Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 14/02/2025

Wannan shafi ne d ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 14/02/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi, Abdullahi Bello Diginza da Ahmad Bawage

  1. Gwamnonin kudu maso yammacin Najeriya sun ce za su kafa rundunar tsaron haɗin gwiwa

    Gwamnonin yankin kudu maso yammacin Najeriya sun amince da kafa wata rundunar tsaron haɗin gwiwa da za ta riƙa sanya idanu kan matsalolin tsaro a yankin.

    Cikin wata sanarwar bayan da taro da ƙungiyar gwamnonin yankin ta fitar, bayan wani taro da ta gudanar a fadar gwamnatin jihar Legas, ta ce matakin ya zama wajibi, sakamakon rahotonin ɓullar ƙungiyar ISWAP da wasu ƙungiyoyin ƴanbindiga a yankin.

    Cikin watan Janairu ne gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya ce ƴanbindigar da ake fattaka daga wasu yankunan arewacin ƙasar na kwarara zuwa wasu sassan jiharsa.

    Lamarin da ya sa masu ruwa da tsaki na yankin - ciki har da ƙungiyar cigaban Yarabawa ta Afenifere - suka riƙa kiraye-kirayen ɗaukar matakan daƙile hakan.

    Ƙungiyar gwamnonin yankin ta ce ɓullar ƴanbindigar a yankin babbar barazana ce ga zaman lafiya da tsaron ilahirin yankin kudu maso yammacin ƙasar.

    Gwamnonin sun kuma ce sabuwar rundunar za ta yi aiki rundunar ƴansanda da sauran jami'an tsaro domin tabbatar da tsaron yankin.

    Shugaban ƙungiyar, wanda shi ne gwamnan jihar Legas ya ce za a samar wa sabuwar rundunar cikakkun kayan aiki na zamani ciki har da jirage marasa matuƙa.

    Taron ya samu halartar duka gwamnonin yankin kudu maso yammacin ƙasar.

  2. Ana buƙatar dala biliyan shida don tallafa wa miliyoyin ƴan Sudan - MDD

    Babban Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce ana buƙatar da dala biliyan shida a wannan shekara kaɗai domin magance buƙatun miliyoyin mutanen da yaƙin Sudan ya ɗaiɗaita.

    A lokacin da yake jawabi a babban taron bayar da tallafi da ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta goyi baya, Mista Guterres ya ce Sudan na cikin halin buƙatar agaji da ba a ''taɓa ganin irinsa ba'' a nahiyar Afirka

    Taron na gudana ne a birnin Addis Ababa na ƙasar Habasha tare da taron shekara-shekara na shugabannin ƙasashen ƙungiyar haɗin kan Afirka ta AU.

    Mista Guterres ya kuma yi kira a kawo ƙarshen shigar da makamai zuwa Sudan, wanda ya ce hakan ne ke ƙara rura wutar yaƙin da ake ɗauki kusan shekara biyu ana gwabzawa, yana mai cewa ''dole ne a dakatar da shigar makaman''.

    An sha zargin ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da mara wa mayaƙan RSF, ɗaya daga cikin ɓangarorin da ke yaƙi da juna a ƙasar, ciki har da samar mata da makamai, zargin da ƙasar ta sha musantawa.

  3. Cutar Lassa ta kashe mutum 70 cikin wata guda a Najeriya - NCDC

    Hukumar Daƙile Cutuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya, NCDC ta ce cutar zazzaɓin Lassa ta kashe mutum 70 a farkon wannan shekarar.

    Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X, ta ce mutum 1,552 ne ake sa ran sun kamu da cutar, yayin da ta tabbatar da kamuwar mutum 358.

    Sanarwar da hukumar ta fitar wanda ta kammala haɗawa a ranar 2 ga watan Fabrairun da muke ciki, ya nuna cewa zuwa ranar haɗa rahoton, jihohi 10 aka tabbatar da ɓullar cutar a faɗin ƙananan hukumomi 58.

    Jihohin da aka fi samun mace-macen sakamakon cutar sun haɗa da Taraba inda mutum 18 suka mutu, sai Ondo mai 17 da Edo mai 11 sai Bauchi da Ebonyi masu 6 kowanne da Gombe mai 5, sai Kogi mai 4 da kuma jihohin Nasarawa da Plateau masu uku jimilla.

    Rahoton na NCDC ya kuma nuna cewa jihohin Ondo da Edo da Bauchi ne ke da kashi 75 cikin 100 na waɗanda aka tabbatar suna ɗauke da cutar.

    Zazzaɓin Lassa dai cuta ce da ake kamuwa da ita daga mu'amala da wasu dabobbi dangin ɓeraye.

  4. Mutum 11 sun mutu bayan fashewar wata mota a Pakistan

    Jami'ai a yankin kudu masu yammacin Pakistan sun ce aƙalla mutum 11 sun mutu sakamakon fashewar wata motar da ke ɗauke da masu haƙar ma'adinai a yankin Harnai da ke lardin Balochistan.

    Jami'an yankin sun ce suna ci gaba da bincike kan abin da ya haifar da fashewar, to amma ana kyautata zaton abubuwan fashewa ne da ƴanbindiga ke amfani da su.

    Lardin Balochistan mai albarkar ma'ainai ya shafe gomman shekaru yana fama da matsalolin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai na ƙabilar Baloch.

  5. Tinubu ya isa Ethiopia domin taron haɗin kan Afirka

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya isa birnin Addis Ababa, na ƙasar Ethiopia domin halartar taron shugabannin ƙasashen ƙungiyar Afirka ta AU.

    Tun a ranar 5 ga watan Fabrairu ne Shugaba Tinubu ya fice daga Najeriya zuwa Faransa domin ziyarar 'ƙashin kai'.

    Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar, ya ce Tinubu ya isa Ethiopian ne daga Faransa cikin daren da ya gabata.

    Shugaban na Najeriya ya samu tarba daga jami'an ofishin jakadandin ƙasar a Ethiopian, inda ministan harkokin wajen ƙasar Amb. Yusuf Tuggar ya jagoranci tarbar.

    Taron shugabannin ƙasashen ƙungiyar AU - karo na 38 ɗin da za a gudanar a Ethiopian - na zuwa ne a daidai lokacin da Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo ke fama da rikice-rikice a yankin gabashin ƙasar.

  6. UAE ta yi kiran dakatar da wuta a yaƙin Sudan

    Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi kiran a dakatar da wuta domin shigar da kayan agaji zuwa Sudan, gabanin fara azumin watan Ramadan nan da makonni biyu masu zuwa.

    Daular Larabawar ta ce ta na son samar da dala miliyan 200 domin kayan agaji ga Sudan a wannan lokacin.

    Ministar harkokin wajen ƙasar, Reem bint Ebrahim Al Hashimy, ce ta sanar da hakan a lokacin taron masu ruwa da tsaki kan yaƙin na Sudan da aka gudanar a birnin Addis Ababa na ƙasar Habasha.

    Ana yawan zargin Dalaular Larabawa ta hannu wajen taimaka wa mayaƙan RSF na Sudan da makamai, zargin da ta sha musantawa.

  7. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a da Hausawa ke yi wa laƙabi da Hajji babbar rana.

    Sannunmu da sake haɗuwa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku ci gaba da kasancewa da mu a wannan shafi domin samun sahahai kuma ingantattun labaran duniya.