Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/08/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/08/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi, Aisha Babangida da Ibrahim Mohammed

  1. Rufewa

    Jama'a a nan muka kawo ƙarshen wannan shafi na labaran kai-tsayr.

    Sai kuma gobe idan Allah ya nuna mana.

    A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.

  2. Prigozhin ya san yana cikin barazana kafin rasuwarsa - Mahaifiyarsa

    Rasha

    Asalin hoton, AFP

    Mahaifiyar wanda ya samar da sojin haya na kungiyar Wagner, Yevgeny Prigozhin, ta shaidawa wata kafar yada labarai dan ta ya san ya na tsaka mai wuya gabannin mutuwarsa.

    Prigozhin ya rasu a hadarin jirgin sama, watanni biyu bayan ya jagoranci macin da aka yi a birnin Moscow, da ake kallon yunkurin juyin mulki.

    Amma mahaifiyarsa mai suna Violetta, Prigozhina, 'yar shekara 85 ta kafe dan ta na kokarin isa inda manyan jami'an sojin kasar su ke, wadanda ya zarga da gazawa da cin hanci da rashawa.

    Kafar intanet ta Fontanka, ta ambato Viollet na cewa har yanzu ta na biyayya ga shugaba Vladimir Putin, duk da wasu na cewa shugaba Putin ne ya bada umarnin kashe dan ta.

  3. Lammy ya buƙaci Isra'ila ta ɗauki mataki kan rage yunwa a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Sakataren harkokin wajen Birtaniya, David Lammy, ya yi Allah-wadai da yunwar da aka kitsa a birnin Gaza.

    Ya yi kira ga Isra'ila ta dakatar da matakan da ta ke dauka da ke kara munana lamarin.

    Sai dai Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya kira rahoton da aka fitar kan yunwa a Gaza da karya tsagwaronta, tare da watsi da zarge-zargen da ake yi wa gwamnatinsa na hana shigar da kayan agaji.

  4. MDD ta ce aƙalla mutum 98 aka kashe kwanaki 10 a Sudan

    Sudan

    Asalin hoton, Mohamed Zakaria/BBC

    MDD ta ce aƙalla mutum 98 aka kashe kwanaki 10 da suka gabata a birnin El-Fasher na Sudan da aka yi wa ƙawanya, da sansanin 'yan gudun hijira da ke yankin.

    Tun watan Mayun shekarar da ta gabata, 'yan tawayen RSF suka yi wa babban birnin na yanmkin Dafur ƙawanya.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ana fama da matsananciyar yunwa a El-Fasher, likitocin Sudan kuma sun yi gargaɗin birnin na gab da zama maƙabarta.

    Ofishin kare haƙƙin ɗan'adam na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce adadin waɗanda yunwa ta yi ajali a baya-bayan nan ya zarta duk yadda ake tunani, sannan ba za a amince da hare-haren da ake kai wa farar hula ba.

    Arewacin yankin Darfur ya kasance daya daga wuraren da yakin basasar shekaru 2 ya daidaita.

  5. Kashe masallata a Malumfashi ba zai tafi a banza ba - Gwamnati

    Tinubu

    Asalin hoton, PRESIDENCY NG

    Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa ba za ta gajiya ba har sai ta farauto maharan da suka kashe masallata a garin Malumfashi da ke jihar Katsina, saboda a cewarta, maharan sun nuna rashin imani a harin.

    Cikin wata sanarwa da ministarn yaɗa labaran ƙasar ya fitar, gwamnatin tarayya za ta tabbatar an maharan tare da gurfanar da su a gaban shari'a.

    "Rashin imani kai hari kan mutanen da babu ruwansu, waɗanda kawai sun taru ne domin gudanar da ibada. Wannan aika-aika ce da ba za mu bari ta tafi a banza ba."

    Ministan ya ce tuni jami'an tsaro suka fara bibiyar maharan, inda ya ƙara da cewa ba za su gajiya ba sai an kama waɗannan suka kai harin.

    "Muna ba ƴan Najeriya tabbacin za a kama tare da hukunta maharan cikin gaggawa, kuma ba za mu bari hakan ya ci gaba a faruwa ba, wannan ɗanyen aiki ga Najeriya, ba mutanen Malumfashi kaɗai ba ko jihar Katsina."

    Ya ce Shugaba Tinubu na miƙa ta'aziyarsa ga iyalan waɗanda aka kashe, da mutanen Malumfashi da jihar Katsina da ma ƙasar baki ɗaya da ma iyalan waɗanda aka kashe.

    Ya ce daga cikin ƙoƙarin da gwamnati ke yi na kawo ƙarshen lamarin akwai kama fitattun ƴan ƙungiyar Ansaru da ake zargi da fasa gidan yarin Kuje da sauran nasarori.

  6. Kungiyoyin fararen hula sun ƙalubalanci gwamnatin Eswatini kan ƙarbar mutum biyar da Amurka ta koro

    Ƙungiyoyin farar hula a Eswatini sun shigar da ƙara a kotu kan yarda da gwamnatin ƙasar ta yi na karɓar wasu mutum biyar da Amurka ta koro a watan Yuli.

    Amurka ta bayyana wadannan mutane a matsayin “‘yan bakin haure masu laifi,” waɗanda suka fito daga Vietnam da Jamaica da Laos da Cuba da kuma Yemen.

    An ce sun aikata laifuka iri-iri daga fyade har zuwa kisa, in ji Mataimakiyar sakataren tsaron cikin Gida na Amurka, Tricia McLaughlin.

    Gwamnatin Eswatini ta bayyana cewa tana sane da damuwar jama’a kan karɓar waɗannan mutane.

    Ƙungiyoyin fararen hula sun ce wannan mataki na iya zama mummunan abin koyi, kuma ƙasar ba ta kamata ta zama wurin ajiye masu laifi ba.

  7. FBI ta kai samame gidan tsohon hadimin Trump

    Wasu jami'an FBI, sun juya baya

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'an hukumar bincike ta Amurka, FBI sun kai samame ofishi da gidan tsohon bai mai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin tsaro John Bolton.

    Mista Trump ya ce ba a sanar da shi game da samamen ba - wani ɓangare binciken tsaron ƙasar - amma ya ce ba ya goyon bayan tsohon hadimin nasa.

    John Bolton ya yi aiki da mista Trump a wa'adin mulkinsa na farko, amma daga baya ya kasance ɗaya daga cikin manyan masu sukarsa, yana mai cewa bai cancanci shugabancin Amurka ba.

    A wata hira da aka yi da shi a baya-bayan nan, Mista Bolton ya bayyana shugabancin Trump a matsayin wata ladabtarwa ga Amurkawa.

    Ya kuma zargi shugaban na Amurka da kitsa masa bi-ta-da-ƙulli, ta hanyar janye masa kariyar da aka ba shi.

  8. Za a ci gaba da tattauna shirin nukiliyar Iran a mako mai zuwa

    Nukiliyar Iran

    Asalin hoton, EPA

    Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta ce a mako mai zuwa za a ci gaba da tattauna shirin nukiliyarta tsakanin ƙasashen Birtaniya da Faransa da Jamus, yayin da ƙasashen uku ke duba yiwuwar saƙe ƙaƙaba wa ƙasar takunkumi.

    Manyan ƙasashen Turai da ƙungiyar EU, sun yi gargaɗin cewa lokaci na ƙure wa Iran ta amincewa da ''gamsasshen maganin'' matsalarsu kan inganta sinadaran uranium ɗinta.

    Iran ta jima tana nanata cewa shirin nukiliyarta na zaman lafiya ne, duk kuwa da ci gaba da inganta sinadaran uranium da ya kusan adadin da ake buƙata na ƙera makamin.

    Duniya ta ƙara nuna damuwa bayan da Iran ta yanke hulɗa da hukumar kula da Nukiliya da Majalisar Dinkin Duniya, bayan hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai mata a watan Yuni.

    A ƙarshen watan Yuni ne Iran da wasu ƙasashen Turai suka cimma matsayar ci gaba da tattaunawar a birnin Geneva.

  9. Rundunar sojin Najeriya ta ce kiran kare kai ba ya nufin mallakar makami

    Sojojin Najeriya

    Asalin hoton, Defence HQ/X

    Shalkwatar tsaron Najeriya ta yi ƙarin haske kan kalaman da babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya yi kan batun kare kai daga hare-haren ƴan fashin daji.

    Cikin wata sanarwa da shalkwatar tsaron ta fitar ta ce kalaman Janar Musa ba suna ƙarfafa wa mutane mallakar makami ba ne, kamar yadda wasu kafofin labarai a ƙasar ke yaɗawa.

    ''Abin da yake nufi shi ne ƴan ƙasa su koyi dabarun kare kai da duniya ta amince da su kamar ƙwarewar tuƙi, da judo da ninƙaya da dambe ko kokawa da sauransu'', in ji sanarwar.

    ''Kalamansa ba sa nufin mallakar makami ta haramtacciyar hanya, saboda yana sane da dokokin Najeriya da suka haramta mallakar makami''.

    A ranar Alhamis ne cikin wata hira da gidan Talbijin an Channels, Janar Musa ya ce ya kamata kowane ɗan Najeriya ya koyi dabarun kare kai domin kauce wa hare-haren ƴanbindiga.

    Kalaman babban hafsan dai sun janyo ce-ce-ku-ce tsakanin ƴan ƙasar inda wasu ke ganin hakan na nuna gazawa a ɓangaren gwamnati na magance matsalar rashin tsaron da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.

  10. Hotuna daga jana'izar tsohon mai tsaron ragar Super Eagles

    ...
    ...
    ...
    ...
    ...
    ...
  11. Sojojin Sudan da RSF sun yi iƙirarin samun nasara a rikicin kusa da El-Obeid

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Sudan da dakarun RSF sun yi iƙirarin samun nasarori daban-daban da jawo mummunar asarar rayuka ga juna, bayan faɗace-faɗace masu tsanani da suka auku kusa da birnin El-Obeid – babban birnin jihar Kordofan ta Arewa.

    RSF ta yi iƙirarin cewa ta yi nasarar korar sojin gwamnati da abokan hulɗarsu daga sassan jihar Kordofan ta Yamma da ta Arewa a kwanakin baya.

    Yaƙin Sudan a ‘yan watannin nan ya fi mayar da hankali a yankin Kordofan mai faɗi, wanda ke haɗa babban birnin ƙasar, Khartoum, da yankin Darfur da RSF ke riƙe da shi.

  12. Gwamnonin PDP na taro a Zamfara

    ...

    Asalin hoton, Zamfara state government

    Gwamnonin jam'iyyar PDP a Najeriya na gudanar da wani taro a jihar Zamfara domin tattaunawa kan yunƙurinsu na "ɗaukar matakai masu muhimmanci".

    Taron zai fara ne daga yau Juma'a bayan hallarar gwamnonin, inda ake sa ran tattaunawa kan muhimman batutuwa a gobe Asabar.

    A cikin sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa, taron na nufin tattauna muhimman batutuwan siyasa da gwamnonin ke fuskanta a halin yanzu.

    PDP, wadda ita ce babbar jam'iyyar adawa a Najeriya na fuskantar ƙalubale na rikicin cikin gida da kuma ficewar wasu daga cikin manyan ƴaƴanta, ko dai zuwa jam'iyyar APC mai mulki ko kuma wadanda ke alaƙanta kansu da haɗakar ƴan adawa waɗanda suka tare a jam'iyyar ADC.

    Hakan na faruwa ne gabanin babban zaɓen ƙasar na 2027. inda ƴan siyasa a kasar ke ci gaba da shiri, duk kuwa da gargadin da hukumar zaɓen ƙasar mai zaman kanta ta ƙasar ta yi kan fara harkokin siyasa gabanin lokaci.

    A cikin sanarwar da gwamnan ya fitar ya ce "taron zai mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi haɗin kan jam’iyyar da kuma shirin bunƙasa ci gaban jihohi, musamman a lokacin da jam’iyyar ke shirin gudanar da babban taronta na kasa a garin Ibadan, a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba, 2025."

  13. Ma’aikatar kasuwancin Nijar ta dakatar da ayyukan wasu gidajen burodi 13

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    A jamhuriyar Nijar, ma'aikatar ministan kasuwancin ƙasar ta dakatar da ayyukan wasu gidajen buga burodi guda 13 a birnin Yamai.

    A wata sanarwa da ma'aikatar kasuwanci ta kasar ta fitar ta ce ta dauki matakin ne mai wa'adin kwanaki 15 bayan da gidajen burodin suka ƙi mutunta wasu sharuɗɗan aiki da ta gindaya masu na tsafta da kuma ka'idojin sarrafa burodin.

    Mai bai wa ma'aikatar kasuwanci shawara, Yunusa Jumrau ya ce bayan sun rubutawa gidajen burodin 13 ƙorafi tare da basu wa'adi, sun lura cewa babu wani yunƙurin da gidajen burodin sukayi na ƙoƙarin gyara ƙorafe-ƙorafen.

    "Wannan dalilin ne ya saka muka dakatar da ayyukansu nan da kwana 15, saboda haka idan wani giidan burodi yayi ƙoƙarin gyara kurakure kuma muka bincika mu ka ga gyaran, za mu bar shi ya ci gaba da aiki." in ji Jumrau.

    Ya ƙara da cewa, "Haka kuma, idan muka bincika mu ka ga babu wani gidan burodi da ya gyara kurakuren, toh gidan burdin zai kasance a rufe har abada."

    Hakazalika, ƙungiyar da ke yaƙi da tsadar rayuwa da kare masu saye ta yabawa wannan matakin inda ta ce abu ne me kyau domin kawo gyara kan yadda ake sarrafa burodi.

    Sai dai a nasu ɓangaren masu gidajen burodin na ganin dokokin da gwamnatin ta gindaya masu sun yi tsauri sossai.

  14. An kashe jagoran Boko Haram a Nijar

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Jamhuriyar Nijar sun sanar da kisan wani jagoran Boko Haram mai suna Bakura, a yankin Tafkin Chadi, inda ƙasar ke iyaka da Najeriya da Chadi da Kamaru.

    A wata sanarwa da sojojin suka fitar a ranar Alhamis, an kashe Bakura ne yayin wani aikin soji a wani tsibiri a yankin Diffa da ke kudu maso gabashin Nijar a makon da ya gabata.

    Bakura dai ya jagoranci wani ɓangare na ƙungiyar Boko Haram wadda ke biyayya ga tsohon shugaban ƙungiyar, Abubakar Shekau, inda ya ƙi shiga reshen abokan hamayyar su na ISWAP inda ya koma tsibirin da ke gefen Nijar na tafkin tare da mayaƙansa.

    Rikicin Boko Haram ya fara ne tun 2009 a arewa maso gabashin Najeriya, inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 40,000 sannan ya tilasta wa sama da miliyan biyu tserewa daga gidajensu.

    Rikicin ya kuma bazu zuwa ƙasashen makwabta, inda Nijar ta fuskanci hare-hare na farko daga kungiyar a Bosso a 2015.

    Sojin Nijar sun ce an kai harin ne da jirgin yaki a safiyar 15 ga Agusta, inda suka bayyana cewa sun harbi Bakura sau uku a matsayinsa na shugaba a Shilawa.

    Sunan asali na Bakura shi ne Ibrahim Mahamadu, mai kimanin shekara 40 a duniya kuma ɗan asalin Najeriya ne.

    Ya shiga Boko Haram sama da shekaru 13 da suka gabata, sannan ya karɓi shugabancin kungiyar bayan mutuwar Shekau a watan Mayu 2021.

  15. Majalisar dokokin California ta amince da sabon tsarin taswirar zaɓe

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan majalisar dokokin Jihar California da ke Amurka wadda 'yan jam'iyyar Democrats ke da rinjaye sun amince da jerin wasu ƙudurori da za su sake fasalin taswirar zaɓen jihar.

    Wannan zai taimakawa wajen bai wa jam'iyyarsu ta Democrats samun ƙarin wasu kujeru biyar a majalisar wakilan ƙasar.

    Matakin martani ne ga abin da ya faru a jihar Texas, to amma ba kamar Texas din ba, a California dole ne sai mutanen jihar sun kaɗa ƙuri'ar amincewa da ƙudurorin.

    Za a gudanar da kuri'ar amincewar ne a watan Nuwamba mai zuwa.

    Dukkan jam'iyyun biyu wato Democrats da Republican na ƙoƙarin ganin sun samu rinjayen majalisar wakilan ƙasar a zaben tsakiyar zangon da za ayi a shekara mai zuwa.

  16. Harin bam a Cali na Colombia ya kashe mutum 6 tare da jikkata 36

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani harin bam da mota ya yi sanadiyyar kashe mutane akalla 6 a wajen wani sansanin sojin sama da ke birnin Cali na Colombia.

    Mahukunta sun ce wasu mutum 36 kuma sun jikkata.

    Ganau sun ce fararen hula na daga cikin wadanda suka rasa ransu. Kafar yada labaran kasar ta dora alhakin harin akan wata kungiyar 'yan tawayen kasar da ke adawa da gwamnati.

    Ana zargin ƙungiya EMC da kai hari da jirgi marassa matuki kan wani jirgi mai saukar ungulu na 'yan sanda a jiya Alhamis lamarin da ya yi sanadin mutuwar 'yan sanda 12.

  17. Isra’ila ta ce za ta lalata birnin Gaza idan Hamas ta ƙi amincewa da sharuɗɗanta

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya bayyana cewa za a lalata birnin Gaza gaba ɗaya idan kungiyar Hamas ta ƙi miƙa makamai da kuma sakin dukkan fursunonin da take riƙe da su.

    Wannan furuci nasa ya zo ne bayan majalisar ministocin Isra’ila ta amince da sabon shirin kai farmaki a birnin Gaza duk da suka da adawa daga ƙasashen duniya da ma cikin gida.

    A cikin sanarwar da ya fitar a shafinsa na X, Katz ya ce: “Idan har Hamas ba ta amince da sharuɗɗan Isra’ila na kawo ƙarshen yaƙi a Gaza ba, musamman sakin dukkan fursunoni Isra'ila da kuma miƙa makamai ba, toh babban birnin Gaza zai zama kamar birnin Rafah da Beit Hanoun,” in ji shi.

    Wadannan garuruwa biyu da ya ambato dai sun ruguje sakamakon hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai a baya.

  18. APC ta lashe zaɓen cike gurbin ɗan majalisar Zamfara

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Jam'iyyar APC ce ta lashe zaɓen cike gurbin ɗan majalisar dokokin jihar Zamfara mai wakiltar Ƙaura Namoda ta Kudu a zaɓen da aka kammala a jiya Alhamis.

    Jami'in hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya da ya bayyana sakamakon zaɓen, Farfesa Lawal Sa'ad, ya ayyana Kamilu Sa'idu, na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen, bayan ya cika dukkan sharuɗɗa tare da samun ƙuri’a mafi rinjaye.

    Sakamakon ya nuna cewa Kamilu ya samu ƙuri'a 8,182 yayin da abokin karawar sa Muhammad B. Lawal Kurya, na jam'iyyar PDP mai mulkin jihar, ya samu ƙuri’u 5,544.

    A makon da ya gabata ne hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya Inec ta gudanar da zaɓukan cike gurbi a jihohi da dama na faɗin ƙasar, inda jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta lashe zaɓe a mazaɓu 12, APGA ta lashe kujeru biyu, PDP ta lashe kujera ɗaya, ita ma NNPP ta lashe ɗaya.

    Sai dai an bayyana zaɓen majalisar dokokin jihar Zamfara a mazaɓar Ƙauran Namoda ta kudu a matsayin wanda bai kammala ba sanadiyyar hargitsin da ya yi sanadin soke sakamako rumfunan zaɓe biyar.

    Lamarin ya sanya an sake gudanar da zaɓen a jiya Alhamis, inda jam'iyyar APCn ta lashe.

    Zamfara na daga cikin jihohin Najeriya da jam'iyyar hamayya ta kayar da gwamna mai ci a zaɓen 2023, inda Dauda Lawal na jam'iyyar PDP ya kayar da tsohon gwamnan jihar Bello Matawalle na APC, lamarin da ya zafafa adawar siyasa tsakanin manyan jam'iyyun biyu a jihar.

    Daga baya shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa tsohon gwamnan jihar muƙamin minista a ma'aikatar tsaro ta ƙasar.

  19. Netanyahu ya amince da tattaunawa kan sakin fursunonin Isra'ila da kawo ƙarshen yaƙin Gaza

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya ce ya bayar da umarnin a fara tattaunawa domin sakin raguwar Isra'ilawan da Hamas ke tsare da su da kuma kawo karshen yakin da ake a Gaza.

    Kazalika ya kuma amince da shirin ƙwace birnin Gaza da ke shan suka inda ake ƙaddamar da manyan farmaki lamarin da ya tursasawa dubban Falasdinawa tserewa suna komawa kudanci.

    Mazauna birnin sun shafe kwanaki suna fama da lugudan wuta daga Isra'ila.

    Netanyahu yayi watsi da wata kwarya kwaryar yarjejeniyar ta Hamas ta amince da ita da za ta bayar da damar sakin mutanen da ake tsare da su.

  20. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a hantsin Juma'a

    Shafin na yau zai fi mayar da hankali ne kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta, da kuma sauran sassa na duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo.

    Ku kasance da mu.