Kyaftin ɗin Liverpool, Virgil van Dijk, ya ce akwai “wani abu da suka rasa” a cikin ƙungiyarsu bayan sun tashi 1–1 da Burnley da ke fama da matsala a wasan Premier League da suka kara ranar Asabar a Anfield.
Liverpool, mai rike da kofin gasar, wadda ta yi canjaras huɗu a jere Premier League, magoya bayanta sun yi ta yi ƴan wasa ihu bayan tashi daga karawar.
Florian Wirtz ne ya ci wa Liverpool ƙwallon farko — mintuna 10 baya Dominik Szoboszlai ya ɓarar da fanariti — amma Marcus Edwards ne ya farke wa Burnley.
“Fushi da takaici shi ne kalmar da take zuciyata,” in ji Van Dijk..
“Muna da sauran awa 48 domin mu tantance kanmu tare da kociyoyinmu, za mu yi nazari, sannan dole ne mu ɗauki mataki.
“Zan ce a halin yanzu akwai wani abu da muka rasa, kuma muna son mu san ko menene.”
Wannan ne karo na farko tun kakar 1980–81 da Liverpool ta kasa doke kowacce daga cikin ƙungiyoyin da hau Premier League a wasannin da ta yi da su a Anfield.
A halin yanzu tana da tazarar maki bakwai a bayan Aston Villa da ke matsayi na uku, wacce kuma tana da wasa ɗaya ranar Lahadi da Everton a Villa Park..
Liverpool za ta fuskanci wasa mai matukar wahala a gasar Champions League da Marseille ranar Laraba, kuma Van Dijk mai shekaru 34 ya ce Liverpool na bukatar inganta wasanninta sosai.
Liverpool na shiga wasan tana matsayi na tara a teburin Champions League, inda ƙungiyoyi takwas ne kai tsaye ke zuwa zagayen gaba.
Marseille na karkashin jagorancin tsohon kocin Brighton, Roberto de Zerbi, kuma Van Dijk ya ce yana sa za su fuskanci kalubale a karawar.