Rufewa
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labaran na yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa domin kawo muku sabbin labarai.
Amma kafin nan, muke cewa mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Ahmad Bawage da Abdullahi Bello Diginza
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labaran na yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa domin kawo muku sabbin labarai.
Amma kafin nan, muke cewa mu kwana lafiya.
Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya yi watsi da raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa yana shirin ficewa daga jam'iyyarsa ta LP domin komawa APC mai mulkin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da mataimakinsa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ferdinand Ekeoma ya fitar, gwamnan ya bayyana raɗe-raɗin da ''ƙarya maras tushe balle makama''.
A ƴan kwanakin nan an yi ta yaɗa jita-jitar cewa gwamna Otti ya gana da takwaransa na jihar Imo, Hope Uzodinma da nufin shirya yadda zai koma jam'iyyar APC.
To sai dai cikin sanarwar, Mista Otti ya ce bai taɓa yin wani taro da gwamnan Imo da wannan manufa ba.
''Haƙiƙa bayan kammala taron majalisar tattalin arziki da aka gudanar ranar Alhamis, 24 ga watan nan, Gwamna Otti tare da wasu takwarorinsa sun halarci bikin murnar zagayowar ranar haihuwar tagwayen ƴaƴan gwamnan Imo, don haka taro ne na biki, ba shi da alaƙa da siyasa'', in ji sanarwar.
A cikin makon nan ne dai gwamnan jihar Delta ya koma jam'iyyar ta APC bayan ficewa daga PDP, babbar jam'iyyar hamayyar ƙasar.
An kuma jiyo shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje na cewa akwai wasu ƙarin gwamnoni da ke shirin komawa jam'iyyar APC bayan ficewa daga jam'iyyunsu.
Shugaban ƙasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan wata babbar fashewa da ta auku a tashar ruwan ƙasar da ake sauke kontenoni, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyar tare da jikkata fiye da 700.
Kafofin yaɗa labaran Iran sun ce fashewar - da ta auku a tashar ruwa ta Shahid Rajaee da ke kusa da birnin Bandar Abbas na kusa da gaɓar ruwa - ana iya jiyo ƙararta daga tazarar kilomita 50.
Jami'ai a tashar ruwan sun ce kontenoni masu yawa ne ɗauke da sinadarai suka fashe, lamarin da ya haddasa tashin gobara.
Shugaban Falasɗinawa, Mahmoud Abbas ya naɗa mataimakinsa a karon farko, wanda kuma ake tunanin shi ne zai gaje shi.
Hussein al-Sheikh mai shekara 89, babban hadimin Mista Abbas ne, wanda ya taɓa riƙe muƙamin ministan harkokin ayyukan gwamnati.
Sabon mataimakin ya yi fice a abota da ƙasashen Isra'ila da kuma Amurka.
Naɗin nasa na zuwa ne bayan kiraye-kirayen ƙasashen duniya na faɗaɗa hukumar gwanatin Falasɗinawa tare da yi mata garambawul, ta yadda za ta faɗaɗa ayyukanta zuwa Zirin Gaza bayan ƙare yaƙin Gaza.
Rundunar sojin Jamhuriyar Nijar ta ce an kashe sojojinta 12 a wani hari da aka kai yammacin ƙasar.
Dakarun na Nijar sun ce an yi wa sojojin kwantan ɓauna ne a yankin Tillaberi da ke kusa da kan iyakar ƙasar da Mali.
Tuni dai sojojin suka ce sun kama mutum biyu bisa zargin hannu a harin.
A baya-bayan nan yankin Tillaberi na fuskantar yawaitar hare-haren masu iƙirarin jihadi.
Ko a watan da ya gabata ma fiye da fararen hula 40 aka kashe a harin da aka kai wani masallacci.
Sojojin na Nijar sun dora alhakin harin kan ƙungiyar IS da ke yankin Greater Sahara.
Shugabannin ƙasashen duniya da sarakuna sun cika birnin Vatican domin shaida jana'izar Fafaroma Francis.
Daga cikin fitattu a dandalin St Peter da safiyar ranar Asabar akwai Yarima William na Birtaniya da shugaban Amurka Donald Trump da wanda ya gada, Joe Biden da Firaiministan Birtaniya Sir Keir Starmer da kuma shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Halartar shugabannin na zuwa ne a daidai lokacin da diplomasiyyar duniya ke cikin garari, yayin da Trump ya gana da Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky gabanin fara jana'izar.
An samu hatsaniya bayan da aka ji ƙarar harbe-harbe a wurin gangamin goyon bayan Ministan Abuja,Nyesom Wike da aka gudanar a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.
Kafofin yaɗa labaran Najeriya sun ce gangamin wanda ƙungiyar NEW Associates mai goyon bayan wike ta shirya an gudanar da shi ranar Asabar.
Ana tsaka da gangamin en lkacin da aka riƙa jin ƙarar harbe-harbe a kusa da inda ake gangamin. Daga baya an maido da zaman lafiya.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai, Sakataren ƙungiyar NEW Associates a jihar Bayelsa, Comrade Ebilade Ekerefe, ya ce babu wabin da zai hana ci gaba da gangamin.
Rundunar ƴansanda a jihar Oyo ta ce ta gano wata ƙungiya da ke safarar mutane a Ibadan, babban birnin jihar.
Ƴansandan sun ce sun ceto mutum 83 haɗe da wani yaro a wani gida a yankin Orogun da ke Ibadan, inda ake kyautata zaton an ajiye mutanen na tsawon lokaci, kamar yadda gidan talabijin na Channels a Najeriya ya ruwaito.
Binciken farko da aka gudanar, ya nuna cewa mutanen ƴan asalin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo ne - waɗanda aka shigo da su zuwa Najeriya kan yaudarar cewa za a sama musu ayyukan yi.
Ana kuma zargin cewa ɓata-garin sun karɓi kuɗaɗe dala da yawa a hannun iyayen waɗanda suka yi safararsu.
Yanzu dai mutanen da aka ceto suna hedkwatar ƴansandan jihar ta Oyo da ke Ibadan, inda hukumomi ke ci gaba da yin bincike domin gano ƙarin masu hannu a lamarin.
Fadar Sarkin Musulmi a Najeriya Mai Alfarma Sa'ad Abubakar III ta buƙaci al'ummar Musulmi da su fara duba sabon watan Dhul-Qadah daga gobe Lahadi.
Kwamitin ganin wata na Najeriya a fadar Sarkin Musulmi ya ce ranar Lahadi 29 ga watan Shawwal daidai ne da 27 ga watan Afrilun, 2025.
Sanarwar da aka wallafa a shafin kwamitin ganin watan a X, ta buƙaci mutane da su kai rahoton ganin watan ga fadar Sarkin Musulmi da ke Sokoto.
Aƙalla mutum 400,000 ne suka halarci jana'izar Fafaroma Francis a dandalin St Peter's da ke Vatican.
Haka kuma sun ga lokacin da aka ɗauki gawarsa zuwa wajen da aka binne shi a cocin Santa Maria, a cewar ministan harkokin cikin gidan Italiya.
''Mun yi kiyasin cewa mutane 400,000 ne tsakanin waɗanda suka halarci dandalin St Peter's da kuma waɗanda suka tsaya kan tituna suka kalli jana'izar," in ji Matteo Piantedosi.
Fadar Vatican ta tabbatar da cewa an binne Fafaroma Francis a cocin Santa Maria Maggiore.
"Fafaroma Francis shi ne mutum na farko cikin shekara 100 da aka binne a wajen Vatican, kuma an binne shi a asirce, inda makusantansa suka yi masa gaisuwar ban-girma," a cewar sanarwar da fadar ta fitar.
Cocin dai yana wajen Vatican da ke tsakiyar birnin Rome.
Wata ƴar ɗarikar katolika da ta halarci jana'izar Fafaroma Francis a dandalin St Peter's, mai suna Beatrice ta ce ''A gare ni, mutuwar Fafaroma Francis babban rashi ne,'' kamar yadda ta faɗa wa BBC.
''A wajensa na ga mutum mai tsarki wanda ya ɗauki kowa a matsayin nasa. Mutum ne mai son zaman lafiya kuma ba ya nuna bambancin yare ko fata.
''Mun yi babban rashi. Ina addu'ar wanda za a zaɓa a matsayin Fafaroma na gaba zai yi koyi da abin da ya Francis ya bari.''
Kamar yadda muke ta bayar da rahotanni, za a binne gawar Fafaroma Francis ne a cocin Santa Maria Maggiore da ke birnin Rome.
Shi ne Fafaroma na farko tun bayan Leo XIII, wanda ya mutu a 1903 - da za a binne a wajen Vatican.
Kowane lokaci idan ya koma birnin Rome daga balaguro, ya sha ziyartar Santa Maria Maggiore.
Yanzu dai motar da ke ɗauke da gawar Fafaroma Francis isa cocin Santa Maria Maggiore da ke birnin Rome.
Masu ɗaukar gawa su ɗaga akwatin sama daga cikin mota zuwa cikin majami'ar da za a binne shi.
Mun sake samun sabbin bayanai daga fadar Vatican, inda fadar ta ce mutum 250,000 ne suka halarci wajen jana'izar Fafaroma Francis a dandalin St Peter's.
Hakan na nufin an samu ƙarin sama da 50,000 kan sanarwar da suka bayar a farko.
Yanzu dai an kammala addu'o'i a wajen jana'izar Fafaroma Francis.
Motar da ke ɗauke da gawarsa ta tashi cikin ayari zuwa cocin Santa Maria Maggiore da ke birnin Rome domin binne shi.
Ayarin zai bar birnin Vatican, inda zai yi tafiyar kilomita kusan shida - zai kuma bi ta kogin Tiber.
Daga nan za su ɗau hanyar zuwa tsakiyar birnin Rome har su kai Piazza Venezia, kafin su juya zwa ɓangaren arewaci sannan su isa cocin na Santa Maria Maggiore.
Mutane za su iya kallon yadda ake tafiya da gawar kaɗai a kan tituna, maimakon bin bayanta.
Ba za a binne shi a bainar jama'a ba a cikin cocin, duk da cewa dandazon mutane sun fara taruwa a wajen.
Babban limami a fadar Vatican Giovanni Battista Re ya saka wa gawar Fafaroma Francis albarka ta hanyar zuba ruwa mai tsarki - wata alama ta tsarkakewa.
Yanzu kuma an kaɗa kararrawa har sau uku - yayin da aka doshi tsakar rana.
An yi tsit a wajen jana'izar, sai wani jirgi mai saukar ungulu da ke shawagi a sama.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC, ta ayyana neman wasu jami'an CBEX waɗanda take zargi da hannu a damfarar ƴan Najeriya miliyoyin kuɗaɗe a wani tsarin zuba kuɗi.
Wata sanarwa da EFCC ta wallafa a shafinta ranar Juma'a, ta ce tana zargin mutanen takwas da yaudarar jama'a su zuba kuɗi don samun riba - daga bisani suka tsere da kuɗaɗensu.
Hukumar ta bayyana sunayen mutanen da Seyi Oloyede da Emmanuel Uko da Adefowora Oluwanisola da Adefowora Abiodun Olaonipekun.
Sauran sun waɗanda ta ce ƴan ƙasashen waje ne sun haɗa da Johnson Otieno da Israel Mbaluka da Joseph Kabera da kuma Serah Michiro.
"Muna son sanar da al'umma cewa muna neman waɗannan mutane ruwa a-jallo saboda zargin damfarar mutane a wani tsarin zuba kuɗi na intanet wanda ake kira CBEX," in ji EFCC.
Hakan na zuwa ne bayan da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bai wa jami'an EFCC ɗin damar kame da kuma tsare mutanen da aka samu da hannu wajen yaɗa tsarin na CBEX.
Kusan mutum 140,000 ne ke taruwa a dandalin St Peter's da kuma wasu tituna da ke kusa, don halartar jana'izar Fafaroma Francis, a cewar ƴansadan Italiya.
Mutanen sun kunshi 40,000 waɗanda ke cikin dandalin na St Peter;s, wanda ya cika makil.