Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya 13/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Juma'a 13 ga watan Maris 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. Amurka ta ce ta kai hari kan kusan wurare dubu 6 a cikin Iran

    Amurka ta ce ta kai hare-hare kan kusan wurare dubu shida a cikin Iran tun bayan fara yaƙi da ƙasar.

    Ta ce hare-haren sun haɗa da kai farmaki kan gomman jiragen ruwa, wuraren kera makamai, da kuma kan garkuwar kare hare-haren sama.

    A halin da ake ciki kuma, Isra’ila ta ce tana kai wasu sababbin jerin hare-hare ta sama kan babban birnin Iran ɗin, Tehran.

    A daren da ya gabata ma, Isra’ilar ta ce ta kai wani hari a wani wuri da ke da alaƙa da kera makaman nukiliya.

    Sai dai Iran ta dage cewa shirinta na nukiliya ba na kera makamai ba ne, yana da nufin ayyukan ci gaban ƙasa na zaman lafiya.

    An kai waɗannan hare-haren na baya-bayan nan ne yayin da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ke cewa ƙasarsa na yi wa rundunar sojin juyin juya hali ta Iran gagarumar illa.

  2. Isra'ilawa da dama sun jikkata sakamakon harin Iran

    Isra'ilawa da dama ne suka jikkata bayan wani harin makami mai linzami da Iran ta harba a Isra'ila wanda ya faɗa wani ƙauye da ke arewacin ƙasar a safiyar Juma’a, kamar yadda hukumomin agajin gaggawa suka bayyana.

    A cewar hukumar motocin daukar marasa lafiya ta Magen David Adom, jami’an jinya sun yi wa Isra'ilawa 58 da suka jikkata magani sannan suka kai su asibitocin yankin bayan harin da ya auku a garin Zarzir kusa da Nazareth.

    Rahotannin kafofin watsa labaran Isra’ila sun ce wata mata ta samu rauni sakamakon gutsattsarin ƙarfen roka, kuma halin da take ciki bai da tabbas.

    Sojojin Isra’ila sun bayyana cewa sun tura wata tawagar sojoji zuwa wurin da lamarin ya faru.

    A cikin wata sanarwa, rundunar sojin ta ce jami’anta tare da hukumomin agaji da na ceto suna duba halin da ake ciki a wurin.

    A jiya ne ma’aikatar lafiyar Isra'ila ta ce adadin mutanen da suka jikkata sakamakon hare-haren makamai masu linzami da Iran ke kai wa ƙasar ya kai 2,745.

  3. Iyalin Ali Khamenei: Su wa aka kashe, su wane ne ke raye?

    Labarin kisan da aka yi wa wasu daga cikin iyalan tsohon jagoran addinin Iran, Ali Khamenei ya haifar da tambaya game da waɗanda suka rage a dangin.

    Surukai maza da mata nawa jagoran addinin ke da su, kuma waɗanne ne danginsa na kusa-kusa?

    A tsawon lokacin mulkinsa, Ali Khamenei ya naɗa da yawa cikin iyalansa manyan muƙaman siyasa ko wasu ma'aikatun gwamnati.

    Kuma da dama cikin dangin nasa daga baya sun koma masu adawa da shi, inda aka ɗaure wasunsu a gidajen yari ko suka tafi gudun hijira ƙasashen ƙetare.

    Wannan muƙala ta tattaro wasu bayanan da ake da su game da iyalan tsohon jagoran addinin.

  4. Jirgin sojin Amurka ya yi hatsari a Iraƙi

    Wani jirgin sojin Amurka ya yi hatsari a Iraƙi, kamar yadda rundunar sojin Amurka ta tabbatar.

    Jirgin sojin na KC-135 ya faɗo ne bayan wani "hatsarin" da ya shafi wasu jirage biyu.

    Rundunar sojin Amurka ta ce "ana ci gaba da aikin ceto" a yammacin Iraƙi - abin da sojoji suka ce ya faru ne a "yankin da ba na maƙiya ba."

    "Lamarin ba ya faru ba ne a yankin da ake yaƙi ko kuma musayar wuta," in ji sanarwar.

    Jirgi na biyu da lamarin ya shafa ya sauka lafiya, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

  5. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a.

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

    Aisha Babangida ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.