Birnin Kyiv ya fuskanci sabbin hare-haren jiragen sama cikin dare
Babban birnin Ukraine, Kyiv, ya fuskanci sabbin hare-haren jiragen saman Rasha a cikin dare.
An samu rahotannin tashin gobara da asarar rayuka a wasu gundumomi.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Ukraine ta ce mutum uku ne suka mutu a wani harin da Rasha ta kai gari a yankin gabashin ƙasar.
A yau Alhamis ne ake sa ran sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio zai gana da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov a Malaysia.
A baya-bayan nan ne dai shugaba Trump ya bayyana rashin jin daɗinsa da shugabancin ƙasar Rasha yayin da yaƙin Ukraine ke ci gaba da ta'azzara.