Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 28/11/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 28/11/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammad da Aisha Aliyu Jaafar da Ibrahim Yusuf Mohammed

  1. Hotunan shirye-shiryen yi wa Sheikh Ɗahiru Bauchi jana'iza, Jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi

  2. Ƴaƴan Shehi sun kai 90, jikoki sun fi 300 - Sheikh Bashir

    A tattaunawarsa da BBC, ɗaya daga cikin ƴaƴan Shehin malamin, Sheikh Bashir Dahiru Usman Bauchi ya ce a yanzu yawan ƴaƴan da malamin ya haifa sun kai kimanin 90, sannan yana da jikoki da suka zarce 300.

    Babban ɗa namiji na malamin shi ne Muhammad Bello, wanda ya rasu tun yana ƙarami, sai kuma mai bi masa, Dakta Hadi Dahiru Bauchi.

    Ya bayyana cewa akwai ƴaƴan malamin sama da 70 waɗanda suka haddace Alƙur'ani, kuma jikokinsa sama da 100 ne suka haddace Ƙur'anin.

    "Wasu daga cikin yarana sun haddace kur'ani tun suna shekara bakwai da haihuwa kuma tun ma kafin su iya rubutu a allo.'' in ji Sheikh Dahiru Bauchi.

    "Sai dai ban sani ba ko a cikin 'ya'yan nawa akwai wanda ya rubuta kur'ani saboda su kan fita ƙasashen waje domin neman karatu na sauran fannonin addini da ma boko.''

    "Yanzu ma akwai daktoci a cikin yaran," a cewar Shehun Malamin da bakinsa.

  3. EFCC ta gayyaci tsohon ministan sharia Abubakar Malami

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta gayyaci tsohon ministan shari'a a Najeriya Abubakar Malami, SAN, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

    Ya ce hukumar ta gayyace shi domin ya yi bayani a kan wasu abubuwa da bai bayyana ba, kuma ya bayar da tabbacin girmama gayyatar.

    " A matsayina na ɗan ƙasa mai bin doka da oda kuma mai kishin ƙasa, na kuduri aniyar girmama wannan gayyata. Na yi imani da muhimmancin gaskiya, riƙon amana da kuma rike gaskiya a harkokin mulki — waɗannan ƙa’idoji ne da na dade ina goyon baya tare da tsayawa a kai, a iya shekaru danayi a aikina na hidimar jama’a'' kamar yadda ya wallafa a shafinsa.

    Ya kuma shaida wa ƴan ƙasar zai ci gaba da sanar da su abin da zai biyo baya, a cewar sa 'domin kowa ya kasance da masaniyar me zai je ya koma saboda halin rayuwa na yau da gobe da kuma tarihi.''

  4. Wane ne Sheikh Ibrahim Saleh wanda zai jagoranci jana'izar Sheikh Ɗahiru Bauchi?, Jana'izar sheikh Ɗahiru Bauchi

    Ɗaya daga cikin ƴaƴan marigayi Sheikh Ɗahiru Bauchi, Naziru Ɗahiru Bauchi ya shaida wa BBC cewa mahaifin nasu ya bar wasiyya dangane da mutanen da za su yi masa sallah idan ya riga su rasuwa.

    ''Da ma ya yi wasiyya cewa Sheikh Shariff Ibrahim Saleh, wanda amininsa ne, shi ne zai yi masa sallah, idan kuma ba ya gari Sheikh Isma'il Khalifa ya yi masa sallah," a cewar Naziru.

    To amma kasancewar Sheikh Isma'il Khalifa ya riga ya rasu. Yanzu Sheikh Shariff Ibrahim Saleh ne zai jagoranci sallar jana'aizar da za a yi wa marigayin bayan sallar Juma'a a garin Bauchi.

  5. Yadda mahalarta jana'izar Sheikh Ɗahiru Bauchi ke ji rashin malamin, Jana'izar sheikh Ɗahiru Bauchi

    Mutane da dama daga jihohi daban-daban, da ma ƙasashen wajen sun isa jihar Bauchi domin nuna alhini da kuma halartar jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi da za a gudanar a yau Juma'a.

    Wasu daga cikinsu sun bayyana wa BBC yadda suka ji da wannan rashin.

  6. Ku San Malamanku tare da Sheikh Ɗahiru Bauchi

  7. Mutum 128 sun mutu a gobara mafi muni a Hong Kong

    Hukumar kashe gobara ta Hong Kong ta ce na'urorin da ke gargaɗin tashin gobara ba sa aiki yadda ya kamata a benayen da aka samu gobara mafi muni cikin gomman shekaru.

    Zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutum ɗari da ashirin da takwas.

    Shugaban sashen tsaro na ƙasar ya shaidawa manema labarai cewa na kawo ƙarshen ayyukan ceto, amma har yanzu ba a gano mutum aƙalla ɗari biyu ba.

    Gobarar dai ta laƙume wasu gine gine masu tsawo guda bakwai masu ɗauke da gidajen kwana na alumma a ranar Laraba.

    Har yanzu ana gudanar da bincike domin gano musabbabin gobarar wanda ake tunanin ya soma ne daga wasu kayyaykin gine gine da ke gefen ginin.

  8. Tarihin rayuwar Sheikh Ɗahiru Bauchi

    A wata tattaunawa da BBC ta yi da Sheikh Dahiru Bauchi a 2019 da kuma 2024 ya shaida cewa an haife shi a wani gari da ake kira Nafada da ke jihar Gombe, wanda garin mahaifiyarsa ce, "kasancewar a al'adar Fulani ana haihuwar ɗan fari ne a gidansu mahaifiyarsa," in ji shi.

    Ya kuma ce shi Bafulatani ne ta wurin uwa da uba. Dukkanin kakanninsa huɗu Fulani ne.

    "Sunan mahaifiyata Maryam 'yar Hardo Sulaiman. Sunan Mahaifina Alhaji Usman dan Alhaji Adam." in ji shi.

    Sheikh Dahiru ya haddace kur'ani a wurin mahaifinsa kafin daga bisani ya tura shi Bauchi domin neman tilawa.

    Mahaifinsa almajirin Shehu Ibrahim Nyass ne kuma mukaddami a cikin ɗarikar Tijjaniyya ta hanyar Amadu Futiy kafin Shehi Ibrahim Nyass ya bayyana.

    "Mahaifiyata ita ma ta je Kaulaha har sau biyu, kuma Shehu ya ƙaddamar da ita har ya ba ta carbi, saboda haka ni da mahaifina da mahaifiyata da 'ya'yana da jikokina duk gaba daya mun taru a cikin Shehu Ibrahim,"

    Ya yi auren fari a shekarar 1948 lokacin yana da shekara 20 "da wata daya."

  9. Wane ne Sheikh Ɗahiru Bauchi

    Shiekh Dahiru Usman Bauchi babban malamin addinin musulunci ne a ɗarikar Tijjaniyya da ake ji da shi a nahiyar Afirka, sannan malami ne wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga koyar da al'kur'ani, littafin Musulmi mafi girma.

    Shehun malamin na ɗaya daga cikin malamai a Najeriya da suke sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa addinin Musulunci hidima.

    An haife shi ne a ranar 28 ga watan Yunin 1927, dai-dai da 2 ga watan Muharram 1346, wato Shehin malamin ya rasu yana da shekaru 98 kalandar Turawa amma a ta Musulunci ya rasu yana shekara 100 da ƴan watanni kenan.

  10. Hamɓararren shugaban Guinea Bissau ya isa Senegal

    Hamɓararren shugaban ƙasar Guinea Bissau ya isa makwabciyar ƙasarsa, Senegal bayan wata yarjejeniya da kungiyar ECOWAS ta jagoranta.

    Wakilin BBC ya ce ma'aikatar harkokin wajen Senegal ta ce a ranar Alhamis da yamma wani jirgin sama na soji ya sauka a ƙasar da Mista Embalo a ciki.

    A shekaran jiya Laraba ne sojoji suka hamɓarar da Umaro Sissoco Embaló, da sauran jami'ai daga mulki - kwana ɗaya kafin bayyana sakamakon zaben shugaban ƙasar da aka yi.

    Da dama na ganin Mr Embaló ne zai yi nasara a zaben na kasar ta yammacin Afirka.

    An rantsar da shugaban rundunar sojin ƙasa ta ƙasar a matsayin shugaba na abin da sojojin suka kira gwamnatin rikon-ƙwarya.

  11. Yau za a yi jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi

    A yau Juma’a ne za a gudanar da jana’izar fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ya rasu, ranar Alhamis, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

    Sheikh Dahiru wanda jagora ne na darikar Tijjaniyya ya rasu yana da shekaru 98 a kalandar miladiyya, a kalandar Musulunci kuma yana da shekara 100 da ƴan watanni.

    Shehin malamin ya rasu ne a asibitin sojojin sama da ke jihar Bauchi bayan gajeriyar jinya.

  12. Trump zai dakatar da ƴan 'ƙasashe masu tasowa' shiga Amurka

    Shugaba Trump na Amurka ya ce zai dakatar da duk wasu masu komawa ƙasar daga abin da ya kira ƙasashe masu tasowa - dindindin.

    A wani dogon sako da ya sanya a shafinsa na sada zumunta, ya ce zai soke duk abin da ya kira, miliyoyin baƙin haure da Biden ya shigar ƙasar.

    Haka kuma ya ce zai daina bayar da duk wani tallafi na gwamnatin tarayya ga waɗanda ba ƴan Amurka ba, da kuma soke takardun zama ƴan kasa na baƙin da suka tayar da zaune tsaye a cikin ƙasar.

    Trump ya bayyana hakan ne bayan da aka sanar da cewa daya daga cikin sojojin gwamnatin tarayyar nan biyu da aka harba shekaran jiya Laraba a Washington ta rasu.

    Ɗan bindigan da ake zargi da harbin ɗan ƙasar Afghanistan ne.

  13. Buɗewa

    Masu bibiyar shafin BBC hausa na kai-tsaye, barkanku da safiyar yau Juma'atu babbar rana.

    A yau ma shafin namu zai mayar da hankali ne kan kawo muku irin wainar da ake toyawa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance tare da mu.

    Za kuma ku iya leƙawa shafukan mu na sada zumunta kamar Facebook, Instagram, youtube da kuma X, inda muke wallafa muku bidiyo.