Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 01/09/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida

  1. SERAP ta soki ƙarin kuɗin yin fasfo a Najeriya

    Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta SERAP ta buƙaci shugaba Bola Tinubu ya soke sabon ƙarin kuɗin yin fasfo da hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS) ta sanar, tana mai cewa hakan ya saɓawa doka kuma cin zarafin haƙƙin ɗan ƙasa ne.

    Wannan na ƙunshe ne a wata cikin wata wasiƙa mai ɗauke da ranar 30 ga Agusta, 2025, wacce mataimakin daraktan ƙungiyar, Kolawole Oluwadare, ya sanya wa hannu.

    NIS ta bayyana cewa daga 1 ga Satumbar 2025, kuɗin yin fasfo mai shafi 32 na shekara biyar zai zama naira 100,000 yayin da na shafi 64 na shekaru goma kuma zai kai naira 200,000

    SERAP ta ce wannan ƙarin zai hana talakawa da mutane marasa galihu damar yin fasfo zai kuma ƙara wahalar tattalin arziki da ake ciki.

    Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa za ta kai ƙara kotu idan gwamnati ta ƙi soke wannan mataki cikin kwanaki bakwai.

  2. 'Girgizar ƙasa ta kashe fiye da mutum 600 a Afghanistan'

    Ma’aikatar cikin gida ta Taliban ta bayyana cewa adadin waɗanda suka mutu a girgizar ƙasar da ta auku a gabashin Afghanistan ya kai mutum 610, inda aka ƙara samun mutuwar mutane 12 a Nangarhar, wanda ya sa jimillar mutuwar ta kai 622.

    Haka kuma, ma'aikatar ta ce sama da mutum 1,500 ne suka jikkata.

    Shugaban asibitin lardin Asadabad, babban birnin Kunar, Dr Muladad, ya ce suna karɓar “marasa lafiya daga girgizar ƙasar guda ɗaya a kowane minti biyar” kuma asibitin ya cika da waɗanda suka jikkata.

    A cewarsa, mutum 188 da suka jikkata – ciki har da mata da yara – aka kawo asibitin a cikin awanni kaɗan da suka gabata.

    Sai dai har yanzu ana samun sabbin bayanai kuma akwai yuwuwar adadin mutuwa zai ƙaru saboda nisan yankin da abin ya shafa da kuma wahalar da ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa ke fuskanta wajen isa wurin.

    Girgizar ƙasar ta faru ne da dare, lokacin da mutane suke cikin gidajensu suna barci, kuma ana fargabar akwai mutane da dama da suka maƙale ƙarƙashin rufin gine-gine.

  3. Takarar Tinubu da Shettima dabara ce ta siyasa ba ta addini ba - El-Rufa'i

    Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce Gwamnan Kaduna, Uba Sani bai abokinsa ba ne, kawai yaronsa ne na siyasa, sannan ya ƙara da cewa ya goyi bayan tikitin Musulmi-Musulmi ne domin lissafin siyasan da neman nasara ba domin addini ba.

    El-Rufai ya bayyana haka ne a zantawarsa da tashar Channels, inda ya ce, "lissafin neman nasarar zaɓe ne kawai takarar Musulmi-Musulmi, ba wai lissafin siyasa ba ne. Idan za ka shiga zaɓe, dole ka lissafa ka ga hanyoyoyin da za ka samu nasara. Kuma wannan ba shi da alaƙa da addini," in ji shi.

    Ya ce duk da cewa tikitin Musulmi da Musulmi ne babu wani abu da Kirista za su ce ana tauye musu, "na yi a Kadua. Ina so a nuna min wani kirista na Kaduna da aka tauye wa haƙƙi."

    A game da alaƙarsa da gwamnan mai ci, ya ce yanzu ba sa magana "saboda duk wajen da na bari bayan na gama aikina, ba na komawa sai dai idan an neme ni."

    "Ba ɓatawa muka yi da gwamnan ba, dama ba abokina ba ne. Yarona ne a siyasa, wanda na ɗaura a hanya. Don haka ba wai ɓatawa muka yi ba," in ji shi, sannan ya ƙara da tabbatar da cewa yanzu ba ya magana da gwamnan na yanzu.

    Tsohon ministan na Abuja ya ce yana alfahari da zama silar ɗaukakar mutane da dama, "wasu ma sun wuce matakin da na taka. Ina jin daɗi da alfahari da haka."

    Sai dai ya ƙara da cewa taimakon mutum ya samu nasara ba zai hana shi sukarsa, "idan mutum ya kauce hanya, ya daina yin abin da ya dace, shin don na taimaka wajen samun nasararsa, sai ya zama dole ba zan yi magana ba? haka ƙasar ta koma a yanzu?"

  4. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin daga nan sashen Hausa na BBC, inda a yau ma za mu ci gaba da kawo muku labaran abubuwan da suka faru a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Ku kasance tare da mu.