Najeriya na cikin ƙasashen da ake kai wa jami'an lafiya hari - WHO
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce Najeriya na cikin ƙasashen da aka samu rahotannin kai hare-hare kan jami'an lafiya da cibiyoyin kiwon lafiya.
WHO ta ce an tabbatar da sama da hare-hare 10,000 kan harkokin lafiya tun daga shekarar 2018 zuwa yanzu, a ƙasashe da yankuna 29.
Hare-haren sun yi sanadin mutuwar kusan mutum 5,700 tare da jikkata wasu 8,500, amma WHO ta ce kawo yanzu ba a gurfanar da kowa a gaban hukuma kan waɗannan hare-hare ba.
Altaf Musani, daraktan sashen agaji da kula da bala'o'i na WHO, ya bayyana alaluman a wani taron manema labarai a Geneva.
Ya ce cibiyoyin lafiya da tsarin kiwon lafiya na ƙarƙashin kariyar dokokin ƙasa da ƙasa, musamman dokokin jinƙai da haƙƙin ɗan Adam da yarjejeniyar Geneva ta tanada.
Sai dai ya ce duk da sama da hare-hare 10,000 da WHO ta tabbatar, “babu ko guda ɗaya da ya shiga tsarin da zai kai ga hukunta masu aikata su.”
A bana kaɗai, WHO ta ce ta tabbatar da hare-hare 914, waɗanda suka kashe mutum 911 tare da jikkata 1,486.
Ukraine, Lebanon da yankunan Falasɗinawa ne suka fi yawan samun hare-haren a bana, yayin da aka kuma samu rahotonsu daga Myanmar, Iran, Sudan, Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, Sudan ta Kudu, Rasha, Syria da Najeriya.
Haka kuma, an samu rahotanni 44 na sacewa, kama ko tsare jami'an lafiya da marasa lafiya, lamarin da ya shafi mutum 148.