Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Jana'izar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shafin bayani kai-tsaye kan binne gawar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Talata 15 ga watan Yulin 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Aisha Aliyu Jaafar, Isiyaku Muhammed, Umaymah Sani Abdulmumin da Usman Minjibir

  1. Yadda ake jiran isar gawar Muhammadu Buhari a garin Daura

    Dandazon al'umma na zaman jiran isar gawar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a garin Daura na jihar Katsina, inda za a binne shi

  2. Gawar Buhari tana kan hanyar Daura tare da rakiyar Tinubu

    Gawar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na kan hanya zuwa Daura inda za a gudanar da sallar jana'iza da kuma binne ta.

    Bayanai da muka samu na bayyana cewa za a yi wa gawar sallah ne a fadar Sarkin Daura, sannan a binne ta a gidan sa da ke GRA Daura.

    An ɗauki gawar ne bayan an mata faretin ban girmamawa, inda manyan hafsoshin tsaron ƙasar suka ɗauk gawar daga jirgi, sannan suka raka ta zuwa jirgin da zai ɗauki gawar zuwa Daura inda za a binne ta.

  3. Yadda aka saka gawar Muhammadu Buhari a motar ɗaukar gawa domin tafiya Daura

  4. Kalli yadda aka fito da gawar Muhammadu Buhari daga cikin jirgi a Katsina

  5. An yi wa gawar Muhammadu Buhari faretin ban-girma a Katsina

    Sojojin Najeriya bisa jagorancin shugaban ƙasar Bola Tinubu sun gudanar da faretin ban-girma ga tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari.

    An gudanar da faretin ne a filin jirgi na Umaru Yar'adu da ke birnin Katsina, jim kaɗan bayan isar gawar daga birnin Landan.

    Muhammadu Buhari ya rasu ne a ƙasar Birtaniya yana da shekara 82 a duniya bayan doguwar jinya.

  6. Shugaba Tinubu ya tarbi gawar Muhammadu Buhari a Katsina

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tarbi gawar tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari bayan isowar sa daga birnin Landan.

    Tinubu ya tarbi gawar ne a filin jirgin na Umaru Musa Yar'aduwa da ke Katsina inda za a tafi da ita zuwa Daura domin yin sallah da kuma binnewa.

    A ranar Lahadi, 13 ga watan Yuli ne tsohon shugaban ƙasar ya rasu a birnin Landan na Birtaniya bayan doguwar jinya.

  7. Gawar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta isa Katsina

    Gawar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta isa filin jirgin sama na Umaru Musa YarAdua da ke Katsina tare da rakiyar mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima.

    Marigayi shugaba Muhammadu Buhari ya rasu ne a ranar 13 ga watan Yulin 2025 a wani asibiti da ke Landan bayan rashin lafiya, kuma ya rasu ne yana da shekara 82.

    Za a wuce da gawar zuwa Daura, garin marigayin domin yi masa jana'iza a gidansa.

  8. Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya isa Katsina don jana'izar Buhari

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya isa Jihar Katsina domin halartar jana'izar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

    Shugaba Tinubu ne kuma zai tarbi gawar marigayin a Katsina idan ta isa daga Landan.

    Tun a safiyar yau ne gawar ta baro Landan tare da rakiyar mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima da wasu jam'ian gwamnati da wasu iyalai da makusantan sa.

    Shugaban ƙasar ya kuma kafa wani kwamitin jam'ian gwamnati ƙarƙashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayya George Akume wanda tuni kwamitin ya isa Katsina.

    Hakazalika ita ma uwargidan shugaban ƙasar Oluremi Tinubu ta isa jihar domin yin ta'aziyya.

  9. Tsohon shugaban Nijar Mahamadou Issoufou ya isa Katsina

    Tsohon shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou ya isa birnin Katsina domin halartar jana'aizar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

    Issoufou ya samu tarba daga gwamnan jihar Katsina Dikko Radda da na Sokoto Ahmed Aliyu da wasu jami'ai na gwamnatin Najeriya.

    Gabanin zuwan Mahamadou Issoufou, tawagar gwamnatin Jamhuriyar Nijar ƙarƙashin jagorancin Firaimistan Lamine Zein da malaman addini sun isa ƙasar bisa umarnin shugaba Abdorahamane Tiani.

  10. An girke bindigogi da jami'an tsaro a Daura gabanin isar gawar Shugaba Buhari

    An tsaurara matakan tsaro a harabar gidan marigayi shugaba Muhammadu Buhari tare da girke manyan bindigogi don yin harbin ban girma ga gawar mamacin.

    Ana sa ran gawar za ta isa Katsina da ranar yau bayan ta bar Landan tun da safiya.

  11. Mutum huɗu sun mutu sanadiyyar ruftawar gini a Kano

    An zaƙulo gawarwakin mutum huɗu daga ɓaraguzan wani gini mai hawa uku da ya rufta a ranar Lahadi a birnin Kano.

    Gidan wanda ba a kammala ginawa ba ya rushe ne a layin Abedi da ke unguwar Sabo Gari sakamakon mamakon ruwan sama.

    Gidan talabijin na gwamnatin Najeriya (NTA) ya ruwaito cewa mutane bakwai sun samu raunuka kuma a yanzu haka suna karɓar kulawa a asibitin da ke birnin.

    Jami'an hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar da ta ƙasa (NEMA) na ci ƙara ƙaimi wajen aikin ceto domin gano wasu gawarwaki da ake zargin suna maƙale a cikin ɓaraguzai.

    Shaidu sun bayyana cewa waɗanda abin ya rutsa da su sun nemi mafaka ne a gidan saboda ruwan sama wanda aka soma a yammacin Lahadin.

    Zuwa yanzu dai hukumomi ba su tabbatar da dalilin da ya sa ginin ya rushe ba.

  12. Tawagar Jamhuriyar Nijar ta isa Katsina domin jana'izar Muhammadu Buhari

    Wata tawaga da gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta tura ta isa jihar Katsina da ke Najeriya domin halartar jana'izar marigayi tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da za a yi a yau Talata.

    Tawagar ta isa jihar ne bisa jagorancin Firaministan ƙasar Ali Lamine Zeine, tare da wasu ministoci da malaman addini da kuma manyan Jami'an gwamnati.

    Tawagar ta samu tarbar gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda, da ministan kasafin kudi na Najeriya Atiku Bagudu da kuma ministan yaɗa labarai Muhammad Idris a filin jirgi.

  13. Uwargidan shugaban Najeriya Remi Tinubu ta tafi Daura domin yin ta'aziyya

    Uwargidan shugaban Najeriya Oluremi Tinubu ta tafi Daura da ke jihar Katsina domin yi wa iyalan marigayi tsohon shugaba Muhammadu Buhari ta'aziyya.

    Oluremi ta tafi ne tare da matan wasu daga cikin manyan ƴan siyasar ƙasar da suka haɗa da matar kakakin majalisar wakilai Fatimah Abbas, da matar mataimakin shugaban majalisar dattawa Laila Barau, sai matar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaron Zarah Rubado da kuma matar Sanata Abu Ibrahim.

  14. Tawagar gwamnatin Najeriya ta isa Katsina domin jana'izar Buhari

    Kwamitin da shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya kafa domin tsara jana'izar tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ta isa Katsina a yau Talata gabanin isar gawar marigayin.

    Ministan yaɗa labarai na Najeriya, Muhammad Idris ya wallafa a shafinsa na X lokacin da jirgin da ke ɗauke da tawagar ta sauka a birnin Katsina.

    Tinubu ya kafa kwamitin ne ƙarƙashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayya George Akume.

    Sauran waɗanda ke cikin kwamitin sun haɗa da ministan tsaro na Najeriya Muhammad Badaru Abubakar da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro Nuhu Ribadu da wasu da dama.

    Jerin sunayen jami'an gwamnati da ke cikin kwamitin jana'izar Muhammadu Buhari.

    • Ministan kudi
    • Ministan kasafi da tsare-tsare
    • Ministan Tsaro
    • Ministan yaɗa labarai
    • Ministan ayyuka
    • Ministan cikin gida
    • Ministan Abuja
    • Ministan Gidaje da raya birane
    • Ministan kiwon lafiya
    • Ministar al'adu
    • Bai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha'anin tsaro
    • Bai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsare-tsare
    • Babban mai taimaka wa shugaba kan harkokin siyasa
    • Babban sifeton ƴansanda
    • daraktan hukumar tsaro ta farin kaya
    • Babban hafsan tsaron ƙasar.

    Gawamnan jihar Katsina, Dikko Radda ya tabbatar wa BBC cewa mambobin kwamitin ne za su wakilci Tinubu a lokacin zaman makokin da za a yi a Daura.

  15. Abin da ya kamata ku sani kan rayuwar Muhammadu Buhari

    A ranar Talata, 15 ga watan Yuli ne ake jana'izar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda ya rasu a birnin Landan ranar 13 ga watan na Yuli bayan fama da jinya.

  16. Halin da ake ciki a Daura gabanin isar gawar Muhammadu Buhari

    A yanzu haka dai alumma na ta tururuwa domin zuwa ta'aziyya da kuma jana'izar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda ya rasu a ranar Lahadi 15 ga watan Yulin 2025 a birnin Landan.

    Mutane da dama sun isa jihar tun a jiya Litinin, inda wasu ke Katsina domin tarbar gawar sa, yayin da wasu kuma suka wuce kai tsaye zuwa Daura inda za a yi janaizar marigayin.

    Mutanen sun haɗa da wasu sannanu a ƙasar ciki har da manyan ƴan siyasa kamar tsohon gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, tsohon shugaban ma'aikata a fadar gwamnatin shugaba Buhari Farfesa Gambari da Arc Ahmed Musa Dangiwa, sai tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El Rufai, da Sunday Dare, da mai magana da yawun Buhari Garba Shehu, sai Malam Isa Ali Pantami da kuma dai dai kun ƴan Najeriya.

    A yanzu haka gidan marigayin da kuma jihar na cike da jam'ian tsaro inda ƴan sanda da jami'an tsaron farin kaya suka jibge ɗaruruwan jam'iansu.

    Rahotanni na cewa bayan an kawo mamacin, za a soma kai shi gidan sa da ke Daura domin yan uwa su yi masa adduoi, daga nan a kai shi fadar mai martaba sarkin Daura Alhaji Faruk Umar Faruk domin yi masa Sallah, daga bisani kuma a sake mayar da gawar gidansa domin birne sa.

  17. Shugabannin ƙasashen Afirka za su halarci jana'izar Buhari

    Ana sa ran wasu daga cikin shugabannin ƙasashen Afirka za su halarci jana'izar marigayi tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da za a yi yau Talata a mahaifarsa Daura.

    Shugabannin ƙasashen sun haɗa da na Gambia Adama Barrow da na Chadi Mahamat Déby da na Guinea Bissau Umaro Sissoco Embaló.

    Tsohon shugaban ƙasar Ghana ma Nana Akufo Addo ya yi wa iyalan marigayin ta'aziyya a Landan tun a jiya Litinin kafin gawar ta bar Landan.

  18. Gawar marigayi shugaba Buhari ta bar Landan zuwa Najeriya

    A safiyar yau Talata ne gawar marigayi tsohon shugaban Najeriya ta baro birnin Landan da ke Birtaniya inda ya rasu, zuwa Daura da ke jihar Katsina domin yi masa jana'iza ta ban girma.

    Marigayi shugaba Muhammadu Buhari ya rasu ne a ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin 2025 bayan jinya na wani lokaci a wani asibiti da ke Landan.

    Bayanai da muka samu daga Landa sun bayyana cewa gawar ta bar Landan ne da misalin karfe 8 na safiya a cikin jirgin sojin saman Najeriya Airforce, kuma ana sa ran za ta isa bayan sallan Azuhar.

    Hakazalika ana sa ran za a gudanar da jana'izar da zarar ta isa kafin binne sa a gidansa da ke Daura.

    Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima, da shugaban mai'aikatan fadar gwamnati Femi Gbajabiamila da ma wasu manyan jami'an gwamnati ne suka rako gawar.

  19. Buɗewa

    Masu bibiyarmu, barkanmu da kasancewa a shafin BBC Hausa na kai-tsaye a safiyar yau Talata.

    Za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya musamman abin da ya shafi jana'izar marigayi Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, da kuma labaran wasu makwaftan Najeriya da ma sauran sassan duniya.

    Dafatan za ku kasance tare da mu.