Rufewa
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 28/12/2024
Abdullahi Bello Diginza da Ahmad Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Isra'ila ta zargi shugaban wani babban asibiti a arewacin Gaza a matsayin mamban Hamas.
Ta ce tana tsare da Dr Hussam Abu Safiya, yana kuma amsa tambayoyi.
A wata sanarwa, rundunar sojin Isra'ila ta ce ta samu makamai tare da kama ɗaruruwan mayakan Hamas a farmakin da ta kai a asibitin na Kamal Adwan.
Mataimakin ministan lafiya na Gaza ya shaida wa BBC cewa jami'an asibitin kusan 100 aka yi wa tambayoyi cikin yanayi marar kyau.
Hukumar lafiya ta duniya ta ce asibitin yanzu ya zama kufai kuma an tarwatsa shi.
Shelkwatar tsaro ta Najeriya ta musanta cewa ƴan bindiga na amfani da jirage mara matuki wajen kai hare-hare a wasu sassan ƙasar, inda ta ce ƙananan abubuwa ne suke amfani da su waɗanda ba su da wani tasiri.
Tun da farko, akwai wasu rahotanni da ke cewa ƴan bindiga na far wa sansanonin soji da jirage marasa matuki a baya-bayan nan, abin da ya janyo jikkatar wasu sojoji.
Sai dai a wata sanarwa,daraktan yaɗa labaru na rundunar tsaro ta Najeriya, Manjo-janar Edward Buba, ya yi kira da a kwantar da hankali kan batun.
A cewarsa, lamarin ba shi da wata barazaga ga tsaron ƙasar.
"Ba za mu kira abubuwan da suke amfani da su a matsayin jirage mara matuki ba. Waɗannan abubuwa ne da suka je suka saya domin zuwa su yi amfani da shi, kuma babu wata barazana," in ji Buba, a wani taron manema labarai a Abuja ranar Juma'a.
Ya ce suna amfani da waɗannan nau'rori ne domin firgitarwa, amma ba don hari ba.
Buba ya ƙara da cewa sojojin Najeriya na shirye domin daƙile ayyukan ƴan ta'adda.
"Muna cikin yaƙi da masu ta da ƙayar-baya, kamar yadda kuke gani a wasu ƙasashe irinsu Ukraine da Isra'ila. Amfani da jirage marasa matuki ba sabon abu bane a yaƙin sari-ka-noke," a cewar Buba.
Lebanon ta kori mutane kusan 70 da suka haɗa da jami'ai da sojoji da take zargin sun tsero ne daga makwabciyarta Syria.
Sabbin hukumomin Damascus na gudanar da aikin da suka kira na kakkaɓe gwamnatin Assad.
Kafofin yaɗa labarai na cikin gida sun ce sojoji da dama ne aka gani cikin wata buɗaɗɗiyar mota a garin Jbeil da ke arewacin Lebanon waɗanda kuma aka tasa keyarsu zuwa Syria.
Rahotanni sun ce manyan jami'an Syria da waɗanda ke kusa da iyalan hamɓararren shugaban ƙasar Bashar al-Assad sun tsere zuwa Lebanon bayan hamɓarar da gwamnatin Assad a farkon wannan watan.
Mutum 13 sun mutu sakamakon wani hatsarin mota a jihar Ondo.
Hatsarin ya afku ne tsakanin wasu motocin bas biyu a daidai wata gada da ake kira Ose da ke kan babban hanyar Owo/Ikare-Akoko.
Ganau sun bayyana cewa haɗarin ya faru da misalin karfe 10 na safiyar yau Asabar, inda lamarin ya rutsa da mutum 14.
Mutum 13 daga cikinsu sun ƙone ƙurmus yayin da aka ceto wani guda da ya samu munanan raunuka.
Babban kwamandan hukumar kiyaye haɗura ta jihar Ondo, Samuel Ibitoye, ya tabbatar wa da gidan talbijin na Channels faruwar lamarin, inda ya ce tayan ɗaya daga cikin motocin ne ya fashe abin da ya janyo motar ta ƙwace wa direba har ta kai suka yi karo da wata motar bas, inda nan take suka kama da wuta.
Ya ce jami'ansu sun garzaya zuwa wajen da lamarin ya faru,inda suka mutumin da ya jikkata zuwa asibitin gwamnatin tarayya da ke Owo domin ba shi kulawa.
Ma'aikatar Lafiya a Gaza ta ce sojojin Isra'ila sun tsare tare da yin tambayoyi ga kusan ma'aikatan lafiya 100 da ke aiki a asibitin arewacin Gaza.
Ma'aikatar lafiyar - da ke ƙarƙashin ikon Hamas - ta ce har yanzu dakarun Isra'ila na tsare da daraktan asibitin na Kamal Adwan, Dakta Hussam Abu Safiya.
Wani jami'in Lafiya ya shaida wa BBC cewa an cuzguna wa ma'aikatan tare da cutar da hankulansu.
A yanzu haka asibtin ya zama kufai, bayan an lalata shi da hare-hare.
A ranar Juma'a ne Isra'ila ta bayyana shi da 'sansanin ƙungiyar ta'addanci ta Hamas' to sai dai ba ta gabatar da cikakkun hujjoji kan hakan ba.
Wata gobara da ta tashi a kasuwar Masaka da ke karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa, ta haddasa asarar rayukan mutum biyu, yayin da sama da 20 ke kwance a asibiti.
Wani ɗan kasuwa da lamarin ya shafa, mai suna Abdulkadir Sagir Ɗanbatta ya shaida wa BBC cewa gobarar wadda ta afku a jiya da daddare, ta kuma janyo asarar dukiya ta sama da biliyan ɗaya da rabi.
Sagir ya ce gobarar ta ƙona ɗaukacin kayayyaki a kasuwar.
"Mutane na ta jimami da ɗebe sauran kayayyakinsu da suka ƙone. Kusan rabin kasuwar ta ƙone ƙurmus," in ji shi.
Ya ce zuwa yanzu ba su san abin da ya janyo ɓarkewar gobarar ba.
Shugaban ƙasar Kenya, William Rutoya alƙawarta kawo ƙarshen ɗauke mutane da ake yi a ƙasar, bayan jerin ɓacewar matasan 'yan gwagwarmaya a Kenya.
Ɓacewar mutanen da ake samu a baya-bayan nan ta matasa ne da ke sukar shugaba Ruto a shafukan sada zumunta.
'Yansanda sun musanta hannu a ɓacewar matasan, wadda ta ƙaru tun bayan zanga-zangar adawa da gwamnati da aka gudanar cikin watan Yuli.
Ƙungiyoyin kare 'yancin ɗan'adam na zargin jami'an tsaron farin kaya da kame mutanen.
A ranar juma'a masu zanga-zanga suka tare tituna a garuruwan mutanen da aka sacen, inda suka yi kira ga shugaban ƙasar ya saki duka mutanen da ake tsare da su cikin kwana guda.
Ƙungiyar Tarayyar Turai ta fara amfani da wata sabuwar doka, da ta buƙaci mafi yawan na'urori masu amfani da wuta su kasance suna da wurin chaji na bai ɗaya.
Shekaru biyu da suka gabata ne masu tsara dokoki na ƙungiyar EU suka amince da amfani da wayar chaji ta 'type C' a matsayin wadda za a riƙa amfani da ita.
Masu tsara dokokin sun ce hakan zai rage yawan chajojin da suke lalacewa tare da rage kashe miliyoyin daloli wajen sayen chajojin.
Tun da farko kamfanin Apple - wanda ya fi kowane kamfani sayar da manyan wayoyin hannu - ya kasance babban mai adawa da matakin, to sai dai a shekarar da ta gabata ya miƙa kai.
Da safiyar yau Asabar ne kamfanin ya dakatar da sayar da tsoffin wayoyinsa a ƙasashe mambobin EU, da ba su fara amfani da dokar ba.
Masu ƙera kwamfutocin Laptop na da wa'adin zuwa 2026 domin yin biyayya ga sabuwar dokar.
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya nemi afuwar shugaban ƙasar Azerbaijan dangane da faɗuwar jirgin saman ƙasar, wanda ya bayyana da ''mummunan tsarin da ya faru a sararin samaniyar Rasha''.
An dai zargi Rasha da kakkaɓo jirgin saman, yayin da yake ƙoƙarin sauka a birnin Grozny na ƙasar a ranar Laraba.
Amma Mista Putin bai amince kai tsaye da hannun Rasha, kamar yadda rahotonni daga Kremlin suka ruwaito.
Shugaba Putin ya kuma ce a lokacin da jrgin ke yunƙurin sauka, jiragen marasa matuƙa na Ukraine sun ƙaddamar da hari kan garin na Grozny, inda ya ce a lokacin dakarun tsaron saman Rasha na ƙoƙarin daƙile hare-haren.
Masu garkuwa sun sace wani fitaccen malamin Addinin Musulunci mai matuƙar tasiri a arewacin Mali, yankin da masu iƙirarin jihadi ke yawan ƙaddamar da hare-hare.
Shaidu sun ce 'yanbindigar ɗauke da muggan makamai sun tare tawagar motocin Sheikh Amadou Hady Tall a wani ƙauye da ke kusa da kan iyakar ƙasar, yayin da yake komawa ƙasar daga wasu tarukan addinin da ya halarta a ƙasar Mauritaniya
Malami - wanda shi ne jagoran ɗariƙar Tijjaniya a ƙasar - na da ra'ayin sassauci saɓanin ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadin da ke yankin.
A lokacin da masu iƙirarin jihadin suka ƙwace wasu manyan yankunan arewacin ƙasar fiye da shekara 10 da suka gabata, sun riƙa lalata wuraren ibada da manyan ƙaburburan sufaye.
Kodayake daga baya an tilasta wa mayaƙan ficewa daga ybirane da garuruwan yankin, amma yankin ya ci gaba da fuskantar hare-hare, inda miliyoyin mutane suka rasa muhallansu.
Kocin Arsenal, Mikel Arteta ya ce ɗan wasan gaban ƙungiyar Bukayo Saka zai yi jinyar fiye da wata biyu bayan an yi masa aiki a cinyarsa.
An sauya ɗan wasan gefen mai shekara 23 a zagayen farko na wasan da ƙungiyarsa ta doke Crystal Palace da ci 5-1 a gasar Premier League ranar 21 ga watan Disamba.
Saka ya kasance ɗan wasa mai matuƙar muhimmanci ga ƙungiyar Arsenal, inda a kakar wasa ta bana ya zura ƙwallo tara sannan ya taimaka aka ci 13 a wasa 24 da ya buga a bana.
A baya kocin ƙungiyar ya ce ɗan wasan zai yi jinyar makonni, to amma a yanzu ce jinyar ka iya kai Saka fiye da wta biyu.
"Na yi ta cewa makonni masu yawa a baya, amma a yanzu ina tunanin zai kai fiye da wata biyu. Ban ma san haƙiƙanin lokacin da zai warke ba''.
Ma'aikatar tsaron Taliban da ke Afghanistan ta ce dakarunta sun ƙaddamar da abin da ta kira 'hare-haren ramuwar gayya'' zuwa cikin ƙasar Pakistan inda ta ce an shirya hare-haren da aka kai Afghanistan.
Wasu rahotonni daga yankin na cewa, an samu arangama a kan iyakar ƙasashen biyu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar dakarun Pakistan.
Kawo yanzu babu martani daga Pakistan, amma da alama an samun ƙarin tashin hankali a yankin.
Lamarin na zuwa ne kwana huɗu bayan Pakistan ta ƙaddamar da hare-hare ta sama a lardin Paktika na Afghanistan - wanda Kabul ta ce ya kashe mutum 46.
Pakistan ta ce ta kai harin ne kan maɓoyar mayaƙan da ke yi wa yankunanta barazana.
Gwamnatin tarayya ta alƙawarta gudanar da cikakken bincike kan harin da aka kai ƙauyukan Gidan Bisa da Rumtawa a ƙaramar hukumar Silame da ke jihar Sokoto.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa X, gwamnan jihar Ahmad Aliyu, ya ce ƙaramin ministan tsaron ƙasar, Bello Matawalle ne ya tabbatar da hakan a lokacin ziyarar jaje da ya kai jihar ranar Juma'a.
A ranar 25 gatan Disamba ne wani hari da jiragen sojin Najeriya suka ''kai wa Lakurawa'' ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 10 a ƙauyukan.
''Gwamnatin tarayya ta tabbatar mana cewa za ta gudanar da cikakken bincike domin gano abin da ya haddasa lamarin domin yi wa waɗanda lamarin ya shafa adalci'', kamar yadda gwamnan ya wallafa.
Tuni dai rundunar sojin ƙasar ta musanta hannu a kisan fararen hulan, inda ta ce bama-baman da Lakurawa suka ɓoye ne suka fashe bayan harin nasu, lamarin da ya yi nadiyyar mutuwar mutanen 10.
Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam'iyyar hamayya ta PDP, Sule Lamido ya zargi gwamnatin shugaban Najeriya, Bola Tinubu da ta Muhammadu Buhari da rashin gaya wa 'yan ƙasa haƙiƙa gaskiya game da gwamnatocinsu.
Cikin wata hira da BBC, toshon gwamnan na jihar Jigawa ya ce gwamnatocin biyu sun fifita farfaganda a maimakon faɗa wa 'yan ƙasa gaskiyar halin da ƙasar ke ciki.
Sule Lamido ya ce a shekarar da ta gabata gwamnatin Tinubu ta yi kasafin kuɗi na kusan Tiriliyan 30, kuma hukumomin tattara haraji na ƙasar sun ce sun tara naira tiriliyan 50, amma duk da haka gwamnatin Tinubu ta buƙaci cin bashin domin cike giɓi a kasafin kuɗin na shekarar da ta gabata.
''Ka yi kasafin kuɗinka da za ka kashe a duka shekarar a kan naira tiriliyan 30, sai kuma ka samu kuɗin shiga naira tiriliyan 50, kenan in za ka yi amfani da su kana da rarar naira tiriliyan 20, to bashin me kuma za ka ciyo''.?
Tsohon gwamnan na Jigawa ci gaba da cewa ''dama mulki ake yi na yaudara da rashin faɗar gaskiya, abin da yake akwai daban-dabna kuma da ake yi daban''.
Masu shigar da ƙara a Koriya ta Kudu sun ce a lokacin da shugaban ƙasar da aka dakatar, Yoon Suk Yeol, ya yi ƙoƙarin ƙaƙaba dokar soji - da ba da yi nasara ba a ƙasar - ya bai wa sojojin damar buɗe wuta, in ma da dama su shiga zauren majaisar dokokin ƙasar a lokacin .
Sun ce ya faɗa wa manyan jagororin sojin ƙasar sun ɓalele ƙofafofin ginin majalisar tare da fitar da 'yan majalisar daga cikin ginin.
Dubban masu zanga-zanga ne suka fabntsama kan tituan ƙasar, riƙe da ƙwalaye masu ɗauke da saƙonni daban-daban ciki har da masu buƙatar kama Mista Yoon, wanda majalisa ta tsige mako biyu da suka gabata.
Shirin Mahangar Zamani na BBC Hausa ya samu gagarumar nasara a shekarar 2024, ta hanyar samun miliyoyin masu kallon shirin - wanda ke matuƙar tasiri ga rayuwar al'umma.
Mahangar Zamani, shiri ne da BBC ta ɓullo da shi domin ilimantar da faɗakarwa kan abubuwan da ke ci wa al'umma tuwa a ƙwarya.
Shirin da ya fi samun masu kallo shi ne wanda muka yi kan 'amfani da magungunan ƙarin kuzari ga maza'. Bidiyon wannan shiri da muka fitar ranar 24 ga watan Agustan 2024 na wannan shekarar, ya samu masu kallo fiye da miliyan uku a shafunkanmu na sada zumunta.
Daga nan sai shirin da muka yi tare da fitacciyar jarumar Kannywood, da Nollywood, Rahma Sadau, wanda ya samu masu kallo fiye da miliyan biyu, bayan fitar da shi ranar 18 ga watan Mayun shekarar.
Donald Trump ya buƙaci kotun kolin Amurka ta dakatar da dokar da za ta haramta amfani da fitaccen dandalin sada zumunta na TikTok.
A baya dai an tsare cewa Amurka za ta haramta amfani da TikTok, idan har ƴan ƙasar Chinan da suka mallaki dandalin ba su saida wa wani kamfanin da Amurkawa suka mallaka ba.
Wa'adin sayar da dandalin dai zai ƙare ne kwana guda kafin Mista Trump ya hau kan karagar mulki a wata mai zuwa.
Donald Trump ya ce bai goyi bayan haramta TiKToK ba a halin yanzu, amma a wa'adinsa na farko ya nemi haramta dandalin wanda ya kira barazana ga tsaron Amurka.
Amurka ta ce ta ga alamun da ke nuni da cewa na'urorin tsaron saman Rasha ne suka harbo jirgin saman da ya yi hatsari a Kazakhstan a ranar Laraba .
Kakakin Fadar White House, John Kirby, ya ce Amurka ta yi tayin taimakawa wajen gudanar da bincike kan hatsarin, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum 38.
Da aka tambaye shi game da zargin, kakakin Kremlin Dmitry Peskov, ya ce Moscow ba ta da abin cewa game da hatsarin.
Ya ce ana gudanar da bincike kan wannan lamarin kuma a halin yanzu ba a kammala ba, don haka babu wani ƙarin bayani da za su bayar da kan hatsarin.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce sojojin Isra'ila sun lalata babbar cibiyar lafiya ta ƙarshe da ta rage a arewacin Gaza.
WHO ta ce rahotanni sun bayyana cewa an ƙona wasu muhimman sassa da aka lalata a harin da aka kai ranar Juma’a a asibitin Kamal Adwan.
Hukumar ta kuma nuna matuƙar damuwa game da lafiyar majinyatan da aka tilasta musu barin asibitin.
Isra'ila dai ta ce Hamas na amfani da asibitin ne a matsayin cibiyar ba da umarni - amma ba ta gabatar da wasu hujjojin da ke gaskanta hakan ba.