Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 07/07/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku abaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Abdullahi Bello Diginza

  1. Adadin mutanen da suka mutu a ambaliyar Texas ya haura 80

    Hukumomi a jihar Texas da ke Amurka sun tabbatar da mutuwar fiye da mutum 80 sakamakon ambaliyar da ta auka wa jihar tun a ranar Juma'a.

    Mutum 68 daga cikin waɗanda suka mutu ciki har da ƙananan yara 28, a gundumar Kerr suke.

    Har yanzu akwai ƴanmata 10 da mai kula da wurin shaƙatawar Mystic da ba a ji ɗuriyarsa ba.

    Alƙaluman waɗanda suka mutu na sauyawa cikin hanzari, yayin da masu aikin ceto ke ci gaba da lalubo gawarwaki.

    Shugaba Trump ya ce ya tsara zuwa yankin da lamarin ya faru cikin wannan mako

  2. Za a ci gaba da tattaunawar tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra'ila

    A yau ne za a ci gaba da tattaunawa tsakanin Hamas da Isra'ila kan yiwuwar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da kuma sakin Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su.

    Wani jami'i a Falasdinu ya ce ba a cimma wata matsaya ba a tattaunawar ranar Lahadi da aka shafe fiye da sa'a uku ana yi.

    A yau ne Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu zai gana da Shugaba Trump na Amurka.

    Mista Trump ya ce yana fatan za a cimma yuarjejeniya a wannan makon.

  3. Trump ya caccaki Musk kan yunƙurin kafa sabuwar jam'iyya a Amurka

    Shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki tsohon mashawarcinsa, Elon Musk, kwana guda bayan hamshaƙin attajirin ya sanar da cewa zai kafa sabuwar jam'iyyar siyasa a Amurka.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, Mista Trump ya ce Elon Musk ya bauɗe hanya.

    ''An gina tsarin siyasar Amurka kan aƙidar tsarin jam'iyya biyu'', in ji Shugaba Trump, yana mai cewa ƙarin jam'iyya zai haifar da ruɗani a siyasar Amurka.

    Shi dai Elon Musk ya ce jam'iyyar America Party da yake yunƙurin kafawa za ta ƙwato wa masu zaɓe ƴancinsu.

  4. Asslam alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye, barkanmu da safiyar wannan rana ta Litinin.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku, bisa kulawar Usman Minjibir, domin kawo muku halin da duniyar ke ciki.

    Ku kasance da mu shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.