Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 01/09/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida

  1. Rufewa

    Masu bin shafin namu na kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku abbin labarai.

    Amma kafin nan, muke cewa mu kwana lafiya

  2. Hatsarin jirgin ƙasa ya kashe mutum uku a Masar, Hafsa Khalil

    Ministan lafiyar Masar ya ce mutum uku sun mutu, yayin da 103 suka jikkata sakamakon hatsarin jirgin ƙasa a Alƙahira, babban birnin ƙasar.

    Jirgin ya taso ne daga birnin Marsa Matruh da ke gaɓar ruwa a lokacin da taragonsa bakwai suka kauce hanya tare da faɗuwa a ƙarshen mako.

    Ministan Lafiyar ƙasar, Dakta Khaled Abdul Ghaffar ya jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu, tare da yin addu'ar fatan samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata.

    Ma'aitakar sufurin ƙasar, tare da haɗin gwiwar ma'aikatar sufurin jiragen ƙasa ta ƙasar, na bincike kan abin da ya haddasa hatsarin.

    Hatsarin jragen ƙasa a Masar na yawan faruwa, sakamakon rashin kula da hanyoyinsu.

    A shekarar 2002, wani mummunan hasarin jirgin ƙasa ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 370 bayan da gobara ta kama wani jirgin ƙasa da ke tafiya a kudancin birnin Alƙahira.

  3. ƴangudun hijira sun yi zanga-zanga kan rashin tsaro a Sokoto

    Wasu yan gudun hijira a karamar hukumar shagari da ke jihar Sokoto, sun gudanar da zanga zanga domin nuna adawa da matsalar tsaro da ta addabe su.

    Aƙalla mazauna ƙauyuka kimanin 10 ne suka yi zanga-zangar a kan titin Jere zuwa Sokoto, kan abin da suka kira watsi da gwamnatin jihar ta yi.

    Masu zanga zangar sun koka kan yadda ƴanbindiga su ka tilasta musu barin garuruwansu, inda suka buƙaci a kawo musu ɗauki.

    Rahotonni sun ce mata da masu shayarwa na daga cikin wadanda suka gudanar da zanga-zangar.

    Shugaban ƙaramra hukumar ta Shagari, Alhaji Maidawa ya shaida wa BBC cewa suna sane da masu zaman gudun hijirar, kuma gwamnati na iya baƙin ƙoƙarinta don ganin sun koma garuruwansu.

    ''Gwamnati ta ɗauki matakin zuwa yankunansu domin samar da tsaro don su koma garuruwansu'', in ji shi.

    Ya kuma zargi ƴan hamayya da kitsa zanga-zangar ƴangudun hijirar.

    A jihar Kebbi ma da ke makwaftaka da Sokoto, alummomin wasu ƙauyuka sun koka kan yadda mayaƙan Lakurawa ke korarsu daga garuruwansu tare da aza musu haraji kan dabbobin su.

  4. Rasha na da hannu a kisan fitaccen ɗan siyasarmu - Ukraine

    Jami’an Ukraine sun ce mutumin da ake zargi da kisan wani fitaccen ɗan siyasar Ukraine a ranar Asabar ɗin da ta gabata, ya aikata hakan ne tare da haɗin gwiwa da Rasha.

    An harbe Andriy Parubiy har lahira a birnin Lviv da ke yammacin ƙasar.

    Rahotanni sun ce wanda ake zargi ya tuntuɓi Rasha domin neman bahasi a kan ɗansa soja da ya ɓata a bakin daga.

    A baya, Andriy Parubiy ya taɓa riƙe muƙamin kakakin majalisar dokokin Ukraine, sannan ya yi fice a fafutikar kusantar da ƙasar ga ƙasashen yamma.

  5. Ƙungiyar ƴanjarida ta duniya ta yi zanga-zangar adawa da kisan ƴan'uwansu a Gaza

    Gamayyar Ƙungiyar ƴan Jaridu da ake kira Reporters Withou Borders, ta ce sama da ƴanjarida 250 daga sama da ƙasashe 70, sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da kisan wasu ƴan-uwansu ƴanjarida a Gaza.

    Zanga-zangar ta haɗar da wasu daga cikin jaridun da suka sanya baƙin Pentin a farkon shafin jaridunsu da suka wallafa, yayinda na Internet su ma suka bi sahu wajen yin hakan a shafukan nasu.

    Kungiyar ta kuma yi ƙiyasin cewa dakarun Isra'ila sun halaka ƴanjarida 220 a yaƙin da suke a Gaza a cikin kasa da wata uku.

  6. Girgizar ƙasar Afghanistan: Fiye da mutum 800 sun mutu

    Mutanen da suka mutu a girgizar ƙasar Afghanistan ya zarta 800, yayain da kusan 3,000 suka jikkata.

    Hukumar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce girgizar ƙasar mai ƙarfin maki 6.0 ta auka wa gabashin ƙasar da tsakar daren ranar Lahadi.

    Jami'ai sun ce an samu mafi yawan mace-macen a lardin Kunar, inda suka yi gargaɗin cewa za a iya samun ƙaruwar alƙaluman mace-macen, yayin da ƙauyuka da dama suka ruguje.

    Yankin ƙasar mai cike da tsaunuka ne lamarin ya fi ƙamari, wani abu da ya sa aikin ceton ke da matuƙar wahala.

    Bala'in na zuwa ne a daidai lokacin da Afghanistan ke fama da matsanancin fari, da yankewar agaji da abin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana da mummunar yunwa.

  7. Abin da ya sa na sauke kwamishinonina - Bago

    Gwamnan jihar Neja Umar Mohammed Bago ya ce ya rushe kwamishinoninsa ne domin auna ƙoƙarin gwamnatinsa a rabin wa'adi.

    A yau Litinin ne gwamnan ya sauke duka kwamishinoninsa bayan zaman majalisar zartaswar jihar da ya guda a fadar gwamnatinsa.

    To sai dai yayin tattaunawarsa da manema labarai, gwamnan ya ce akwai yiwuwar sake mayar da wasu cikin kwmaishinonin a wasu ma'aikatun na daban domin sake gwada sa'arsu.

    Gwamnan ya ce gwamnati tana da faɗi don haka wasu za su sake komawa wasu fannonin.

    “Wasu za su sake dawowa, yayin da wasu za su koma wasu ma'aikatun domin samun sabon tsari'', in ji shi.

    “Sun yi iya bakin ƙoƙarinsu: Wasu sun yi zarra, yayin da wasu suka yi ƙoƙarin a fannoninsu'', in ji shi.

    Gwamnan ya kuma gode wa kwamishinonin nasa kan taimakon da suka bayar wajen ciyar da gwamnatinsa gaba.

  8. An kama mutum biyu kan zargin safarar muggan makamai daga Jigawa zuwa Katsina

    Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da kama wasu mutum biyu bisa zargin safarar muggan makamai daga jihar Jigawa zuwa Katsina.

    Cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida na jihar, Nasir Mu'azu ya fitar ya ce da asubahin yau ne ƴansandan da ke sintiri tsakanin Ingawa da Karkarku suka kama wata mota ƙirar Golf maƙare da muggan makamai.

    "An kuma kama wasu mutum biyu, mazauna ƙauyen ɓaure da ke ƙaramar hukumar Safana tare da makaman'', in ji sanarwar.

    Nasir Mu'azu ya ce binciken ƴansanda ya gano cewa motar ta taso ne daga garin Hadejia da ke jihar Jigawa da nufin zuwa Safana a jihar Katsina.

    Makaman da aka kama cikin motar sun haɗa da:

    • Babbar bindiga mai jigida (GPMG)
    • Alburusan bindigar AK-47 1,063
    • Alburusan bindigar PKT 232.
  9. 'Arewa maso yamma ce kan gaba a more wa ayyukan gwamnatin tarayya'

    A Najeriya, gwamnati ƙasar ta ce shiyyar arewa maso yammacin ƙasar ce ke da kaso mafi yawa na kuɗaɗen da aka ware wa manyan ayyukan gwamnatin tarayya, inda aka amince wa shiyyar kusan naira triliyan 6, kwatankwacin kashi 40 na duka kuɗaɗen da aka ware don gudanar da ayukka.

    Martanin na zuwa ne bayan rahoton da wata jaridar ƙasar ta wallafa da ke cewa kuɗaɗen da aka amince domin yin ayyuka a jihar Legas da ke kudu maso yamma kaɗai, ya fi waɗanda jihohi 18 da ke kudu maso gabashi da arewa maso yammaci da kuma arewa maso gabashin ƙasar suka samu cikin shekara biyu.

    Sai dai a martanin da ta mayar, gwamnatin ƙasar ta fitar da jadawalin shiyoyin da kuɗaden da aka amince musu da kuma ayyukan da za a yi da kuɗaɗen wanda ya sha bamban da rahoton gidan jaridar.

    Minstan yaɗa labaran ƙasar, Muhammad Idris, ya shaida wa BBC cewa arewa maso yamma ne ke da kashi 40 cikin ɗari na ayyukan da gwamnatin tarayya ta samu da ya kai naira tiriliyan 5.9, sai yankin arewa ta tsakiya da ya samu naira tiriliyan 1.1 tsakiya.

    Ministan ya kuma ce jihar Legas ta samu naira tiriliyan 1.2.

    Sai dai ya ce abin da ya sa na jihar Legas ya fi na wasu yankuna yawa, shi ne saboda yadda jihar ke da manyan gadoji da kuma manyan tasoshin jiragen ruwa da batun filin jirgi.

    ''Sauran kuɗin kuma wasu manyan ayyuka ne da suka haɗa da yankin kudu maso yammacin ƙasar da aiki ya shafi jihar Legas'', in ministan.

  10. Mutane na guduwa daga birnin Gaza saboda hare-haren Isra'ila

    A daidai lokacin da dakarun Isra’ila ke ci gaba da matsawa cikin birnin Gaza, mazauna yankin sun ce an tura tsaffin motocin sulke cike da abubuwan fashewa zuwa wasu sassan yankin Sheikh Radwan, sannan aka harba musu su daga nesa.

    Wakiliyar BBC ta ce bidiyon da aka wallafa a intanet sun nuna karin Falasdinawa na tserewa daga birnin Gaza a motoci da kekuna da taraktoci.

    A baya-bayan nan ne Isra’ila ta watsa takardun gargadin da ke cewa jama’a su gaggauta tserewa zuwa Kuduncin Gaza.

    Ma’aikatar lafiya da Hamas ke gudanarwa ta ce akalla mutum 98 aka kashe, a hare-haren Isra’ila a fadin Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata.

  11. Mutum shida ne suka mutu a zanga-zangar Indonesia

    Masu zanga-zanga a Indonesia sun ƙara ƙaimi wajen fafutikar da suke yi, inda suke ta cinna wuta a ofishoshin gwamnati, da faɗa wa gidajen ƴan siyasa, ciki har da ginin majalisar birnin Bandun.

    Sauran wasu yankunan ma an samu artabun da ’yan sanda a ci gaba da jerin zanga-zangar adawa da gwamnati da ake yi a ƙasar.

    Aƙalla mutum shida ne suka mutu, a abin da shugaban Indonesia ya bayyana a matsayin hari da kuma barazana ga dimokuradiyya.

    Prabowo Subianto ya yi kokarin rage fushin masu zanga-zangar ta hanyar yanke wasu alawus-alawus da damarmaki da ake bai wa ’yan majalisar dokokin Indonesia, sai dai da dama daga cikin masu zanga-zangar na neman sauye-sauye a fannoni da dama na ƙasar.

  12. Shugaban Ghana ya sauke babbar mai shari'ar ƙasar

    Shugaban ƙasar Ghana, John Mahama has ya sauke babban alƙaliyar alƙalan ƙasar, Mai Shari'a Gertrude Torkornoo.

    Matakin na zuwa ne bayan shawarar kwamistin bincike kan ƙorafe-ƙorafen da wani ɗan ƙasar mai suna Daniel Ofori ya shiga kan Misis Torkornoo.

    John Mahama ya ce matakin sauke Misis Torkornoo ya fara aiki nan take.

  13. Amnesty ta buƙaci a bincika ƙone wata mata a Neja bisa zargin ɓatanci ga Annabi

    Ƙungiyar Amnesty International ta yi kira da a gudanar da bincike cikin gaggawa kan kisan gilla da ta ce an yi wa wata mai sayar da abinci a ƙaramar hukumar Mariga da ke jihar Neja bisa zarginta da ɓatanci.

    Rundunar ƴansandan jihar ta tabbatar da cewa matar mai suna Amaye, mazauna yankin ne suka ƙone ta ƙurmus a jiya Lahadi a ƙauyen Kasuwar Garba.

    Ƙungiyar ta kare haƙƙin ɗan'adam ta ce akwai buƙatar hukumomin Najeriya su tabbatar da kama waɗanda suka ƙone ta,tare da tabbatar da suna fuskanci hukunci ba tare da ɓata lokaci ba.

    Amnesty ta ce ɗaukar doka a hannu na cikin manyan ƙalubalen da ke barazana ga ƴancin rayuwa a Najeriya, "saboda yadda irin wannan kashe-kashe ke maimaituwa, kuma kaɗan ne kawai aka bincike tare da yanke hukunci na nuna sakacin hukumomi wajen gaza cika alƙawarin su na kare rayuwa da dukiyar al'umma daga cutarwa."

  14. Gwamnatin Najeriya ta yi maraba da ɗaure Simon Ekpa a Finland

    Gwamnatin Najeriya ta yaba da hukuncin da kotun lardin Päijät-Häme da ke ƙasar Finland ta yanke a ranar Litinin, inda ta yanke wa mai fafutikar kafa ƙasar Biyafara Simon Ekpa hukuncin zaman gidan kaso na shekara shida bisa samunsa da laifin ta'addanci.

    A wata sanarwa da ministan watsa labarai Mohammed Idris ya fitar, ya ce suna maraba da hukuncin, kuma suna jinjina wa ƙasar ta Finland.

    "Hukuncin ya zo a daidai, domin zai zama adalci ga ɗimbin ƴan Najeriya da suka rasa rayukansu da waɗanda suka shiga tashin hankalin a sanaiyar bala'in da su Ekpa suka jefa su," kamar yadda sanarwar ta bayyana, inda ministan ya ƙara da cewa wannan hukuncin zai ƙara ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin Najeriya da Finland.

    Sanarwar ta ce Ekpa ya yi shekaru yana tunzura jama'a suna aikata laifuka, wanda ke "ruguza rayuwar iyalai da karya kasuwancin su da mayar da yara marayu da jefa garuruwa da dama cikin fargaba, da ma zama silar mutuwar ɗaruruwan mutane da sunan fafutikar da ke barazana ga haɗin kan Najeriya da ƴancinta."

    Ya ƙara da cewa a shirye gwamnatin Tinubu take ta tsayawa da ƙarfinta wajen kare ƴancin ƙasar da mutuncin ƴan ƙasar baki ɗaya ta hanyar "amfani da diflomasiyyar ƙasa da ƙasa da jami'an tsaro da ɓangaren shari'a domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin ƙasar."

  15. Shugaban MDD ya nemi a saki ma’aikatansu 11 da aka kama a Yemen

    Shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya nemi a saki ma'aikatan Majalisar 11 da hukumomin Houthi suka kama a Yemen nan take ba tare da sharaɗi ba.

    An kama ma’aikatan ne a yayin wata samame da jami'ai suka kai a ofisoshin shirin abinci na duniya WFP, da UNICEF da kuma hukumar lafiya ta duniya WHO, a cewar jaridu da Majalisar Ɗinkin Duniya.

    Wannan ya faru ne a birnin Sanaa da Hudaydah, in ji Jakadan Musamman na MDD a Yemen, Hans Grundberg.

    Grundberg ya ce Houthi suna riƙe da wasu ma’aikata 23 tun a 2021, yayin da kuma hukumomin ba su ce komai ba kan wannan sabon kamar.

    A wata sanarwa, Guterres ya ce ya yi Allah-wadai da kama ma’aikatan MDD 11 ba bisa ƙa’ida ba tare da karɓe ofisoshin WFP da sauran wuraren MDD da Ƙwace kayayyaki.

    Ba a fayyace dalilin da ya sa Houthi suka kai hari kan ma’aikatan MDD ɗin ba.

  16. Aƙalla mutum 70 sun mutu bayan jirgin ƴan gudun hijira ya kife a tekun Afrika ta Yamma

    Gwamnatin Gambiya ta tabbatar da wani mummunan haɗarin jirgin ruwa da ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 70 bayan wani jirgin da ke ɗauke da ‘yan gudun hijira ya kife a gaɓar tekun Afirka ta Yamma.

    Ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta bayyana hakan ne a ranar Juma’a da daddare, tana mai cewa wannan shi ne ɗaya daga cikin manyan asarar rayuka a ‘yan shekarun nan a sanannen hanyar ƙaura zuwa Turai.

    Rahotanni sun ce jirgin yana ɗauke da kusan mutum 150 lokacin da ya kife, inda hukumomin Mauritaniya suka tabbatar da gano gawarwaki 70, tare da ceto mutum 16 kawai daga cikin ruwa.

    Shaidun gani da ido sun ce adadin mutanen da suka mutu na iya haura 100.

    A wani lamari makamancin wannan wanda gwamnatin Gambiya da kamfanin dillancin labarai na Reuters suka rawaito ya nuna cewa wani jirgi ruwa da ake zaton ya tashi daga Gambiya ya nutse a gaɓar Mauritaniya makon da ya gabata, inda ake tsoron aƙalla mutum 30 ne suka mutu.

    Yawancin fasinjojin jirgin sun fito ne daga Gambiya da Senegal.

    Hanyar tekun Atlantic daga Yammacin Afirka zuwa Tsibiran Canary na Spain na ɗaya daga cikin hanya mafi haɗari ga ‘yan gudun hijira.

    A bara kaɗai, sama da mutum 46,000 ne suka yi gudun hijira ta wannan hanyar wanda ya kafa tarihin mafi yawa sai dai an ƙiyasta sama da mutum 10,000 sun mutu yayin ƙoƙarin ketarewa ta wannan hanyar.

  17. An kama wani mutum da hannu a kisan tsohon kakakin majalisa a Lviv ta Ukraine

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya ce an kama wani da ake zargi bayan kisan da aka yi wa wani fitaccen dan siyasa a kasar a ranar Asabar.

    Andriy Parubiy, wanda tsohon kakakin majalisar dokokin ƙasar ne, ya taka muhimmiyar rawa a zanga zangar data kawo ƙarshen gwamnatin da ke goyon bayan Rasha a 2014.

    An harbe shi ne a birnin Lviv da ke yammacin ƙasar.

    Jami'an Ukraine sun ce an gabatar da shaidar farko akan mutumin da ake zargi da harbin dan siyasar.

    Sun ce tsara kisan aka yi saboda sai da aka yi nazarin duk wani motsin mutumin da aka kashen.

  18. Atiku ya nemi a soke sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin Rivers

    Tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya a zaɓen 2023, Atiku Abubakar ya yi kira da a soke sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a jihar Rivers inda ya bayyana zaɓen a matsayin "abin kunya da cin fuskar tsarin dimokraɗiyya".

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Atiku ya fitar a shafinsa na X ranar Lahadi.

    Atiku ya ce "Yadda aka gudanar da zaɓen ya nuna cewa jam’iyyar APC tana shirin keta doka don samun nasara ta siyasa."

    "Ina jawo hankalin ‘yan Najeriya da ƙungiyoyin duniya da abokan hulɗa kan yadda gwamnatin Tinubu ke ƙoƙarin karkatar da Najeriya zuwa turba mai haɗari," in ji shi

    Atiku ya buƙaci duk jam’iyyun adawa a jihar Rivers su ƙi amincewa da sakamakon zaɓen, saboda "gwamnatin ba ta da hurumin gudanar da zaɓen."

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Rivers (RSIEC) ta ce sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin jihar da aka gudanar ranar Asabar ɗin da ta gabata ya nuna cewa jam’iyyar APC ta lashe ƙananan hukumomi 20 daga cikin 23 yayin da PDP ta samu sauran guda uku.

  19. UNICEF ta ce a shirye take don bayar da agaji bayan girgizar ƙasar Afghanistan

    UNICEF ta bayyana cewa tana da ƙungiyoyi a ƙasa waɗanda ke shirye domin rarraba agaji bayan girgizar ƙasar da ta auku a Afghanistan.

    Hukumar UNICEF, wacce ke kula da yara, ta ce ƙungiyoyinta na gida suna aiki tare da hukumomin ƙasa domin samun cikakken bayani kan wuraren da abin ya fi shafa.

    Har yanzu ba a iya samun damar shiga hanya ta ƙasa zuwa wuraren da girgizar ƙasa ta fi shafa amma akwai yiwuwar ɗarurruwan gidaje sun lalace, in ji Salam Al Janabi daga ofishin UNICEF na Kabul.

    Manyan abubuwan da hukumar ke mai da hankali a kai sun haɗa da lafiya da kare yara da samar da ruwa da tabbatar da tsaftar muhalli.

  20. An yanke wa ɗan Najeriya Simon Ekpa hukuncin ɗaurin shekara 6 a Finland

    Kotu a ƙasar Finland ta yanke wa ɗan Najeriya mai 'rajin ɓallewar ƙasar Biyafara', Simon Ekpa hukuncin ɗaurin shekaru shida a gidan yari bisa laifukan ta’addanci.

    Kotun ta same shi da laifin ƙoƙarin harzuƙa jama'a da niyyar ta’addanci da kuma shiga cikin ayyukan ƙungiyar ta’addanci.

    Kotun ta kuma same shi da laifukan zamba ta haraji da kuma karya doka wanda hakan ya sanya kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara shida a gidan yari.

    Kotun ta bayyana cewa Ekpa ya yi ƙoƙarin ƙarfafa rajin ɓallewar yankin Biyafara a kudancin Najeriya ta haramtacciyar hanya tsakanin watan Agustan 2021 zuwa Nuwamban 2024.

    Kotun ta ce ya yi amfani da kafafen sada zumunta domin samun shigewa gaba-gaba a wannan fafutika.

    Ƙungiyar ƴan-awaren ta kuma samar da wasu ƙungiyoyi masu ɗaukar makami, waɗanda kotun ta bayyana a matsayin na ta’addanci.

    A cewar hukuncin, Ekpa ne ya samar wa waɗannan ƙungiyoyin makamai da abubuwa masu fashewa da harsasai ta hanyar wasu mutanensa.

    Haka kuma, an same shi da laifin amfani da kafafen sada zumuntarsa wajen ingiza mabiyansa su aikata laifuka a Najeriya.

    Kotun ta ce ya dikata duk wadannan laifuka ne ya yin da yake zama a garin Lahti na ƙasar ta Finland, sai dai ya musanta zarge-zargen.

    Hukuncin da kotun ta yanke ba shi ba ne na ƙarshe, wanda ake zargin zai iya ɗauka ƙara zuwa kotu ta gaba.