Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 15/11/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail, Ahmad Bawage da Abdullahi Bello Diginza

  1. Trump ya yi jawabi ga magoya bayansa karon farko bayan lashe zaɓe

    A karon farko tun bayan nasarar da ya yi a zaɓen shugaban ƙasar Amurka da aka yi kwanaki goma da suka gabata, Donald Trump ya gabatar da jawabi ga magoya bayansa a dabdalar da aka shirya a wurin shakatawarsa da ke Mar-a-Lago a Florida.

    Mista Trump ya ce abu mai muhimmanci da zai yi shi ne kawo karshen yaƙin Rasha da Ukraine da zarar ya sha rantsuwar kama aiki a watan Janairun mai zuwa.

    "Za mu yi aiki tukuru kan Gabas Ta Tsakiya, za kuma mu yi aiki don kawo karshen yaƙin Rasha da Ukraine, dole mu kawo karshen yakin nan," in ji Trump.

    Ya kuma gode wa attajirin nan mai shafin X Elon Musk da Robert Kennedy Junior da sauran waɗanda suka marasa masa baya, inda ya ce za su haɗu tare domin ciyar da Amurka gaba.

  2. Gwamnatin Najeriya ta amince da kasafin kuɗin 2025

    Majalisar zartaswar Najeriya ta amince da kasafin kuɗin ƙasar na 2025 da ya kai naira tiriliyan 47.9.

    Ministan kasafin kuɗi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ne ya bayyana haka ranar Alhamis bayan kammala taron majalisar da shugaba Bola Tinubu ya jagoranta.

    Kasafin kuɗin ya ƙunshi manyan ayyuka da kuma na musamman da za a gudanar a faɗin ƙasar.

    "Mun amince da kasafin kuɗin, kuma za a miƙa shi gaban majalisar dokoki ta ƙasa domin yin nazari da kuma amincewa da shi," in ji Bagudu.

    Ya kuma ce za a ciyo sabon rancen da ya kai naira tiriliyan 9.2 don cike giɓin kasafin kuɗin na shekarar 2025.

    Ya ce an yi hasashen samun bunƙasar yawan kayayyakin da ake samarwa a cikin gida da kashi 4.6 cikin 100.

  3. Ya kamata a ƙara zuba kuɗi a riga-kafin cutar ƙyanda - WHO

    Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi kiran a ƙara zuba jari a shirye-shiryen rigakafin cutar Kyanda, bayan yaduwar cutar mafi muni da aka gani a bara.

    Sama da yara miliyan 22 ne ba a yi musu riga-kafin ba, ko waɗanda ba a kammala yi mu su ba a shekarar da ta gabata, yayin da aka samu ƙaruwar kashi 25 na sabbin waɗanda suka kamu da kyandar.

    A ɓangare guda kuma WHO ɗin ta ce, an samu ɓarkewar cutar a sama da ƙasashe 50, ta kuma yi ajalin sama da mutane 100,000 a faɗin duniya, yawancin su yara 'yan ƙasa da shekara biyar da haihuwa.

  4. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Juma'a - Hajj babbar rana.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.

    Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.