Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. 07/11/2024

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Abdullahi Bello da Isiyaku Muhammed

  1. 'Ya kamata Trump ya ba Ukraine damar kai wa Rasha hari'

    Tsohuwar ambasadar Amurka a Nato ta ce tana fata Donald Trump zai "ba Ukraine damar kai wa Rasha hari a ƙarshen iyakar ƙasar" domin kawo ƙarshen yaƙin.

    Da take yi wa BBC ƙarin bayani, Kay Hutchinson, ta ce gwamnatin Ukraine ta yi ƙoƙarin shiga yarjejeniya da Amurka da zai amfane ta.

    A baya Trump ya soki yanayin yadda Amurka ke kashe kuɗaɗe a game da Ukraine a ƙarƙashin mulkin Joe Biden, kuma ana masa kallon ba zai goyi bayan Rasha ba. .

    Hutchinson ta ce Trump zai yi ƙoƙarin tabbatar da kasuwanci da China.

  2. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Alhamis, daga nan sashen Hausa na BBC inda za mu riƙa kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa daga Najeriya da sassan duniya.

    Za kuma ku iya leƙawa shafukanmu na sadarwa domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.