Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 24 ga watan Maris 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Farashin man fetur ya sake haura dala 100 kan kowanne ganga

    Farashin ɗanyen man fetur samfurin Brent ya sake haura sama da dala 100 kan kowanne ganga, bayan ya yi ƙasa sosai a ranar Litinin.

    A kasuwannin Asiya da safiyar Talata, farashin fetur ya ƙaru da kashi 3.75 zuwa dala 103.69.

    A ranar Litinin ne dai farashin man ya faɗi da fiye da kashi 10 bayan da Donald Trump ya ɗage shirin kai hare-hare kan tashoshin lantarkin Iran bayan ya ce ya tattauna da Iran lamarin da Iran din ta musanta.

    Dalilin haka ne masu zuba jari suke sake duba wannan lamari.

  2. Muna nazari kan buƙatar tattaunawa da Amurka - Iran

    Wani babban jami’i a ma’aikatar harkokin wajen Iran ya tabbatar cewa Iran ta samu bayanai daga Amurka ta hannun masu shiga tsakani, kuma a yanzu haka ana nazarin su, a matsayin wata hanya da za ta iya kai ga fara tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu.

    CBS ta bayyana cewa wannan mataki na iya zama kawai shiri ko share fage kafin fara tattaunawa kuma har yanzu ba a tabbatar da cewa an fara tattaunawar ko ana gudanar da ita ba.

    Wannan na zuwa ne bayan da shugaban Amurka, Donald Trump ya ce an gudanar da tattaunawa tsakanin Amurka da Iran kan kawo ƙarshen rikicin, sai dai kakakin majalisar dokokin Iran ya musanta hakan.

    Trump ya kuma sake jaddada cewa Amurka na da damar cimma yarjejeniya don dakatar da rikicin, bayan ya sassauta barazanar kai hari kan wuraren makamashin Iran tare da dage shirin kai harin.

  3. Yadda Amurka da Iran ke musayar bayanai masu karo da juna kan tattaunawa

    Jami'an Amurka da na Iran na bayar da bayanai masu karo da juna kan yiwuwar tattaunawa tsakanin kasashen biyu kan yakin da ake yi.

    Shugaba Donald Trump ya ce ya ɗage barazanarsa ta kai hare-hare kan tashoshin wutar lantarkin Iran bayan abin da ya kira "tattaunawa mai ma'ana da Tehran."

    Sai dai kakakin majalisar dokokin Iran ya musanta cewa an gudanar da tattaunawar, yana mai danganta iƙirarin Trump da "labarin ƙarya."

    Masu sharhi dai sun ce ayyukan Trump a ƴan kwanakin da suka gabata sun kasance masu karo da juna musamman ta fuskar diflomasiyya da kuma ƙoƙarin karkatar da hankali.

    Tun a ranar Litinin shugaba Donald Trump ya ce ya yi tattaunawa mai ma'ana da jami'an Iran, matakin da gwamnatin Tehran ta ce Trump ya yi hakan ne domin yaudara don farfado da darajar kasuwar makamashi, musamman kafin cikar wa'adinsa na bude mashigar Hormuz ko kuma ya tarwatsa babbar tashar lantarkinta.

    Matakin na Trump ya sa farashin danyen mai ya sauka kafin daga bisani kuma ya kara tashi bayan Iran ta karyata cewa ta tattauna da Amurka.

  4. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Aisha Babangida ce za ta sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.