Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 18/08/2025.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida

  1. Ƴansandan Isra'ila sun tarwatsa masu zanga-zangar kawo ƙarshen yaƙin Gaza

    Ƴansanda kwantar da tarzoma sun tarwatsa gungun masu zanga-zanga a wajen ginin hedikwatar ofishin jam'iyyar Likud ta Firaministan ƙasar da ke Tel Aviv.

    Dubban al'umma ne dai ke zanga-zangar da ta kasance mafi girma tun soma yaƙin Gaza shekaru kusan biyu.

    Mutanen da suka kuɓuta daga hannun Hamas da 'yanuwa wadanda har yanzu ke tsare sun yi jawabai ga dandazon jama'ar da ke wannan bore, inda suka nemi a gaggauta kawo karshen yaƙin.

    Wakiliyar BBC ta ce Firaministan ƙasar ya zargin masu boren da kokarin haifar da nakasu a tattaunawar da ake yi da Hamas.

    Zanga-zangar ta haɗa da yajin aikin kwana guda domin adawa da manufofin gwamnatin Isra'ila na ƙwace cikakken ikon Gaza

  2. Isra'ila na fuskantar matsin lamba kan shigar da kayan agaji Gaza

    Isra'ila na sake fuskantar matsin lamba kan bada damar shigar da kayan agaji zirrin Gaza, yayinda yunwa mai tsanani ke cigaba da laƙume rayuka.

    Firaiministan Falasɗinawa, Mohammad Mustafa, da ministan harkokin wajen Masar, Badr Abdel-Atty, na ziyartar garin Rafah da ke kan iyaka domin sake fito da girman matsalar.

    Wakiliyar BBC da ke cikin ayarin ta bada labarin yadda Motoci maƙare da kayan abinci suka yi jeren gwano suna jiran izini domin shiga Gaza ta iyakar.

    A makon da ya gabata sama da ƙungiyoyin agaji 100 sun zargi mahunkuntan Isra'ila da datse rumbunan da suke jibge kayan tallafi - zargin da Isra'ila ta musanta.

  3. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu ɗaura daga inda muka tsaya a jiya wajen kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sadarwa irin su Facebook da X da Instagram da ma zaurenmu na Whatsapp domin karanta wasu labaran da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.