Sadio Mané ne farke wa Senegal ƙwallo, yayin da suka tashi 1-1 da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ranar Asabar, lamarin da ya sa suka ci gaba da zama a saman rukunin na huɗu a wasannin Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) da ake bugawa a Morocco.
Cedric Bakambu ne ya fara ci wa Kongo a minti na 61, amma Mané ya farke bayan mintuna takwas tsakani, kuma da na 51 da ya zura a raga a tarihin bugawa kasarsa tamaula, inda Senegal ke daga cikin manyan tawagogin da ake ganin za su iya lashe gasar da ake yi a Morocco.
Kasashen biyu suna da maki hudu daga wasanninsu bibiyu a cikin rukuni, kuma alamu na nuna za su kai zagaye na biyu cikin ruwan sanyi, bayan da kowaccensu ke da wasa na ƙarshe a rukunin da za ta buga ranar Talata.
Senegal na gaban DR Kongo a jadawalin rukuni ne saboda yawan cin kwallaye, bayan da suka doke Botswana da ci 3-0 a wasansu na farko ranar Litinin, yayin da DR Kongo ta yi nasara a kan Benin da ci 1-0 a dai ranar