Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye - Laraba, 19 ga watan Fabarairun 2025

Taƙaitattu

  • Trump ya soki Zelensky, ya kira shi mai mulkin kama karya
  • An yi asarar rayuka 10 da dukiya biliyan 11 lokacin zanga-zanga a Kano
  • Ɓarakar da ke tsakanin Shugaba Trump da Zelensky ta bayyana
  • An samu ƙaruwar kai wa Musulmi hari a Birtaniya
  • Na ji takaicin kalaman da kocina ya yi a kaina - Lookman
  • Hukumomi a Philippines na biyan mutane kuɗi domin kama sauro
  • Ma'aikatan ofisoshin jakadancin Najeriya na kokawa kan rashin biyan su albashin watanni
  • Tsohon shugaban Brazil Bolsonaro na fuskantar tuhuma kan juyin mulki
  • 'Yanbindiga sun kashe fasinja bakwai a Pakistan
  • Trump ya ce ya samu ƙwarin guiwa kan ƙare yaƙin Ukraine

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Annur Muhammad da Ahmad Bawage

  1. Trump ya ce ya samu ƙwarin guiwa kan ƙare yaƙin Ukraine

    Shugaba Trump ya ce bayan soma tattaunawa da Rasha, ya samu ƙwarin guiwa kan samar da zaman lafiya a Ukraine.

    Tattauanwar ita ce ta farko tsakanin Amurka da Rasha tun bayan mamayar da Rashar ta yi wa Ukraine.

    A wajen wani taron manema labarai a Ma-ra-La-go shugaba Trump ya ce, za a cimma yarjejeniyar zaman lafiya cikin sauƙi, sai dai ya ce ya ji takaicin yadda Ukraine ta yi ƙorafin ba a sanya ta cikin tattaunawar ta Saudiya ba.

    Wakiliyar BBC ta ce shugaba Trump ya dora wa Ukraine laifi na fara takalar yaƙin, inda ya ce da shi ne shugaban ƙasa a lokacin hakan ba za ta faru ba.

  2. Buɗewa

    Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, muna muku maraba a wannan safiya ta Laraba, 19 ga watan Fabarairun 2025.

    Ni Muhammad Annur Muhammad da sauran abokan aiki za mu kasance da ku daga yanzu zuwa wani lokaci a nan gaba.

    Za kuma ku iya leƙawa shafukanmu da sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo har ma ku yi muhawara

    Ku kasance tare da mu.

    Mu fara da wannan karin maganar da ke cewa - Komai daɗewar farin kare ba zai zama rago ba