mutu a harin da aka kai a asibitin Nasser da ke Khan Younis.
Gwamnatin Isra'ila ta fitar da wata sanarwa inda ta ce Isra'ila ta yi matuƙar nadamar wannan mummunan hatsarin da ya afku, kuma ta ce sojojin na gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Faransa ta mayar da ƙoƙon kan sarkin da aka kashe zuwa Madagascar
Asalin hoton, Reuters
An mayar da ƙoƙon kan wani sarkin Malagasy da sojojin Faransa suka kashe a lokacin yaƙin mulkin mallaka a Madagascar.
An miƙa ƙoƙon kan sarki Toera - da na wasu mambobin majalisarsa guda biyu - a wani biki a ma'aikatar al'adu a birnin Paris.
An kai ƙoƙon kan Faransa ne a ƙarshen ƙarni na 19 kuma an adana shi a gidan tarihi a babban birnin ƙasar.
Wannan dai shi ne karon farko da aka fara amfani da sabuwar doka da ke da nufin gaggauta dawo da gawarwakin mutane da aka tafi da su Faransa.
A watan Agustan 1897, sojojin Faransa da aka aika don tabbatar da ikon mulkin mallaka a kan masarautar Menabé na mutanen Sakalava a yammacin Madagascar sun kashe sojojin yankin.
An kashe Sarki Toera kuma an yanke masa kai: an aika da kansa zuwa Paris inda aka sanya shi a ɗakin ajiyar kayan tarihi na ƙasa.
Bayan kusan shekara 130, matsin lamba daga zuriyar sarkin da kuma gwamnatin ƙasar Madagascar sun sa an dawo da ƙoƙon kan.
Gwamnatin Najeriya ta dakatar da jigilar jirgin ƙasa tsakanin Abuja da Kaduna
Asalin hoton, NRC
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa ta Najeriya NRC ta dakatar da ayyukan jiragen ƙasa kan hanyar Abuja zuwa Kaduna har sai lokacin da aka sanar da ɗage hakan.
Shugaban hukumar ta NRC, Kayode Opeifa, ne ya sanar da hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, sa’o’i bayan faruwar lamarin.
Opeifa ya ce wasu ma’aikatan hukumar tare da hukumar binciken sufuri ta Najeriya (NSIB) da sauran hukumomin da abin ya shafa, a halin yanzu suna nan a wurin da jirgin ƙasan ya tuntsure suna gudanar da bincike.
Ya yi watsi da iƙirarin cewa jiragen ba su da kyau kuma ya ce an fara mayar da kuɗaɗen tikiti ga duk fasinjojin da ke cikin jirgin.
Shugaban na NRC ya kuma karɓi wasu fasinjojin da ke cikin jirgin a tashar Asham da kuma tashar jirgin ƙasa ta Idu.
Ƴan jarida sun yi zanga-zanga don jimamin abokan aikinsu da aka kashe a Gaza
Asalin hoton, Getty Images
Ƴan jarida sun gudanar da zanga-zanga a birnin Brussels na ƙasar Belgium domin tunawa da abokan aikinsu da aka kashe a lokacin da suke bayar da rahoto a Gaza.
Zanga-zangar wacce ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasa da ƙasa ta shirya, ta biyo bayan mutuwar wasu ƴan jarida biyar ne sakamakon harin da Isra'ila ta kai a asibitin Nasser ranar Litinin.
Lamarin da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya kira "mummunan kuskure" ya fuskanci suka daga ƙasashen duniya.
Isra'ila ta ce sojojinta na gudanar da cikakken bincike kan lamarin
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Getty Images
Malaman jami'a a Najeriya na zanga-zanga kan rashin kuɗi da yanayain aiki
Asalin hoton, Getty Images
Malaman jami’a a Najeriya sun gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya a ranar Talata, suna neman gwamnati ta cika yarjejeniyar da suka ƙulla tun 2009.
Zanga-zangar ta jawo tsaiko a wasu jami’o’i inda ɗalibai suka rasa kulawar karatu.
Malaman da ke ƙarƙashin ƙungiyar ASUU sun koka da cewa suna wahala da kuma koyarwa cikin yunwa, da rashin kayan aiki a ɗakunan karatu da dakunan gwaji tare da fama da matsalolin rayuwa da aiki.
Shugaban ASUU, Farfesa Christopher Piwuna, ya ce idan gwamnati ba ta ɗauki mataki ba, za a iya shiga wani yajin aiki na dindindin.
Ƙungiyar na buƙatar ƙarin kuɗaɗen tallafi ga jami’o’i da inganta yanayin aiki da ’yancin gudanarwa da kuma ’yancin yin bincike.
ASUU ta sha shiga yajin aiki tun 2012 saboda gazawar gwamnati wajen cika yarjejeniyar 2009, kuma ta ce gwamnati tana zaɓar abin da ta ga dama kawai daga cikin alƙawuran.
Shekaru biyu kenan da ƙungiyar ta yi yajin aikin ƙasa na ƙarshe.
Mambobin ASUU sun haɗa da malamai daga jami’o’in tarayya da na jihohi a faɗin ƙasar.
Kotu a Afirka ta Kudu ta yanke hukunci kan binne tsohon shugaban Zambia
Asalin hoton, Getty Images
Kotun ƙoli ta Afirka ta Kudu ta yanke hukunci cewa tsohon shugaban Zambiya, Edgar Lungu, wanda ya rasu a watan Yuni yana da shekaru 68, dole ne a binne shi a ƙasarsa ta haihuwa.
Lungu ya rasu ne a asibitin Pretoria inda yake jinya.
Sai dai wannan hukunci na iya jinkirta binne shi, domin lauyoyin iyalansa za su iya komawa kotu domin ɗaukaka ƙara.
A farkon wannan watan, kotun Pretoria ta yanke cewa gwamnatin Zambiya na da haƙƙin yin jana’izar tsohon shugaban. Amma iyalinsa suna so a binne shi a Afirka ta Kudu, inda suke rikici da gwamnatin Zambiya kan lamarin.
Ƙasashen Afirka sun nuna adawa da mayar da Sudan cikin AU
Asalin hoton, Getty Images
Ƙasashen Afirka ta Kudu da Kenya da Habasha sun nuna adawa da ƙoƙarin Sudan na dawo da matsayin ta a Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) bayan juyin mulkin soji a shekarar 2021, kamar yadda gidan jarida na Sudan mai zaman kansa, Rakoba, ya ruwaito.
An ce ƙasashen uku sun bayyana adawarsu a lokacin ganawa a hedkwatar AU, suna mai cewa dawo da Sudan cikin kungiyar zai saɓa wa ƙa’idodin AU kan sauyin gwamnati ba bisa ƙa’ida ba.
Sudan ta ce ta cika dukkan sharuɗɗan da ake buƙata, ciki har da nada firaminista farar hula da gwamnati ta masana masu zaman kansu, don a mayar da ita cikin AU.
'Mutane da dama sun mutu, ɗaruruwa sun jikkata cikin sa'o'i 24 a Gaza '
Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar lafiyar Hamas ta bayyana cewa mutum 75 ne suka mutu a Zirin Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata, lamarin da ya kawo jimillar waɗanda suka mutu zuwa 62,819 tun daga watan Oktoba 2023.
Haka kuma, jami’an lafiya sun ce mutum 370 ne aka kai asibitoci daban-daban a Gaza ɗauke da raunuka, sannan kuma wasu adadin mutane har yanzu suna karkashin ɓaraguzan gine-gine da kuma a kan tituna in ji ma'aikatar.
Sabbin alƙaluman sun haɗa da mutanen uku da ma'aikatar ta ce sun mutu sakamakon rashin abinci mai gina jiki da yunwa.
Jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna ya sauka daga kan layin dogo
Asalin hoton, Facebook/Various
Jirgin ƙasa ɗauke da fasinja da ya taso daga Abuja babban birnin Najeriya zuwa Kaduna ya faɗi a ranar Talata da safe.
Lamarin dai ya jefa fargaba a tsakanin fasinjoji da ke cikin jirgin.
Rahotanni na cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na safe a kauyen Asham da ke hanyar Abuja zuwa Kaduna kuma jirgin ƙasa ta bar Abuja ne da misalin karfe 9:45.
Har yanzu ba a san abin da ya jawo saukar jirgin daga kan layin dogo ba, kuma babu tabbacin ko an samu waɗanda suka jikkata.
Hukumar Jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC) ba ta yi tsokaci a kan lamarin ba.
Asalin hoton, Facebook/Various
Asalin hoton, Facebook/Various
Bayanan bidiyo, Kalli bidiyon yadda jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna ya tuntsure
Trump ya yi barazanar korar gwamnar babban bankin Amurka, Lisa Cook
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amruka, Donald Trump ya sanar da aniyarsa na korar gwamnar babban bankin ƙasar, yayin da yake matsa ƙaimi kan yadda ake tafiyar da harkokin bankin.
A wata sanarwa, Trump ya zargi Lisa Cook, da bada bayanan ƙarya kan sharuɗan bada bashin sayen gida.
Cook ta ce shugaban ba shi da ikon cireta daga kujerarta tare da alƙawarta cigaba da ayyukanta ba tare da wani dar ba.
Tsohon shugaban Amurka Joe Biden ne ya naɗa Lisa Cook a wannan muƙamin, inda ta kasance mace bakar-fata 'yar tsantson Afrika ta farko da ta riƙe wannan muƙamin.
ECOWAS na shirin ƙaddamar da rundunar yaƙi da ta’addanci
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar ƙasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS ta bayyana shirin kafa rundunar gaggawa mai ƙarfin mutum 260,000 don yaƙi da ta’addanci da tashe-tashen hankula a yankin.
Wannan shi ne mafi girman shirin tsaro da ƙungiyar ta yi a kwanakin baya-bayan nan.
An bayyana wannan ne a taron manyan hafsoshin sojojin asashen Afirka da aka gudanar a Abuja, wanda ya tattaro manyan jami’an soja da jakadu da masana harkar tsaro.
Kwamishinan ECOWAS na harkokin siyasa da zaman lafiya da tsaro, Abdel-Fattah Musah, wanda ya yi wannan sanarwa, ya ce rundunar da za a kafa za ta ƙara ƙarfin runduna ta mutum 5,000 da ke ƙarƙashin tsarin zaman lafiya da tsaro na Tarayyar Afirka sosai.
ECOWAS na neman kasafin kuɗi na dalar Amurka biliyan 2.5 a shekara don ƙaddamar da rundunar, yayin da ministocin tsaro da kuɗi za su gana ranar Juma’a don kammala shirye-shiryen.
Haka kuma, ECOWAS na ƙarfafa tsaron ruwa tare da sabbin cibiyoyin tsaro guda uku da hedkwata ta haɗin gwiwa a Abuja don yaƙi da laifuka kamar fashi da makami da safarar mutane da dai sauran su.
Wannan mataki na zuwa ne a lokacin da Africa ta Yamma ke fama da tashin hankali na masu iƙirarin jihadi da juyin mulkin soja, da rashin kwanciyar hankali na siyasa.
Mutum uku sun mutu sakamakon yunwa a Gaza – Ma’aikatar lafiyar Hamas
Asalin hoton, Reuters
Ma’aikatar Lafiya ta Hamas ta bayyana cewa an samu karin mutuwar mutum guda uku sakamakon yunwa da ƙarancin abinci mai gina jiki a cikin kwana ɗaya da ya gabata.
Ta ce wannan ya ƙara yawan mutanen da suka mutu sakamakon yunwa da ƙarancin abinci mai gina jiki zuwa 303.
Cikin waɗannan akwai yara 117, kuma wannan rahoto ya biyo bayan wani binciken da Majalisar Ɗinkin Duniya ta tallafa da aka fitar makon da ya gabata wanda ya tabbatar da yunwa a birnin Gaza da sauran yankunan Gaza.
Sai dai Isra’ila ta soki wannan rahoto, tana mai cewa "ƙarya ce" kuma ta ƙi amincewa da cewa akwai yunwa a Gaza.
Jihohin Arewacin Najeria ba su nuna aniyar yin rajistar zaɓe sosai ba a makon farko
Asalin hoton, INEC
Bayanan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya - Inec - ta fitar kan alƙaluman makon farko na mutanen da suka nuna aniyar yin rajistar zaɓe ta intanet sun nuna cewa al'umma ba su fito sosai ba a yankin arewacin ƙasar domin yin rajistar.
Alƙaluman da hukumar ta Inec ta fitar a jiya Litinin sun nuna cewa jihar Osun ce ta fi yawan mutanen da suka nuna aniyar yin rajistar, inda take da yawan mutane 393,269, jihar Legas ke biye mata da mutum 222,205 sai kuma jihar Ogun mai yawan masu son yin rajista 132,823.
A arewacin Najeriya, Abuja, babban birnin tarayyar ƙasar ne ke da mafi yawan mutanen da suka nuna aniyar yin rajista, inda take da mutum 107,683, sai jihar Kaduna mai mutum 61,512 yayin da jihar Kogi ke biye mata da mutum 58,546.
Jihar Kano wadda ta fi kowace yawan al'umma a Najeriya na da yawan waɗanda suka nuna aniyar yin rajistar zaɓe 10,166 ne, Adamawa kuma na da 2,115 kacal.
Sai dai idan aka duba ƙasar baki ɗaya za a ga cewa yankin kudu maso gabashin ƙasar shi ne ya fi ƙarancin mutanen da suka nuna aniyar yin rajista a makon na farko.
Jihar Enugu na da mutum 484, Imo 481 sai kuma jihar Ebonyi mai mutum 261 kacal.
A ranar 18 ga watan Agusta ne hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya ta buɗe shafinta na intanet domin mutane su nuna aniyar yin rajistar katin zaɓe.
Alƙaluman na Inec sun nuna cewa ya zuwa ranar Lahadi 24 ga watan na Agusta an samu mutum miliyan 1,379,342 waɗanda suka nuna sha'awar yin rajistar ta shafin intanet.
Ya zuwa yanzu alƙaluman na Inec sun ce mata ne waɗanda ke gaba a yawan wadanda suka nuna aniyar yin rajista a fadin ƙasar, inda suke da kashi 52.04% yayin da maza ke da kashi 47.96%.
Daga nan sai hukumar ta sanar da cewa ta buɗe rumfunanta a fadin ƙasar domin bai wa mutane damar zuwa ƙafa-da-ƙafa domin yin rajista.
Aikin yin rajistar zaɓen na zuwa ne gabanin babban zaɓen shekara ta 2027, inda tuni jam'iyyu da kuma masu neman takara suka fara shiri.
Yanzu haka dai ƙasar ta Najeriya mai yawan mutum sama da miliyan 200 na da mutane miliyan 93,469,008 da suka yi rajistar zaɓe a faɗin ƙasar.
Asalin hoton, INEC
Ƙa'idojin rajistar zaɓe a Najeriya:
1- Wajibi ne mutum ya kasance ɗan Najeriya
2- Wajibi ne mutum ya kai shekara 18 da haihuwa kafin ranar yin rajista
3- Wanda ya kai shekara 18 amma bai samu damar yin rajista ba a baya
4- Wajibi ne ya kasance mazauni, ko ma'aikaci, ko kuma ɗan asalin wata ƙaramar hukuma ce ko gundumar da ake yin rajistar zaɓe
5- Ya kasance babu wani abu na shari'a da ya haramta masa yin zaɓe bisa dokokin Najeriya
6- Dole ne mutum ya gabatar da kansa a wajen masu aikin rajistar zaɓe domin yin rajista kuma ya gabatar da shaidar tantancewa, da na shekara da kasancewa ɗan ƙasa idan aka buƙaci hakan
7- Idan mutum yana da katin zaɓe amma babu sunansa a rajista akwai buƙatar ya je domin yin rajista
8- Idan mutum ya samu matsala lokacin tantancewar kada ƙuri'a a zaɓen da ya gabata zai je domin yin rajista
Ana zanga-zanga a Isra’ila domin sako mutanenta da Hamas ke riƙe da su
Asalin hoton, Reuters
An shiga zanga-zangar gama gari a Isra'ila wanda ƙungiyar da ke fafutikar ganin an sako sauran 'yan ƙasar da ke hannun Hamas a Gaza ke jagoranta.
Masu zanga-zangar suna ƙira ga shugaba Donald Trump da ya taimaka wajen ganin an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da dawo da sauran ƴan ƙasar da ke riƙe a Gaza.
Trump a wani tsokaci da ya yi ya nuna cewa yana da yaƙinin yaƙin zai zo ƙarshe nan da makonni biyu zuwa uku.
Majalisar tsaron Isra'ila na zaman taro a yau Talata domin nazartar daftarin yarjejeniyar da aka gabatar musu, wanda tuni Hamas ta amince da shi.
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Akwai yiwuwar samun ambaliya a jihohin Borno, Jigawa da Yobe - Nimet
Asalin hoton, DESOPADEC MEDIA
Akwai yiwuwar samun ambaliya a jihohin Borno, Jigawa da Yobe, kamar yadda Hukumar Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta sanar a wani hasashen yanayi da ta fitar a shafinta na X.
Hukumar ta ce tsawa da ruwan sama matsakaici na iya sauka a wasu sassan arewacin Najeriya wadda zai iya haddasa ambaliyar ruwan.
NiMet ta bayyana cewa da safiyar yau Talata, ana sa ran ruwan sama a jihohin Borno, Yobe, Jigawa, Gombe, Bauchi, Adamawa, Kaduna da Taraba.
Hakanan, da yamma zuwa dare, ana sa ran yawancin jihohin Arewa za su ci gaba da samun ruwan sama tare da iska da tsawa.
A tsakiyar Najeriya kuwa, hasashen ya nuna cewa za a samu yanayin giragizai da safe, sannan da yamma za a samu ruwan sama matsakaici a wasu sassan Nasarawa, Benue, Kogi, Kwara, Neja, Filato da kuma babban birnin tarayya Abuja.
NiMet ta kuma bayyana cewa a Kudancin Najeriya, da safe ana sa ran yanayi mai giragizai tare da yiwuwar ruwan sama a wurare kaɗan, yayin da a Yammaci ake hasashen ruwan sama a lokuta daban-daban.
Hukumar ta yi gargaɗi ga al’ummar da ke zaune a wuraren da ke da haɗarin fuskantar ambaliya da su ɗauki matakan kariya. Ta kuma shawarci hukumomin agaji da sauran masu ruwa da tsaki da su kasance cikin shiri domin bada taimako idan buƙata ta taso.
Birtaniya ta amince da tallafin karatu kyauta ga ɗalibai 40 daga Gaza
Asalin hoton, HANDOUT
Gwamnatin Birtaniya ta amince da shirin bai wa ɗalibai 40 daga Gaza tallafin karatu kyauta a jami'o'inta nan da makonni.
Ɗaliban Falasɗinawa da suka hada da masu sha'awar karatun Likita da masana kimiya da malamai za su kasance rukunni na farko da za su bar Zirrin domin karatu a Birtaniya tun soma wannan yaƙi shekaru kusan biyu.
Matakin na zuwa bayan shafe watanni ana neman wannan dama a madadin ɗalibai sama da 80 da suka samu tallafin karatun daga jami'o'in Burtaniya a Gaza.
Sai dai akwai bukatar gwamnatin Isra'ila ta tantace kowanne ɗalibi kafin ya bar zirrin zuwa Burtaniya.