Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 10/07/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 10/07/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Abdullahi Bello Diginza da Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Ƙarshen rahotonnin kenan a yau Alhamis.

    Mu haɗu gobe Juma'a domin samun wasu sababbi.

  2. Najeriya ba za ta karɓi mutanen da Amurka ta kora daga ƙasarta ba - Tuggar

    Najeriya ta ce ba za ta amince ta karɓi mutanen da Amurka ke kora daga ƙasarta ba duk da irin matsin lambar da take yi wa ƙasashen Afirka, kamar yadda Ministan Harkokin Waje Yusuf Maitama Tuggar ya bayyana.

    Da yake magana ta cikin shirin Politics Today a kafar talabijin ta Channesl TV, Tuggar ya ce Najeriya na da nata matsalolin da za su sa ba za ta karɓe su ba.

    "Ku sani cewa Amurka na matsa wa ƙasashen Afirka domin su karɓi 'yan ƙasar Venezuela da ta kora daga ƙasarta, wasu ma daga gidan yari aka ɗauko su kai-tsaye," in ji shi.

    "Abu ne mai wuya Najeriya ta karɓe su. Matsalolinmu sun ishe mu, ba za mu iya karɓar 'yan Venezuela ba a Najeriya saboda da ma muna da mutum miliyan 230."

    Tun bayan hawansa mulki, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi alƙawarin korar baƙin haure miliyan ɗaya daga ƙasar.

  3. Ɗanbindiga ya harbe jami'in leƙen asiri na Ukraine

    Wani ɗanbindiga ya harbe jami'in leƙen asiri na Ukraine da tsakar rana a Kyiv babban birnin ƙasar, a acewar hukumomi.

    Maharin ya harba wa jami'in hukumar tsaron ta Security Service of Ukraine (SBU) da yawa a wani wurin ajiyar motoci bayan ya yi ta bin sawunsa, kamar yadda wani bidiyo ya nuna.

    Hukumar SBU ba ta bayyana sunansa jami'in nata ba, amma kafofin yaɗa labarai na Ukraine sun ce sunansa Kanal Ivan Voronych.

  4. Jami'an tsaro sun kashe 'yanfashin daji kusan 150 a jihar Kebbi

    Hukumomi a jihar Kebbi sun ce kimanin 'yanfashin daji 150 ne ake kyautata zaton an kashe a wani kwanton ɓauna da sojoji suka yi musu cikin daren da ya gabata.

    Sojojin ƙasa da na sama sun buɗe wuta ne kan ayarin 'yan fashin da ke kan ɗaruruwan babura a kan hanyarsu ta zuwa yankin Mariga na jihar Neja mai maƙwabtaka bayan samun bayanan sirri game da zirga-zirgarsu.

    Hon Husaini Bena, shi ne shugaban ƙaramar hukumar Danko/Wasagu da ke jihar Kebbi inda aka rutsa da 'yanfashin, kuma ya faɗa wa BBC cewa bayanai sun nuna cewa baburan da suka fito sun kai kusan 350.

    "Bayanan da muka samu ya nuna cewa sun taru a wani ƙauye mai suna Kawaye kuma suna shirin shiga garin Mariga ko Rijau na jihar Neja," in ji shi.

    "Allah ya taimaka babu ko mutum ɗaya da ya rasa ransa, ko ya jikkata a ɓangaren mutanen gari ko kuma jami'an tsaro."

    Ya ƙara da cewa bayanan da suka samu sun ce waɗanda suka tsere sun koma inda suka fito bayan janye wasu daga cikin gawawwakin mutanensu.

  5. Mun yi tattaunawa mai kyawu da Trump kan makaman kariya - Zelensky

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce ya yi wata tattaunawa "mai kyawu" da Shugaban Amurka Donald Trump kan batun ba da makaman kariya da kuma garkuwar tsaron sararin samaniyarta.

    Zelensky ya ce yana buƙatar na’urorin garkurwar tsaro 10, inda Jamus za ta biya kuɗin biyu, Norway za ta dauki nauyin ɗaya.

    A baya dai Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Runbio ya bukaci ƙasashen Turai su duba yiyuwar bai wa Ukraine din na'urorin wanda ba su amfani da su.

    Ukraine na cewa tana buƙatar ƙarin makaman kariya na gaggawa domin kare kanta daga hare-haren Rasha.

    Zelensky ya kuma bukaci Amurka ta jagoranci batun sanya tsauraran takunkumai kan Rashar.

  6. Labarai da dumi-dumi, Ƙungiyoyin da ke neman zama jam'iyyar siyasa a Najeriya sun kai 129

    Hukumar zaɓe a Najeriya ta ce zuwa yau Alhamis, 'yansiyasa sun miƙa mata buƙata 129 ta ƙungiyoyin da ke son a yi musu rajistar zama jam'iyyars siyasa.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun Independent National Electoral Commission (inec) ya fitar ta ce an bayyana sabon adadin ne yayin taron mako-mako da mahukuntanta ke yi a yau Alhamis.

    "Tun daga makon da ya gabata, an samu ƙarin masu neman rajista bakwai, abin da ya sa jimillarsu ta zama 129 zuwa yanzu," a cewar Sam Olumekun.

    Ta ƙara da cewa tana ci gaba da aiki kan buƙatun ta hanyar yin amfani da wani sabon shafin intanet da za ta ƙaddamar, maimakon a baya da take amfani da biro da takarda.

    "Hakan zai sauƙaƙa tare da hanzarta aikin. Nan da mako ɗaya hukumar za ta kammala gwajin shafin kafin ta fara aiki da shi," a cewar Mista Olumekun.

  7. Isra'ila ta kashe masu karɓar tallafi 15 a Gaza

    Aƙalla Falasɗinawa 15 ne Isra'ila ta kashe yayin da suke kan layin karɓar tallafin ƙwayoyin gina jiki a gaban wani asibiti da ke tsakiyar Zirin Gaza, a cewani wa ni asibiti.

    Asibitin al-Aqsa ya ce cikin waɗanda aka kashe akwai yara takwas da mata biyu, yayin hari ta sama da jirage suka kai kan yankin Deir al-Balah.

    Wani bidiyo daga cikin asibitin ya nuna gawawwakin yara daban-daban da kuma wasu warwatse a dandariyar ƙasa yayin da likitoci ke ba su kulawa.

    Ƙungiyar Project Hope da ke gudanar da asibitin ta ce harin keta dokar ƙasashen duniya ne. A nata ɓangaren, rundunar sojin Isra'ila na cewa wani sansanin ƙungiyar Hamas ta kai wa hari.

    Haka nan, an bayar da rahoton kashe wasu 37 a hare-haren na Isra'ila a Gaza.

    Hare-haren na faruwa ne yayin da ake ci gaba da fatan samun labarin amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta a tattaunawar da ƙasashen Amurka da Qatar da Masar ke shiga tsakanin Isra'ila da ƙungiyar ta Hamas mai iko da Gaza.

  8. EFFC na neman majalisa ta amince da dokar bincika arzikin 'yan Najeriya

    Shugaban hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci a Najeriya Ola Olukayode ya shawarci majalisar tarayyar ƙasar ta amince da ƙudirin dokar "Unexplained Wealth Bill", wanda zai ba ta damar bincikar ɗaiɗaikun 'yan Najeriya game da yadda suka tara dukiyarsu.

    Olukayode ya ce ƙudirin ya je gaban 'yanmajalisar tun a majalisa ta tara, wanda suka yi watsi da shi, kamar yadda kamfanin labarai na NAN ya ruwaito.

    "Akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin ɓarnar da ake yi arzikin ƙasarmu da kuma matsalar tsaro," a cewarsa yayin wani taro da kwamatocin majalisar tarayya suka shirya kan arzikin ƙasa.

    "Idan kana binickar ayyukan 'yanfashin daji, da ta'addanci, za ka ga suna da alaƙa da wani nau'i na cin hanci da rashawa, ko kuma karkatar da kuɗaɗen da suka kamata a yi wa al'umma aiki.

    "Ina neman ku taimaka min wajen amincewa da ƙudirin Unexplained Wealth Bill. Shekara ɗaya kenan ina neman hakan, kuma shi ne dai majalisa ta tara ta yi watsi da shi. "Idan ba mu binciki dukiyar da mutane suka tara ba ba za mu taɓa gyara al'amuran ba.

    "Akwia wani da ya yi aiki shekara a wata ma'aikata. Mun lissafa baki ɗayan albashi da alawus ɗinsa. Sai kuma muka gano gidaje biyar da yake da su, biyu a Maitama, uku a Asokoro. Amma kuma ana so mu gabatar wa kotu hujja a kansa kafin mu yi wani bincike. Wannan abin takaici ne."

  9. Al-Shabab ta ce ta kashe mutum 16 a hari kan kwalejin sojoji ta Somaliya

    Ƙungiyar Al-Shabab mai alaƙa da Al-Qaeda ta ce ta kai harin ƙunar baƙin waƙe kan wata makarantar horas da sojoji a birnin Mogadishu.

    Al-Shabab ta yi iƙirarin kashe mutum 16 a lokacin harin da ta ce ta kai a ranar Laraba.

    Ƙungiyar ta ce cikin waɗanda suka mutu har da jami’an soji biyu na ƙasashen Turai da ke aiki da rundunar samar da zaman lafiya a Somaliya da kuma wasu ƙasashe 14.

    Ma’aikatar tsaron ƙasar ta tabbatar da harin, amma ba ta bayar da wani bayani kan adadin waɗanda suka mutu ko jikkata ba.

  10. Kalli yadda shugaban Laberiya ya turance Donald Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya yaba wa shugaban ƙasar Laberiya Joseph Boakai saboda turancin Ingilishi da ya zabga a lokacin wata ganawa da shugaban na Amurka ya yi da shugabannin wasu ƙasashen Afirka a fadar White House.

    Trump ya ce wa Boakai "ka iya turanci".

  11. Najeriya ta kama mazaƙutar jakai fiye da 10,600 da aka yi yunƙurin safararsu

    Hukumar hana fasa ƙwauri ta Najeriya, ta kama wata mota da ke ɗauke da wata kontena maƙare da Mazaƙutar jakai fiye da 10,600.

    Hukumar ta kama motar a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

    Maimagana da yawun hukumar ta Custom, Abdullahi Aliyu Maiwada shida wa BBC cewa an daskarar da mazaƙutar jakunan ne cikin kontena da nufin safararsu zuwa ƙasashen ƙetare.

    Abdullahi Maiwada ya ce sun samu nasarar kama sassan jakunan bayan samun bayanan sirrin da suka jima suna tattarawa game da safarar.

    Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ake kashe jakuna a Najeriya, ''wannan yana nuna girman yadda ake kashe waɗannan dabbobi a Najeriya da makwabtan ƙasashe''.

    Maiwada ya ce hakan na barazana ga rayuwar dabbobin, wanda zai iya sanya wa su ƙare a ƙasar idan ba a ɗauki mataki ba.

    Kakakin hukumar ya ce ana safarar wasu sassan irin waɗanan dabbobi daga ƙasashen Afirka ta dama tare da kawo su Najeriya daga nan kuma a kai su ƙasashen waje.

  12. Rashin abinci mai gina jiki: 'Najeriya ce kan gaba a Afirka, ta biyu a duniya'

    Babbar mai taimaka wa shugaban Najeriya Bola Tinubu kan harkokin lafiyar al'umma, Uju Anwukah ta ce ƙasar ce ta farko a Afirka kuma ta biyu a duniya a yawan mutanen da ke fama da ƙarancin abinci mai gina jiki.

    Hadimar Tinubun ta bayyana hakan ne ta bakin shugaban kwamitin kula da ingancin abinci na Majalisar Wakilan ƙasar, Chike Okafor, wanda ya ce Najeriya na kashe dala biliya ɗaya da rabi a kowace shekara sakamakon matsalar rashin abinci mai gina jiki.

    Anwukah ta wadda ta yi magana kan inganta abinci ta ce ƙasar ƙoƙari ta wanan fanni ta hanyar ƙirƙiro da shirin N-774 da yanzu haka majalisar Wakilan ƙasar ta shirya taron ƙasa da ake gudanawar kan samar da wadataccen abinci mai gina jiki a ƙasar.

    Hakan na zuwa ne kwana biyu bayan da Ƙungiyar agaji ta ƙasar, Red Cross Nigeria ta ce akwai kimanin yara mliyan 5.4 da ke fama da uƙubar yunwa a jihohin ƙasar tara da ke fama da matsalar tsaro.

  13. Gwamnatin Najeriya ta ciyo bashin dala miliyan 747

    Najeriya ta karɓo bashin dala miliyan 747 daga bankunan zuba jari ƙarƙashin jagorancin Deutsche Bank domin gudanar da wani ɓangare na aikin kilomita 700 na babban titin gaɓar teku.

    Kakakin ma'aikatar kuɗin ƙasar, Mohammad Manga ya ce ba shin shi ne irinsa na farko mafi girma da ƙasar ta ciyo domin aikin titi.

    Kashin farko na babban titin da aka yi da kuɗin ramcen da aka karɓo ya kai kilomita 47.47 a cewar Manga.

    Ana sa ran aikin titin - wanda zai ɗauki shekara takwas ana yi zai laƙume kuɗi kimanin dala biliya 11.

    Babban titin zai haɗa cibiyar kasuwancin ƙasar Legas da birnin calabar mai tashar jiragen ruwa da ke kudu maso kudancin ƙasar.

  14. 'Ba don Tinubu ba ko zaɓen fitar da gwani Buhari ba zai ci ba'

    Babban mai taimaka wa Shugaba Tinubu kan kafofin yaɗa labarai, Temitopr Ajayi ya mayar da martani kan kalaman tsohon babban sakataren gwamnatin tarayya da ya ce ko ba Tinubu Buhari zai ci zaɓen 2015.

    A ranar Laraba ne tsohon babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya ce Buhari ne jigon nasarar APC a 2015 ba Bola Tinubu ba kamar wasu da dama ke iƙirari.

    Boss Mustapha ya ce ƙuri'un da APC ta samun zaɓen 2015 an same su ne sakamakon tsantsar farin jinin Buhari.

    To amma Temitope Ajayi, ya ce ba don taimakon Tinubu ba, babu ta yadda za a yi Buhari ya ci zaɓen fitar da gwani, ballantana a yi maganar nasara a babban zaɓe.

    Ajayi ya ce bai kamata a manta irin ƙoƙarin da Tinubu ya yi ba don tabbatar da Buhari ya zama shugaban ƙasa.

    ''Mun ji Buhari yana da ƙuri'a miliyan 12 daga jihohin arewa, amma ai duk da haka sau uku yana faɗuwa zaɓen shugaban ƙasa, a 2003 da 2007 da kuma 2011'', in Ajayi.

  15. Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Okpehbolo a gwamnan Edo

    Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Monday Okpebholo na jam'iyyar APC a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Edo.

    Kotun mai alƙalai biyar - ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a, Mohammed Garba Lawal - ta ce masu ƙorafin ba sun kasa gabatar gamsasshiyar hujja kan iƙirarin da suka yi lokacin shari'ar.

    Masu gabatar da ƙarar sun gabatar da ƙorafin cewa Gwamna Okpebholo bai ci zaɓen gwamnan jihar ba, bisa dalilan rashin aiki da dokokin zaɓe da amfani da haramtattun ƙuri'u.

    Kotun ta tabbatar da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yanke a watannin baya.

    A shekarar da ta gabata ne aka gudanar da zaɓen gwamnan jihar da ke kudu maso kudancin Najeriya.

  16. Dangote zai gina rumbum man fetur da dizel a Namibia

    Matatar mai ta Dangote da ke Najeriya za ta gina wani rumbun ajiyar man fetur a ƙasar Namibiya domin adana ganga miliyan 1.6 na man fetur da dizel domin sayarwa a ƙasashen kudancin Afirka.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wasu majiyoyi na cewa za a yi amfani da rumbun wajen yin hada-hadar fetur a ƙasashen Botswana, da Namibiya, da Zambiya, da kuma Zimbabwe.

    Haka kuma, Dangote na duab yiwuwar fara kai man fetur zuwa ƙasar Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.

    Wani jami'i a hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan Namibiya ya tabbatar wa Reuters shirin, yana mai cewa za a gina ma'adanar ne a yankin Walvis Bay da ke ƙasar.

    A watan da ya gabata ne wata majiya ta bayyana cewa matatar Dangote ta fara sayar da mai zuwa nahiyar Asiya, karon farko da matatar ta yi hakan a wajen nahiyar yammacin Afirka.

  17. Sojojin Najeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram 24

    Sojojin Najeriya - ƙarƙashin rundunar 'Operation Hadin Kai' mai yaƙi da ta'addanci - sun kashe mayaƙan Boko Haram 24 a wani mummunan hari da suka ƙaddamar kan maɓoyarsu a yankin raewa maso gabashin Najeriya.

    Mataimakin dakartan hulda da jama'a na rundunar, Captain Reuben Kovangiya ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar.

    Captain Kovangiya ya ce cikin wadanda aka kashe har da mutum biyar da ke samar wa mayaƙan makamai, waɗanda aka yi wa kwanton-ɓauna a wani samame da sojojin suka ƙadamar cikin dare.

    Sanarwar ta ce sojojin sun ƙaddamar hare-haren ne dajin Sambisa da yankin Timbuktu da tsaunukan Mandara da wasu wurare, tun daga ranar 4 zuwa 9 ga watan da muke ciki.

    Sojojin sun kuma samu nasarar ƙwato makamai da alburusai da wasu kayyakin yaƙin ƙungiyar ta Boko Haram.

  18. Muna duba yiwuwar kawo ƙarshen yaƙin Gaza na dindindin - Isra'ila

    Wani jami'in Isra'ila ya ce ƙasarsa za ta duba yiwuwar kawo ƙarshen yaƙin Gaza na dindindin idan Ahmas ta amince da ƙudirin farko na tsagaita wuta na kwana 60 tare da miƙa makamanta.

    Jami'in ya ce Isra'ila za ta ci gaba da kai hare-harenta idan har Hamas ta ƙi amincewa da waɗannan buƙatu.

    Tun da farko, Hamas ta ce tattaunawar da ake yi kan cmma yarjejeniyar tsagaita wutar na da tsauri.

    Can a Gaza Isra'ila ta ci gaba da hare-hare a faɗin yankin, inda rahotonni suka ce an kashe aƙalla Falasɗinawa 23 ciki har da ƙananan yara da dama.

  19. ...Daga Bakin Mai Ita tare da Ikram ta Labarina

    Shirinmu na Daga Bakin Mai Ita na wannan makon, mun kawo muku tattaunawa da tauraruwa a masana'antar Kannywood, Amina Muhammed Rabi'u.

    Ƴar asalin jihar Katsina, Amina, wadda aka fi sani da Ikram a fim ɗin Hausa mai dogon zango na 'Labarina' ta yi bayani kan rayuwarta ta yanzu, ta baya da kuma abin da yake son cimmawa a gaba.

  20. Majalisar Wakilai ta gayyaci gwamnan Fitalo kan matsalar tsaron jihar

    Kwamitin wucin gadi kan matsalolin tsaron jihar Filato na Majalisar Wakilan Najeriya ya gayyaci gwamnan jihar Caleb Mutfwang da tsaffin gwamnonin jihar da sauran masu ruwa da tsaki na jihar zuwa wani babban taro da nufin lalubo hanyar magance hare-haren da jihar ke fuskanta a jihar.

    Jaridar Dailu Trust ta ambato shugaban kwamitin, Hon. Dr Wale Hammed na cewa matakin wani yunƙuri ne na ɗaukar matakan da suka dace domin magance kashe-kashen da jihar ke fuskanta.

    A baya-bayan jihar - wadda ke tsakiyar Najeriya - ta fuskanci hare-haren da faɗan ƙabilanci da ya haddasa asarar rayuwa da dukiyoyi masu dimbin yawa.

    Dakta Hammed ya ce yana fatan taron - wanda ya ƙunshi duka masu ruwa da tsaki na jihar - zai kawo ƙarshen matsalar da ta jima tana ci wa jihar tuwo a ƙwarya.

    Cikin wata hira da BBC Hausa a makon da ya gabata, Gwamna Jihar Caleb Muftwang ya alaƙanta rikice-rikicen da jihar ke yawan fama da su, da gazawar hukumomi, wajen hukunta masu haddasa rikicin da ya-ƙi-ci-ya-ƙi-cinyewa.