Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/05/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 29/05/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Usman Minjibir, Aisha Babangida da Badamasi Abdulkadir Mukhtar

  1. MDD ta nemi Isra'ila ta ba da damar shigar da ƙarin kayan abinci a Gaza

    Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga Isra'ila ta ba da damar shigar da karin kayan agaji zuwa Gaza, bayan da dubban mutane suka kutsa cikin rumbun hukumar da ke tsakiyar Zirin.

    An bayyana cewa an harbe mutane biyu, kana aka take ƙarin wasu biyu da mota yayin balahirar.

    Hotunan bidiyo sun nuna mutane ɗauke da jakunkuna da kwalaye suna ficewa daga rumbun.

    A wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, jakadan Isra'ila a MDD ya zargi majalisar da cin dunduniyar kasarsa, ta hanyar bin hanyoyin da suka saɓawa ƙasarsa wajen rabon kayan jin kai a Gaza.

  2. Kotu ta taka wa Trump birki kan harajin da ya lafta wa ƙasashe

    Kasuwar hannayen jari ta yi sama a Asiya, bayan wata kotun tarayya a Amurka ta yanke hukuncin cewa shugaba Trump ya tsallake makaɗi da rawa wajen lafta haraji ga ƙasashen duniya.

    Lamarin dai ya zama wata babbar illa ga wani muhimmin ɓangare na manufofinsa na tattalin arziki.

    Kotun ta cinikayya ta ƙasashe duniya ta ce fadar White House ba ta da hurumin sanya harajin kasuwanci, kuma majalisa ce kaɗai ke da ikon daidaita harkokin kasuwanci da sauran kasashe.

    Kotun ta bai wa fadar White House kwanaki goma, ta cire dukkan harajin da ta laftawa ƙasashe da dama na duniya, da ta ce an sanya su ba bisa ƙa'ida ba.

    A cikin 'yan mintoci da yanke hukuncin, gwamnatin Trump ta ɗaukaka kara.

    Wani kakakin fadar White House ya ce ba aikin alƙalai bane yanke shawarar yadda za a magance matsalar gaggawa da ta shafi ci gaban kasa.