Mutum bakwai sun mutu a harin Isra'ila a kudancin Lebanon
Mutum bakwai sun mutu yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon wani hari da Isra'ila ta kai a kudancin Lebanon a safiyar Asabar, a cewar Kamfanin Dillancin Labaran Ƙasar.
Rahotanni sun ce wani jirgin yaƙin Isra'ila ya kai hari wani gida da ke wajen ƙauyen Ansar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutanen tare da rusa gidan gaba ɗaya.
An kuma ruwaito cewa sojojin Isra'ila sun tarwatsa wasu gidaje a garin Bint Jbeil da ke kusa da kan iyaka.
Wannan shi ne mafi yawan mutanen da suka mutu a hari guda tun bayan yarjejeniyar watan Yuni da ta rage faɗace-faɗace tsakanin Isra'ila da Hezbollah.
A gefe guda, babban sakataren Hezbollah, Naim Qassem, ya zargi jami'an Lebanon da matsa wa rundunar sojin ƙasar lamba ta hanyar aiwatar da yarjejeniyar da ta haɗa da kwance ɗamarar Hezbollah da tura sojojin Lebanon zuwa kudancin ƙasar.