Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/06/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi, Aisha Babangida

  1. An tarwatsa masu zanga-zanga da hayaƙi mai sa hawaye a Kenya

    Masu zanga-zanga a Kenya sun sha duka da hayaƙi mai sa ƙwalla bayan sun fito suna boren neman kadin mutuwar wani fitaccen mai fafutika a ofisihin 'yansandan ƙasar.

    Masu zanga-zangar sun ce wasu matasa ɗauke da tsumagiya da makamai a kan babura ne suka kai musu hari, sannan suka zargi ƴansanda da zuba ido ana cin zarafinsu.

    Tun da farko, dama jami'ai sun yi ƙoƙarin amfani da hayaƙi mai sa ƙwalla wajen tarwatsa masu zanga-zangar.

    Ƴansanda a Kenya sun ce Albert Ojwang ya mutu ne sakamakon raunin da ya ji wa kansa, batun da masu shigar da ƙara suka musanta

  2. Martanin shugabannin Turai kan yaƙin Isra'ila da Iran

    Shugaba Macron na Faransa ya ce duk wani yunƙuri na sauya gwamnati a Iran na iya haifar da gagarumin rikici - kuma yana fatan Amurka za ta sake duba batun diflomasiya.

    Shugaba Erdogan na Turkiyya ya zargi firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da kasancewa babbar barazana ga tsaron gabas ta tsakiya.

    Amma shugaban gwmanatin Jamus, Merz, ya nuna goyon-bayansa ga hare-haren Isra'ila - ya ce tana aikin cire kazantar da sauran ƙasashen duniya suka tara.

  3. Isra'ila na Iran na ci gaba da kai wa juna hare-hare

    Isra'ila da Iran na ci gaba da yi wa juna lugeden wuta a rana ta biyar da soma yaƙi babu sararawa.

    Sojojin Isra'ila sun ce sun ƙaddamar da jerin hare-hare a cibiyoyin harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa na Iran.

    Sojojin Iran kuma sun ce hare-harensu sun karkata ne a kan wuraren na'urorin tsaron Isra'ila da kuma buƙatar mazauna manyan birane su fice.

    Yayin da kuma a wani labarin, kafar yada labaran Iran ta bada rahoton yi wa babban bankin ƙasar kutse da katsewar intanet.

  4. Iran ta miƙa wuya ba tare da wani sharaɗi ba - Trump

    Donald Trump ya buƙaci Iran ta miƙa wuya ba tare da sharuɗa ba, yayin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta, yana mai jadadda cewa ana neman kure haƙurinsa.

    A wani sakon mai tsayi da ya wallafa a shafinsa Social Truth, Mista Trump ya yi gargaɗin cewa kai wa ga jagoran addinin Iran, Ali Khamenei ba abu ne mai wahala ba, amma dai Amurka ba za ta kashe shi ba, a yanzu.

    Jawaban shugaban na zuwa ne gabanni tattaunawa da kwamitin tsaro na Amurka.

    Ana dai ci gaba da yaɗa jita-jitar cewa Amurka na shirin shiga wannan yaƙi.

  5. Wane ne Ayatollah Ali Khamenei, jagoran addini na ƙasar Iran?

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya ƙi amincewa da yunƙurin Isra'ila na kashe jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei a yaƙin da take yi da Iran, lamarin da kafofin watsa labaran Amurka suka ruwaito yana cewa "bai dace ba."

    Bayan burin da Isra'ila ke da shi na tarwatsa abin da take kira babbar barazanar da shirin Iran na mallakar makamin nukiliya ke yi ga ƙasarta a matsayin dalilin hare-haren na yanzu, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyanhu, ya ce kawo sauyin gwamnati a Iran ma na cikin burinsu.

    Netanyahu ya sha faɗa a baya cewa akwai buƙatar ƴan ƙasar su tashi tsaye wajen ƙwatar ƴancinsu daga jagoran.

    A wannan maƙalar, za mu yi nazarin wane ne jagoran addinin, da irin ƙarfin ikonsa a ƙasar, da kuma rawar da iyalansa suke takawa a siyasar ƙasar.

  6. Isra'ila ta ce ta kashe kwamandan sojin Iran

    Isra'ila ta ce ta kashe wani babban kwamandan sojin Iran wanda shi ne shugaban sojoji a wannan yaƙin da ake gwabzawa tsakanin ƙasashen biyu.

    Sojojin Isra'ila sun ce Ali Shadmani ya gamu da ajalinsa a hare-haren da suka kai tsakiyar birnin Tehran ne.

    Kwamandan na da kusanci sosai da shugaban addinin kasar, Ali Khamenei, wanda ya ƙara masa matsayi bayan kashe magabacinsa a makon da ya gabata.

    Wakilin BBC ya ce mutuwarsa na nuna tabbas Isra'ila na samun bayanai sirri sosai kuma ta kutsa cikin rundunar sojin Iran .

  7. Burina a kawo ƙarshen yaƙi tsakanin Iran da Isra'ila na dindindin - Trump

    Shugaba Trump ya ce ba neman tsagaita wuta a yaƙin da ake yi tsakanin Isra'ila da Iran yake yi ba, inda ya nanata cewa so yake a kawo ƙarshen yaƙin da gaske.

    A lokacin da yake magana da ƴanjarida a lokacin da yake shiga jirgin shugaban ƙasa, ya ce tuntuni ya kamata a ce Iran ta cimma yarjejeniya da Amurka kan shirinta na Nukiliya kuma shi ba shi da wani lokacin ja-in-ja.

    Gwamnatin Tehran na tattaunawa da Washington kafin Isra'ila ta soma kai hare-hare.

    Shugaba Trump ya katse taron G7 da yake halarta a Canada inda ya koma Amurka saboda rikici na gabas ta tsakiya.

  8. Isra'ila ta kashe gomman Falasɗinawa wajen karɓar agaji a Gaza

    An kashe gomman Falasɗinawa a hare-haren Isra'ila a Gaza wajen karban kayan tallafi.

    Shaidu da masu aikin ceto sun ce sojojin Isra'ila sun kashe sama da mutane 51 da jikkata 200, yayin da suke jiran a ba su garin fulawa a kusa da inda sansanin raba kayan tallafi na MDD da ke Khan Yonnis yake.

    Shaidu sun fada wa BBC cewa an rasa rayukan ne a hare-hare da jirage marasa matuka da tankokin yaƙi.

    Wakilin BBC ya ce wanna shi ne hari mafi muni a jerin irin hare-hare da ake kai wa kan mutanen da suke fitowa suna neman tallafin abinci a Gaza.

    Asibitin Nasser da ke kusa da yankin ya cika makil da masu rauni.

  9. Ƴansanda sun kama 'ƴandaba' 51 a Kano

    Rundunar ‘yansanda jihar Kano a Najeriya ta sanar da kama mutum 51 da take zargi da zama ‘yan daba a cikin wani samame da ta kwashe kwana uku tana kai wa a unguwanni daban-daban na na garuruwa cikin ƙwaryar birnin jihar.

    Ta kuma ce an samu makamai da miyagun ƙwayoyi daga hannun waɗanda ta kama ɗin.

    Wannan dai na zuwa yayin da samun rahotanni faɗace-faɗace tsakanin ‘yandaba da haren-haren ƙwacen waya a sassan birnin na Kano ke ƙaruwa.

    Wasu rahotanni daga wasu majiyoyi na cewa faɗace-faɗacen na ƙwanan nan su yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutum biyar, ko da yake rundunar ba ta tabbatar da alƙalumman kashe-kashen ba.

  10. Al'ummar Nijar sun koka kan ƙarancin wutar lantarki

    A jamhuriyar Nijar matsalar ɗauke wutar lantarki a Yamai da sauran jihohin yammacin ƙasar na ƙara ƙamari, lamarin da ke ɗaga hankalin ƴanƙasar.

    Wannan ya sa ƙungiyoyi da sauran jama'a sun fara kiraye-kiraye ga gwamnatin mulkin sojan ƙasar ta fito fili ta yi wa ƴanƙasa cikakken bayani kan dalilin da ya sa matsalar lantarki ta ƙi ci, ta ƙi cinyewa.

    Jama'a musamman masu ƙananan sana'o'i sun koka kan yadda kamfanin dillancin lantarki na kasa ke kawo wa kwastomominsa kuɗin lantarki da ya wuce ƙima duk da rashin wutar lantarkin.

    Haka kuma masu sana'o'in sun bayyana cewa sun tafka asara saboda rashin wutar, wanda ke taɓa yadda suke adana kayayyakinsu.

  11. "Fiye da mutum 450 sun mutu a Iran tun daga ranar Juma'a"

    A cewar hukumar kare haƙƙin ɗan'Adam a Iran (HRANA), fararen hula 224 ne suka mutu, yayin da 188 suka jikkata a hare-haren Isra’ila a ƙasar.

    HRANA ta kuma bayyana cewa sojoji 109 ne suka mutu inda kuma 123 suka jikkata.

    Haka kuma mutum 119 da ba a gano ko su wanene ba aka ruwaito sun mutu, yayin da 335 suka jikkata wanda ya kawo jimillar adadin waɗanda suka mutu zuwa 452 da suka mutu da kuma 646 da suka jikkata.

    Kafofin watsa labarai na gwamnatin Iran dai ba su fitar da cikakken bayani ba dangane da adadin waɗanda suka mutu, inda ba su fitar da cikakken bayani daga gwamnati ba.

  12. Fiye da mutum 18 sun mutu a hari kan sansanin ƴangudun hijira a Sudan

    Rahotanni sun ce yawan mutanen da suka mutu a harin da dakarun RSF suka kai da jirage marasa matuƙa a wani sansani da ke kula da ’yan gudun hijira a garin al-Fashir da ke yammacin Sudan ya haura 18.

    Shafin intanet na Sudan Tribune ya ce harin ya faru ne a ranar 15 ga Yuni, kuma wani likita a asibitin soja na cikin garin ya tabbatar da cewa mutum 18 sun mutu, yayin da wasu 50 suka jikkata.

    Harin ya zo ne bayan wani mummunan hari da RSF ta kai a garin al-Fashir, babban birnin jihar Darfur ta arewa— birni mafi girma a yankin da ba ya ƙarƙashin ikon RSF.

    Tun watan Afrilun 2024 ne dakarun RSF ta kewaye birnin.

  13. Wane hali ake ciki a Benue?

    Wane hali ake ciki a Benue yanzu kuma wane mataki gwamnati ke ɗauka domin kawo ƙarshen rikice-rikicen?

    Rikicin jihar Benue na ci gaba da ɗaukar hankali a Najeriya, musamman yadda matsalar ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa.

  14. Masu ceto na bincike a unguwannin Tehran bayan hare-haren Isra'ila

    Jami’an agajin gaggawa a birnin Tehran na ci gaba da bincike a cikin ɓaraguzan gine-gine bayan hare-haren da Isra’ila ta kai wa babban birnin Iran.

    Cikin wani sakon da suka wallafa a shafin Telegram, hukumar bayar da agajin gaggawa ta Iran, wato Red Crescent Society, ta ce: "Harin da gwamnatin Isra’ila ke kai wa kan gidajen fararen hula na ci gaba da faruwa," sannan sun ƙara da cewa suna bayar da "agaji ga waɗanda suka ji rauni da waɗanda abin ya shafa."

    Isra’ila ta fara kai hari kan wasu muhimman cibiyoyin nukiliya da wasu wurare a Iran tun a ranar Juma’a da ta gabata.

  15. Mutum 154 aka kai asibiti bayan hare-haren Iran - Ma'aikatar lafiyar Isra'ila

    Ma’aikatar lafiyar Isra’ila ta bayyana cewa mutum 154 ne aka kai asibitocin Isra'ila tun daga daren jiya sakamakon hare-haren da Iran ta kai.

    Cikin waɗanda aka kai asibiti, an ce guda huɗu na cikin “matsakaicin hali”, 130 na da “rauni mai sauƙi”, 15 kuma ana ci gaba da tantance su, yayin da biyar ke karɓar kulawa saboda tashin hankali.

    A sabon bayani da ta fitar, ma’aikatar lafiyar Iran ta ce aƙalla mutum 224 ne suka rasa rayukansu, fiye da 1,200 kuma sun jikkata sakamakon hare-haren jiragen saman Isra’ila tun daga ranar Juma’a.

    Isra’ila ta bayyana cewa aƙalla mutane 24 ne suka mutu sanadiyyar hare-haren Iran a cikin wannan lokaci.

  16. Rikice-rikice uku da suka sa kashe-kashen Benue suka ƙi ci suka ƙi cinyewa

    Rikicin jihar Benue na ci gaba da ɗaukar hankali a Najeriya, musamman yadda matsalar ke ci gaba da haddasa asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa.

    Jihar Benue - wadda ke tsakiyar Najeriya - ta kasance kan gaba a jihohin da ke fama da matsalar tsaro a ƙasar.

    Sau da yawa akan alaƙanata rikicin jihar da addini ko ƙabilanci.

    To amma shugaban ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International a Najeriya, Mallam Isa Sanusi ya ce rikicin jihar ba shi da alaƙa da addini, kamar yadda ake bayyanawa.

    ''Ƙungiyarmu ta sha gudanar da bincike masu yawa kan rikicn jihar, kuma abin da muka gano shi ne rikicin ba shi da alaƙa da addini ko ƙabilanci ko kaɗan'', in ji shi.

  17. Kafofin yaɗa labaran Iran sun ce ƙasar ta kai hari cibiyar tattara bayanan sirri ta Isra'ila

    Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce ƙasar ta kai hari kan cibiyar tattara bayanan sirri ta Isra'ila, wato Mossad.

    Kamfanin dillancin labaran ƙasar na Tasnim ya wallafa wasu jerin hotuna da ya ce suna nuna yadda shalkwatar cibiyar Mossad ke ci da wuta.

    Tasnim, ya ambato rundunar juyin juya halin Iran, na cewa ƙasar ta kai hari kan cibiyar ne ta hanyar amfani da makamai masu linzami.

    A wani saƙo da kamfanin dillancin labaran na Iran ya wallafa a shafinsa na Telegram, ya ce: "A wani salo a ƙwarewa makaman IRGC masu linzami sun faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra'ila, duk kuwa da ƙarfin tsaron sararin samaniya na zamani da ƙasar ke da shi.''

    Kawo yanzu Isra'ila ba ta ce komai ba game da wannan iƙirari, kuma saboda dokokin taƙaita yaɗa labarai da gwamnati ta sanya, kafofofin yaɗa labaran da ke aiki a ƙasar ba za su iya bayar da labaran wasu wuraren da aka kai wa hari ba.

  18. 'Yayin da hankula ke kan Iran, an kashe aƙalla mutum 45 a Gaza

    Falasɗinawa da dama sun mutu yayin wata mummunar harin da ya faru kusa da wurin rabon agaji a Gaza.

    Ma’aikatar lafiya ta Hamas ta bayyana cewa mutum 45 ne aka kashe ta harbin bindiga daga sojojin Isra’ila inda babban asibitin da ke aiki a yankin ke fama da yawan mutanen da suka jikkata. BBC ta nemi martani daga Rundunar sojin Isra’ila (IDF).

    Wannan na iya zama hari mafi muni a cikin hare-haren bindiga da ake kai wa kusan kowace rana a kusa da wuraren rabon agaji a Gaza.

    Shaidu sun ce sojojin Isra’ila sun buɗe wuta ne tare da harba bam a wurin rabon kayan abinci a gabashin birnin Khan Younis.

    An sami cunkoson jama'a sosai a asibitin Nasser inda mutane da dama da suka sami rauni suke kwance a ƙasa yayin da ma’aikatan lafiya ke kula da su.