Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/04/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mika'il, Ibrahim Yusuf Mohammed, Aisha Aliyu Ja'afar da Ahmad Bawage

  1. Dalilan da suka sa na koma jam'iyyar APC - Kawu Sumaila

    Bayan jan ƙafa na tsawon lokaci, ɗaya daga cikin ƴan majalisar dattawa na jam'iyyar NNPP Sanata Abdurahman Kawu Sumaila ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.

    Matakin na zuwa ne bayan shafe watanni ana takun saƙa tsakanin Sanatan da jam'iyyarsa ta NNPP a jihar Kano.

    A makon da ya gabata ne Sanata Kawu Sumaila ya jagoranci wata tawagar yanmajalisar tarayya na NNPP inda suka gana da shugaban jam'iyyar APC mai mulki kuma tsohon gwamnan jihar Kano.

    A hirar da ya yi da BBC, Sanatan ya bayyana dalilansa na ficewa daga jam'iyyar NNPP, inda ya tabbatar da cewa ya ɗauki matakin ne domin samar da ci gaba ga al'ummar mazaɓarsa.

    Ya ce ''Wasu daga cikin dalilan da za su sa mu fice shi ne yankin da muka fito. Ya za mu iya samar wa mutanen yankin mu wani abu da zai amfanar da su, kuma ai ita siyasa da ƙunshi tattaunawa domin nema wa al'umma maslaha.''

    Sanatan ya kuma yi watsi da batun cewa ya yi wa jam'iyyar NNPP butulci ganin cewa a ƙaƙashin inuwarta aka zaɓe shi inda ya yi nuni da cewa akasarin ƴan siyasa 109 da suka tsaya zaɓen majalisar dattawa a jam'iyyar ba su kai labari ba.

    ''Ai ba wai NNPP ɗin ba ce, waye ya tsaya a cikin NNPP ɗin,saboda haka ai zaɓa ta da aka yi kowa ya san an zaɓe ni ne saboda ni ne ɗantakaran, kuma a zone ɗin ai da sun tsaya, me ya sa ba su ci ba, sai yanzu? Saboda haka suna yana da tasiri.'' in ji shi

    Sanatan ya ƙara da cewa barinsa jam'iyya ba ta na nufin an ja zare tsakaninsa da gwamnatin NNPP a jihar Kano ba ne, inda ya ce a shirye ya ke ya goyi bayan duk wani shirin da gwamnatin za ta ɓullo da shi wanda zai kawo ci gaba ga al'umma.

  2. Gwamnatin Najeriya za ta sake ƙaddamar da shirin ciyar da ɗalibai

    Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da cewa za ta sake ɗaddamar da shirin ciyar da ɗalibai a makarantu, ranar 29 ga watan Mayu.

    Ƙaramin Ministan ma'aikatar jin-ƙai da rage talauci, Dr Yusuf Sununu ne ya bayyana hakan a ranar Larabar da ta gabata yayin wata ganawa da ƙungiyoyi masu zaman kansu da kuma jami’an gwamnati a Abuja.

    Sununu ya sanar da cewa za a sake kaddamar da shirin ne domin murnar cikar shugaba Bola Tinubu shekara ta biyu akan karagar mulki.

    Ya ce shirin na da nufin magance yunwa da kuma inganta ɓangaren ilimi a faɗin ƙasar baki ɗaya.

    ''Shirin na nufin amfanar yara miliyan 10 kuma zai iya ƙara yawan yaran da ke shiga makarantu da kashi 20 cikin 100 sannan kuma ya bunƙasa hazaƙar yara a ɓangaren karatu da kashi 15 cikin 100 ,” in ji shi.

    Sake ƙaddamar da shirin na zuwa ne a daidai lokacin da ake hasashen cewa sama da ƴan Najeriya miliyan 30 na iya fuskantar matsananciyar yunwa, wanda hakan ke nuni da muhimmancin ɓullo da shirye-shirye makamantan wannan cikin gaggawa.

  3. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Alhamis.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.

    Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya.