Arnold ya yi watsi da sabunta kwantiragi da Liverpool, Alonso zai bar Leverkusen
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail, Ahmad Bawage da Abdullahi Bello Diginza
Shugaba Tinubu ya karrama marigayi Laftanar Janar Lagbaja da lambar CFR
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya karrama marigayi tsohon babban hafsan sojin saman Najeriya, LaftanaR Janar Taoreed Lagbaja da lambar CFR.
Bola Tinubu wanda ya halarci taron jana'izar marigayin ranar Juma'a a Abuja ya bayyana Taoreed da mutumin da ya zama manuniyar irin nagartar jagoranci a aikin sojin Najeriya.
Asalin hoton, Nigerian Army
Asalin hoton, Nigerian Army
Asalin hoton, Nigerian Army
Asalin hoton, Nigerian Army
Yadda rantsar da shugaban ƙaramar hukuma a Kano ya janyo ce-ce-ku-ce
Asalin hoton, Abba Yusuf/X
A jihar Kano, ana ci gaba da ce-ce-ku-ce da
musayar ra'ayoyi bayan da gwamnan jihar ya rantsar da sabon shugaban ƙaramar
hukumar Kumbotso.
Wata babbar kotun jihar ce ta yi hukunci game da shari'ar
dambarwar shugabancin ƙaramar hukumar wadda daya daga cikin masu jayayya kan
takarar shugabancin ƙaramar hukumar ya shigar.
An shafe lokaci mai tsawo kafin
a rantsar da sabon shugaban karamar hukumar duk kuwa da nasarar da jam’iyyar
NNPP ta samu saboda dambarwar shari’a.
Rahotanni na cewa gwamna Abba Kabir Yusuf , ya rantsar da sabon
shugaban ƙaramar hukumar ta Kumbotso ne bisa dogaro da hukuncin kotun da ya
dakatar da zartar da hukuncin farko, wanda lauyoyin jam’iyyar NNPP suka
nema.
Hotuna: Sarki Sanusi ya naɗa ɗansa DSP Aminu Lamiɗo a matsayin Ciroman Kano
Asalin hoton, Maikatanga
Asalin hoton, Maikatanga
Asalin hoton, Maikatanga
COP29: Ana zargin Azerbaijan mai masaukin baƙi da kama masu rajin kare muhalli
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam sun zargi gwamnatin Azerbaijan da yin amfani da taron COP29 wajen murƙushe masu fafutikar kare muhalli da sauran 'yan adawar siyasa.
Wannan ce shekara ta uku a jere da ake zargin ƙasar da ke karbar baƙuncin taron sauyin yanayi da muzgunawa da hana masu fafutikar dama.
Ƙungiyar 'Climate Action Network' - gamayyar ƙungiyoyin rajin kare muhalli kusan 2,000 - ta shaida wa BBC cewa kare fararen hula na da matuƙar muhimmanci ga duk ƙasashen da ke son samun cigaba a fannin sauyin yanayi.
Gwamnatin Azerbaijan ta yi watsi da iƙirarin tana mai cewa gwamnatin ba ta tsare da kowane irin fursunan siyasa.
Ana zargin shugaban ma'aikatan Netanyahu da sauya bayanai kan yaƙin Gaza
Asalin hoton, Getty Images
An
zargi shugaban ma'aikatan Firaiministan Isra'ila da ƙoƙarin sauya
bayanan wata hira ta wayar tarho, domin a ce Benjamin Netanyahu ya yi gaggawar ɗaukar mataki lokacin da Hamas ta kai harin 7 ga watan Oktoba.
An
buɗe binciken Tzachi Braverman wanda aka zarga da ɗaukar takardun bogi bayan wani
babban jami'in soji ya kai rahoto.
An
bayyana harin da Hamas ta kai a watan Oktoban bara wanda mutane 1,200 suka rasa rayukansu a kudancin Isra'ila a matsayin gazawa irinta ta
farko a tarihin Isra'ila.
Dalilai biyar da ke sa ma'aikatan Najeriya ƙaryar shekarun haihuwa
Asalin hoton, Getty Images
Batun ƙaryar shekarun haihuwa tsakanin ma'aikatan Najeriya shi ne ya zamo abin tattaunawa a ƙasar tun bayan da majalisar kula da harkokin shari'a ta Najeriya wato NJC ta bayar da shawarar yi wa wasu manyan alƙalai biyu ritaya saboda laifin yin ƙarya a shekarunsu na haihuwa.
Cikin wata sanarwa a ranar Juma'a, National Judicial Council (NJC) ta ce ta gano Alƙalin Alƙalai na jihar Imo T. E. Chukwuemeka Chikeka, da shugaban kotunan shari'ar Musulunci na jihar Yobe Babagana Mahdi sun aikata laifi.
Haka nan majalisar ta ɗauki mataki kan wasu alƙalan da suka haɗa da na yin gargaɗi, da hana su albashi, da kuma saka musu ido bisa laifuka daban-daban da suka aikata.
Ana dai alaƙanta ƙaryar shekaru tsakanin ma'aikata a Najeriya da wasu dalilai manya guda biyar kamar haka:
Masu haƙar ma'adinai sama da 4,000 na ɓoye saboda tsoron kame a Afrika ta Kudu
Asalin hoton, Getty Images
Ministan ƴansandan Afrika ta Kudu, Senzo Mchuni ya ziyarci wurin haƙar ma'adinan da ake tunanin sama da mutane 4,000 sun ki fito wa saboda tsoron kame.
Mahukunta sun bayyana su a matsayin masu laifi bayan an hana shigar musu da abinci da ruwan sha da nufin a tilasta musu fito wa.
Rahotannin sun bayyana cewa da dama daga cikin su sun zo ne daga makwabtan ƙasashe da suka haɗa da Mozambique.
Jam'iyyar sabon shugaban Sri Lanka ta kama hanyar lashe zaɓen ƴan majalisa
Haɗakar
jam'iyyun siyasa karkashin jagorancin sabon shugaban Sri Lanka na sahun gaba a
zaɓen 'yan majalisun da aka gudanar.
Yayin da aka kirga kusan rabin kuri'un da aka kaɗa, jam'iyyar shugaba Anura
Kumara Disanayaka ta National People’s Power ta samu sama da kashi 60 cikin 100
na kuri'un.
Idan aka tabbatar da sakamakon, wannan babbar nasara ce ga Mr Disanayaka,
wanda ya ke buƘatar kashi biyu bisa uku domin rike madafun iko.
A
watan Satumba ne aka zaɓi Mr Dissanayaka, inda ya yi alkawarin
magance matsalar cin hanci da rashawa a Sri Lanka.
Kotun koli ta yi watsi da ƙarar da ke kalubalantar dokar kafa EFCC
Asalin hoton, Supreme Court
Kotun kolin Najeriya ta ƙori ƙarar da wasu manyan alkalai na jihohi suka shigar, inda suke kalubalantar dokar da ta kafa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC.
Tawagar alkalai mai mambobi bakwai da alkali Uwani Abba Aji ta jagoranta, sun amince da ƙorar ƙarar saboda ba ta cancanci a saurare ta ba.
Ƙarar wadda alkalai na jihohi 16 suka shigar, na neman a rushe EFCC.
Yayin da wasu jihohi suka janye daga ƙarar, wasu sun ki yin haka inda suka ce za su kalubalanci lamarin.
Jihohin da suka shigar da ƙarar sun haɗa da Ondo da Edo da Oyo da Ogun da Nasarawa da Kebbi da Sokoto da Jigawa da Enugu da Benue da Anambra da Filato da Cross River da kuma Niger.
Sai dai a lokacin sauraron ƙarar ranar 22 ga watan Oktoba, jihohin Imo da Bauchi da kuma Osun su ma sun shiga cikin ƙarar yayin da Anambra da Ebonyi da kuma Adamawa suka sanar da janye wa daga ƙarar.
Sabon shugaban Sri Lanka ya gode wa jama'a saboda zaɓar jam'iyyarsa
Asalin hoton, Getty Images
Sabon
shugaban Sri Lanka ya gode wa masu kaɗa ƙuri'a saboda
yadda suka bai wa jam'iyyarsa mai sassaucin ra'ayi damar jagorantar gwamnatin
haɗaka a zaɓen cike gurbi
na ƴan majalisa.
Sakamakon
zaɓen ya bayyana
irin adawar da an kasar suke yi da yanayin matsin tattalin arziki da
gwamnatocin baya suka jefasu.
Gagarumar nasarar da ya samu za ta taimaka masa wajen farfaɗo da
tattalin arziki da kawo sauyi a siyasa, alwashin da ya ɗauka lokacin yakin neman
zabe.
Gwamnatin
Haɗakar ta samu kusan kashi 62 na kuri'u har a yankin Jaffna da ke kudancin Sri
Lanka a karon farko tun bayan samun yancin kai daga Birtaniya.
An ayyana dokar ta-ɓaci a lardin Punjab kan gurɓacewar iska
Asalin hoton, EPA
An
ayyana dokar ta-ɓaci a yankunan lardin Punjab na Pakistan sakamakon gurɓacewar iska.
Gwamnatin
yankin ta dakatar da gine-gine, ta kuma bayar da umarnin rufe makarantu na ƙarin
mako guda yayin da ɗaliban jami'a
za su din ga ɗaukar darasi
ta internet.
Wani
minista ya bayyana cewa akwai yiwuwar a hana fita tsawon kwanaki uku a mako mai zuwa idan yanayi bai sauya ba.
Lardin
Lahore na fuskantar gurbacewar iska kowanne lokacin bazara idan iska ta zuƙo ƙura da hayaƙin wutar da gonaki suke kunnawa ba tare da izini
ba.
Harin Isra'ila ya kashe ma'aikatan agaji 15 a Lebanon
Asalin hoton, AFP via Getty Images
Jami'ai
a Lebanon sun ce aƙalla
ma'aikatan agaji 15 aka kashe a wani hari da Isra'ila a arewa maso gabashin ƙasar.
Harin
da aka kai birnin Baalbek ya sauka a wata cibiyar tsaron gwamnati wadda ba ta da
alaƙa da Hezbollah.
Gwamnan lardin, Bachir Khodr, ya ce waɗanda lamarin ya rutsa da su sun haɗa da shugaban jami'an tsaro na civil defence a yankin, Bilal Raad.
Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta yi Alla-wadai da mummunan harin.
Sojojin Isra'ila ba su ce uffan ba kan harin, waɗanda ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta kwatanta da mai muni.
Rahotanni sun bayyana cewa sabon harin Isra'ila a ƙauyukan da ke kudancin Beiruta ya lalata gine-gine.
Majalisar harkokin shari'a ta Najeriya ta nemi a kori alƙalai kan ƙarya a shekarunsu
Asalin hoton, Getty Images
Majalisar kula da harkokin shari'a a Najeriya ta bayar da shawarar yi wa wasu manyan alƙalai biyu ritaya saboda laifin yin ƙarya a shekarunsu na haihuwa.
Cikin wata sanarwa a ranar Juma'a, National Judicial Council (NJC) ta ce ta gano Alƙalin Alƙlai na jihar Imo T. E. Chukwuemeka Chikeka, da shugaban kotunan shari'ar Musulunci na jihar Yobe Babagana Mahdi sun aikata laifi.
Haka nan majalisar ta ɗauki mataki kan wasu alƙalan da suka haɗa da na yin gargaɗi, da hana su albashi, da kuma saka musu ido bisa laifuka daban-daban da suka aikata.
A cewar sanarwar, binciken NJC ya gano alƙalin alƙalan na Imo na da ranakun haihuwa biyu na 27 ga watan Oktoban 1956 da 27 ga Oktoban 1958, yayin da shi kuma shugaban kotunan shari'a na Yobe yake da kwanan wata har uku daban-daban.
Bisa wannan dalili ne majalisar ta ce ta bai wa gwamnatin jihar Imo da ke kudancin Najeriya shawarar yi wa Mai Shari'a Chikeka ritayar dole tare da ƙwace albashin da ya karɓa tun daga ranar 21 ga watan Oktoban 2021.
Kazalika, majalisar ta bai wa gwamnatin jihar Yobe shawarar yi wa Mai Shari'a Babagana Mahadi ritaya ta tilas, wadda ya kamata ya yi tun shekara 12 da suka wuce, sannan kuma ya dawo da albashin da ya karɓa na tsawon waɗannan shekarun.
Duk da cewa an fara gudanar da binciken tun kafin shugabar majalisar kuma alƙaliyar alƙalai ta Najeriya Kekere-Ekun ta samu muƙamin, matakan sun yi daidai da alwashin da ta ɗauka na dawo kima da martabar ɓangaren shari'a a Najeriya.
Lamarin na zuwa ne yayin da ƙungiyoyi da 'yan gwagwarmaya ke caccakar Ministan Abuja Nyesom Wike saboda bai wa wasu alƙalai 40 kyautar gidaje, abin da ya ce manufa ce ta gwamnatin Bola Tinubu yake aiwatarwa.
Trump ya naɗa Robbert Kennedy JR sakataren lafiya
Asalin hoton, Getty Images
Zaɓaɓɓen
shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da Robbert Kennedy JR a matsayin
sakataren lafiya na ƙasar.
Mukamin
da ya bai wa Robert Kennedy Junior wani abu ne da zai janyo rarrabuwar kawuna
tsakanin 'yan majalisa musamman na adawa.
A jawabin da ya yi daga wurin shakatawa na Mar-a-lago, Mr Trump ya
yaba wa Mr Kennedy, inda ya ce babu wanda zai iya aikin inganta fannin lafiya a
Amurka kamar shi.
Kennedy
mutum ne mai janyo cece-kuce kan allurar
riga-kafi, musamman ra'ayinsa na nuna shakku kan riga-kafi lokacin annobar Korona.
An fara jana'izar tsohon babban hafsan sojin ƙasan Najeriya Janar Lagbaja
Asalin hoton, Nigerian Army/X
An fara shirye-shiryen binne tsohon babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya a Abuja, Janar Taoreed Lagbaja.
Ana gudanar da jana'izar ce a Abuja, babban birnin Najeriya.
Gwamnatin Najeriya ta ce babban hafsan sojin na ƙasa ya rasu ranar ne 5 ga watan Nuwamba, 2024, yana da shekara 56 a wani asibiti a Lagos, bayan fama da rashin lafiyar da ba a bayyana ba.
Kafin tabbatar da rasuwar, an fara raɗe-raɗin cewa babban hafsan ya rasu a sanadiyar cutar kansa a wani asibiti a ƙasar waje, inda masu yaɗa maganganun suka riƙa cewa an ɓoye rasuwar ne saboda masu rububin neman maye gurbinsa.
An rufe makarantun firamare a faɗin Delhi saboda hazo
Asalin hoton, Getty Images
Za a rufe dukkan makarantu firamare a birnin Delhi na ƙasar Indiya saboda gurɓacewar iska,a cewar jami'ai.
A wata sanarwa a shafin X, ministan birnin Delhi, Atishi Marlena Singh, ya ce za a koma ɗaukar darussa ta intanet har sai abin da hali ya yi saboda hazo da ya mamaye birnin.
Delhi da makwabtan birane na fuskantar gurɓacewar iska waɗanda aka ce barazana ne ga lafiyar mutane.
A ranar Alhamis, iskan da ya gurɓace ya kai sau 50, wanda hukumar lafiya ta duniya ta ce shi ne mataki da ake so na iska mai lafiya.
Delh da wasu jihohi da ke arewacin ƙasar ta Indiya na fuskantar hazo lokacin bazara saboda ƙaruwar yanayi da iska mara kyau da kuma gurɓataccen iska ababen hawa ke fitar wa.
Asalin hoton, AFP
An girke ƴansanda don tabbatar da tsaro a zaɓen gwamnan Ondo
An girke ƴansanda a faɗin jihar Ondo gabanin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar gobe Asabar.
Ƴansandan riƙe da makamansu na ta sintiri don tabbatar da tsaro da kuma ganin komai ya tafiya cikin tsakani.
Rundunar ƴansandan Najeriya dai ta ce a shirye take tsaf domin daƙile duk abin da zai kawo barazana yayin zaɓen.
Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta ce ta kama 'ɗan leƙen asirin Faransa'
Asalin hoton, FB/PRESIDENCE DE LAPERUBLIQUE DU NIGER
Gwamnatin mulkin sojin jamhuriyar Nijar ta ce ta kama wani da take zargin ɗan leƙen asirin Faransa da ke zaune a ƙasar.
Kafar talabijin ɗin ƙasar Tele Sahel ya ruwaito cewa wanda ake zargin, mai suna Marius Barcea, ya shiga ƙasar ba bisa ka'ida ba ranar 12 ga watan Nuwamba a hanyar amfani da fasfo ɗin ƙasar Romania.
Amma kwana guda bayan shigarsa ƙasar aka kama shi.
Kafar talabijin ɗin ba ta yi wani ƙarin bayani ba kan mutumin da aka kama.
Wani shafi mai wallafa labarai kan ayyukan gwamnatin mulkin sojoji a Nijar da Mali da kuma Burkina Faso AES, ya kwatanta kama Barcea a matsayin wani koma baya ga Faransa.
"Kamen yana ƙara nuna zarge-zarge da gwamantin Nijar ɗin ta sha yi wa Faransa, wanda ta ce tana son wargaza ƙasar da kuma janyo ruɗani a faɗin yankin Sahel," in ji shafin na AES.
Ta ce duk da Faransa ta sha musanta zarge-zargen, amma ana ƙara samun hujjoji da ke nuna cewa Paris ɗin na yaƙin sunkuru kan Nijar, ta hanyar yaɗa labaran karya da kuma sauran abubuwa.
Harkokin yau da kullum na tafiya gabanin zaɓen gwamnan Ondo
Al'ummar jihar Ondo na shirin fita rumfunan zaɓe ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba, domin zaɓen sabon gwamnan jihar.
Gabanin fita kaɗa kuri'a a gobe, harkokin kasuwanci da na yau da kullum na ci gaba da tafiya cikin tsanaki.
Wakilin BBC a jihar ta Ondo, ya ruwaito cewa harkoki na tafiya yadda ya kamata ba tare da wata matsala ba.
Abin da ya kamata ku sani kan mayan ƴan takara a zaɓen gwamnan jihar Ondo
Asalin hoton, @LuckyAiyedatiwa, @Iwillvote Sola Ebiseni, @A_AgboolaAjayi, @Abbas Mimiko/Facebook/X
A ranar Asabar ne za a gudanar da zaɓen gwamnan jihar Ondo da ke yankin kudu maso yammacin Najeriya.
Jihar Ondo na daga cikin jihohin ƙasar ba a gudanar da zaɓukansu lokaci guda da na sauran jihohi.
Zaɓen na zuwa ne wata 11 bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu, wanda ya shafe tsawon lokaci yana da fama da jinya.
Hukumar zaɓen ƙasar, INEC ta ce mutum miliyan 2,053,061 ne suka yi rajistar zaɓe a faɗin jihar, yayin da matasa ke da kasi 35.41 cikin 100 na waɗanda suka yi rajistar zaɓen.