Trump ya bukaci Iran ta biya diyyar sojojin Amurka da fararen hular da ta kashe
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya bukaci Iran ta biya diyyar sojojin Amurka da fararen hular da ya ce Iran ta kashe ko raunata su a hare-hare daban-daban da ta kai.
Trump ya bayyana hakan ne bayan wasu jami'an Iran sun bukaci Amurka ta biya diyya kan ɓarnar da suka ce ta yi wa Iran a cikin watanni biyar na rikicin da kasashen biyu suka yi.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce batun biyan diyya bai taba tasowa ba a tattaunawar da Amurka da Iran suka yi.
Ya ce: "Amma wannan ra'ayi ne mai ban kyau, domin yanzu ina bukatar Iran ta biya diyya kan duk mutanen da ta kashe ko ta jikkata."
Trump ya kuma zargi Iran da hannu wajen kashe ko raunata sojojin Amurka ta hanyar bama-bamai da aka dasa a gefen tituna da kuma wasu hare-hare da ya ce an kai a karkashin jagorancin Janar Qassem Soleimani.
Trump ya ce ya umurci wakilan Amurka da su gabatar da buƙatar diyya tare da neman a cimma matsaya a kansa a duk wata tattaunawa da za a yi nan gaba da Iran.
Ya kuma bukaci Iran ta biya diyya ga iyalan daruruwan dubban masu zanga-zangar da ya zargi gwamnatin Iran da kashewa cikin shekaru 50 da suka gabata.
A cewar Trump, ya kamata a kuma biya diyya kan mutanen da ya ce an kashe a cikin watanni biyar da suka gabata.