Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 13/01/2025

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Ibrahim Muhammad da Isiyaku Muhammed, Rabiatu Kabir Runka

  1. 'Gobara ta laƙume kadarorin sama da naira biliyan 67 a 2024 a Najeriya'

    Hukumar kashe gobara ta Najeriya ta ce gobara ta laƙume kadarorin aƙalla naira biliyan 67.1 a shekarar 2024 da ta gabata.

    A wata sanarwa da tashar Channels ta ruwaito daga shugaban hukumar, Abdulganiyu Jaji a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, ya ce bayan asarar kadarorin, gobara ta kashe aƙalla mutum 100 a shekarar.

    Sai dai ya ce hukumar ta taimaka wajen tseratar da kadarori na sama da naira tiriliyan 1.94, sannan sun taimaka wajen tseratar da sama da mutum 30,890.

    Jaji ya ce gobara ta fi tashi a lokacin sanyi, inda ya yi kira ga mutane su ƙara sa ido tare da ɗaukar matakan kariya.

  2. An sace ƴar ƙasar Austria a Nijar

    A Jamhuriyar Nijar wasu mutane ɗauke da makamai sun sace wata mata ƴar ƙasar Austria Eva Gretzmacher, da ke zaune a jihar Agadez.

    Wasu bayanai sun ce wasu mutane ɗauke da bindigogi ne suka kutsa kai gidan matar tare da tursasa mata shiga mota, kana suka tafi da ita.

    Matar mai kimanin shekara 70 tana ayyukan agaji ne a ƙasar ta Nijar, inda ta yi kusan shekara 20 tana rayuwa, kamar yadda kafar Air Info Agadez ta ruwaito.

    Sai dai har yanzu Nijar ba ta ce komai ba, amma ma'aikatar harkokin wajen Austria ta ce tana tattaunawa da wakilan tarayyar turai da hukumomi domin kuɓutar da ita.

  3. Biden ya tattauna da Netanyahu kan tsagaita wuta a Gaza

    Shugaba Biden na Amurka ya tattauna ta wayar tarho da firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, game da tattaunawar da ake yi ta tsagaita wuta a Gaza da kuma sako mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su.

    Mista Biden ya kuma jaddada buƙatar ƙara yawan taimakon jin ƙai a zirin.

    Ana tunanin tattaunawa kan yiwuwar tsagaita tsakanin Isra'ila da Hamas wutar na cigaba, amma akwai wasu muhimman abubuwa da suke kawo tsaiko.

    Wannan wayar da suka yi wani ɓangare ne na yunƙuri na ƙarshe da yake yi na cimma yarjejeniya kwanaki kaɗan kafin Donald Trump ya gaje shi.

    Tattaunawar ta zo ne bayan Netanyahu ya tura manyan jami'an gwamnati, ciki har da daraktocin babbar cibiyar leƙen asirin ƙasar, wato Mossad da na Shin security service zuwa Qatar domin tattauna batun tsagaita wutar, wadda gwamnatin Qatar da Amurka da Masar ke jagoranta.

    Sannan rahotanni sun cewa Netanyahu yana ganawa da ministocinsa da suke adawa da tsagaita wutar, yana ƙoƙarin fahimtarsu, tare da kira da kar su ajiye aiki.

    Shi dai Mista Trump ya ce za a yi ta ta ƙare a Gabas ta Tsakiya, idan har aka kuskura aka ƙi sakin mutanen da aka yi garkuwa da su kafin ya hau mulki.

  4. Hajjin 2025: Gwamnatin Najeriya ta zaɓi kamfanonin jirage huɗu domin jigilar maniyyata

    Gwamnatin Najeriya ta amince da kamfanonin jiragen sama guda huɗu domin jigilar maniyyata Hajjin bana.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban hukumar jin daɗin alhazai ta Najeriya, NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman ya fitar a ranar Lahadi, inda ya ce an zaɓi kamfanoni huɗu ne daga cikin guda 11 da suka nuna sha'awar aikin jigilar maniyyatan, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

    Ya ce kamfanonin huɗu su ne: Air Peace Ltd, da wani kamfanin ƙasar Saudiya mai suna Fly-Nas da Max Air da kuma UMZA Aviation Services Ltd.

    Ya ƙara da cewa kwamiti mai mutum 32 da aka kafa a ranar 26 ga Nuwamban bara ne suka zauna suka tantance kamfanonin, kafin suka amince da guda huɗun

  5. Waɗanda suka rasu a gobarar Los Angeles sun kai 24

    Adadin mutanen da aka tabbatar da mutuwarsu yanzu haka a gobarar birnin LA, wato Los Angeles ya kai ashirin da huɗu.

    Ko da yake an samu ci gaba wajen daƙile gobarar, ƴan kwana-kwana na can na shiryawa tarar gagarumar iska mai ƙarfi ta tsawon kwanaki da ke barazanar dagula al'amura.

    Wakiliyar BBC ta ce ta kowanne ɓangare, gabas da yadda kudu da arewa ɓarna ce kawai kake gani a nan inda muke, kuma haka lamarin yake a kowanne ɓangare na birnin Lo Angels.

    An ɓullo da matakan gaggawa don taimakawa waɗanda gobarar ta shafa da kuma kare su daga masu zamba da masu fakewa da bala'i wajen tsuga farashi.

    An kama mutane da dama da laifin kwasar ganima a wuraren da aka fasa, ciki har da wani mutum da ke sanye da kayan kashe gobara.

  6. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin, inda za mu kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sadarwa domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.