Abin da kuke son sani kan wasan Ingila da Argentina a gasar kofin duniya, Gasar kofin duniya
Ingila na fatan kaiwa wasan ƙarshe a Kofin Duniya karon farko cikin kusan shekara 60, yayin da za ta kara da Argentina mai rike da kofin a zagayen daf da ƙarshe ranar Laraba.
Bayan rashin sa'a a shekarar 1990 da kuma 2018, Ingila ta sake tsintar kanta a mataki daf da karshe a Gasar Kofin Duniya karo na biyu a tarihinta.
Ingila ta fara gasar Kofin Duniya ta 2026 da ƙwazo, inda ta doke Croatia da ci 4-2 a wasan farko a rukuni na 10.
Daga baya ta tashi babu ci da Ghana, kafin ta tabbatar da matsayinta na ta ɗaya a rukuni, bayan doke Panama da ci 2-0.
A zagayen na biyu kuwa, tawagar da Thomas Tuchel ke jan ragama ta nuna jajircewa sosai bayan da aka zujra mata ƙwallo daga baya ta farke ta kara ta kuma doke Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.
A zagayen tawaga 16 kuma, duk da rage mata mutum ɗaya, ta yi nasarar fitar da ɗaya daga cikin ƙasashen da suka karɓi bakuncin gasar, wato Mexico.
Haka zalika a wasan kwata fainal, Ingila ta sake nuna ƙarfin hali, inda ta farke ƙwallon da aka fara zura mata a raga sannan ta kara na biyu ta yi waje da Norway da cin 2-1.
Da wannan ƙoƙarin, Ingila na fatan kai wa zagayen ƙarshe a gasar kofin duniya karon farko tun bayan 1966.
To sai dai kuma za ta fuskanci ƙalubale a hannun Argentina mai riƙe da kofin, inda wannan karawar ta hamayya ce mai cike da tarihi a gasar cin kofin duniya.
Ko Messi zai yi bajinta kan Ingila fiye da Maradona?
Lionel Messi ya fara wannan gasa ta Cin Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026 cikin ƙayatarwa tare da karya tarihi a karo da dama, yayin da Argentina ta fara kare kambunta da doke Aljeriya 3-0.
Messi ne ya zura ƙwallaye uku rigis a wasan, wanda ya sa ya kai matsayin wanda ya fi kowa yawan cin kwallaye a tarihin Gasar Cin Kofin Duniya.
Daga baya ya zama shi kaɗai ke riƙe da wannan tarihi bayan da ya sake zura ƙwallo a wasan da Argentina ta doke Austria da Jordan.
Haka kuma ya ci ƙwallo a fafatawar zagayen gaba, inda Argentina ta samu nasarar 3-2 a kan Cafe Verde a zagayen na biyu da fitar da Masar da cin 3-2 a zagayen tawaga 16.
Tawagar ta Argentina da Lionel Scaloni ke jan ragama ta fuskanci ƙalubale a hannun Switzerland, inda sai da ta kai ga ƙarin lokaci da aka tashi a mintuna 120 domin kai wa wasan kusa da ƙarshe.
Julian Alvarez da Lautaro Martinez suka zura ƙwallaye a raga a ƙarin lokaci, lamarin da ya tabbatar da nasarar 3-1 a wasan zagayen kwata fainal.
Duk da cewa Messi, wanda shi ne mafi yawan zura ƙwallaye a tarihin Gasar Kofin Duniya, ya ci gaba da kasancewa ginshikin kai hare-hare a Argentina, nasarar da tawagar ke yi ta samo asali ne daga ƙoƙarin da ƴan wasan ke sawa gaba ɗaya.
Wasu ƴan wasa bakwai suna daga cikin waɗanda suka ci wa Argentina ƙwallaye, yayin da wasu takwas suka bayar da ƙwallayen aka zura a raga.
A ɓangaren tsaron baya kuwa, haɗin gwiwa tsakanin Cristian Romero da Lisandro Martinez ta sa golan Argentina na samun natsuwa.
Ingila na fatan hana Argentina lashe kofin karo na biyu a jere
Ingila ta kai wasan daf da ƙarshe karo na biyu a gasar Kofin Duniya uku da suka gabata.
A shekarar 2018 a Rasha, ta sha kashi da ci 2-1 a hannun Croatia.
Kafin nan a shekarar 1990 a Italiya, ta rasa damar kaiwa wasan ƙarshe bayan da ta sha kashi a bugun fenariti a hannun Jamus ta Yamma.
Karo na ƙarshe da Ingila ta kai wannan mataki kuma ta tsallake zuwa wasan ƙarshe shi ne shekaru 60 da suka gabata, lokacin da ta lashe kofin da ta gudanar da gasar a ƙasarta.
Kaftin ɗin tawagar Ingila Hary Kane na cikin masu takarar ƙyautar takalmin zinare, mai shida a raga, iri ɗaya da yawan wanda Jude Bellinghm ya ci.
Sai dai Kuma Messi da Mbappe ne kan gaba a bana da kowanne ya zura takwas a raga da kuma Erling Haaland mai bakwai, yayin da aka yi waje da ƙasarsa Norway.
Marcus Rashford shi ne kaɗai sauran ɗan wasan Ingila da ya ci ƙwallo a gasar zuwa yanzu, yayin da Anthony Gordon da Bukayo Saka suka bayar da ƙwallon da aka zura a raga.
A gefe guda kuma, Argentina mai kofin duniya sau uku jimilla na neman zama ƙasa ta farko da za ta kare kambunta tun bayan Brazil a shekarar 1962.
Wannan ne karo na shida da Argentina ke kaiwa wasan dab da ƙarshe.
Abin mamaki shi ne cewa a duk lokuta biyar da ta kai wannan mataki a baya, ta kan tsallake zuwa wasan ƙarshe ba tare da rashi nasara ba.
Lionel Messi ya kasance babban jigo a nasarorin Argentina a baya-bayan nan.
A wasan dab da ƙarshe a 2014, shi ne ya fara cin fanaritin da Argentina ta yi nasara a kan Netherlands.
Haka kuma a 2022, Messi ne ya buɗe cin ƙwallo daga bugun fanariti a nasarar 3-0 da Argentina ta samu a kan Croatia.
Tarihin Haɗuwar Ingila da Argentina a Gasar Kofin Duniya
Ingila da Argentina sun haɗu sau biyar a tarihin Gasar Cin Kofin Duniya kafin wannan wasan na 2026, inda Ingila ta yi nasara uku, yayin da Argentina ta ci wasa biyu, idan aka kirga nasarar da ta samu a bugun fanariti a 1998.
Chile 1962
Haɗuwarsu ta farko a Kofin Duniya ta zo ne a matakin rukuni. Ingila ta yi nasara da ci 3-1, inda ta fara doke Argentina a karon farkon a tarihin wannan wasan hamayya.
Ingila 1966
Shekaru huɗu bayan haka, sun sake haɗuwa a wasan kwata-fainal. Ingila ta yi nasara da ci 1-0, kuma daga baya ta ci gaba da kwazon da ta lashe kofin duniya karo na farko kuma tilo a tarihinta kawo yanzu.
Mexico 1986
Wannan shi ne wasan da ya fi shahara a tarihin hamayyar tsakanin ƙasashen biyu. Diego Maradona ya jagoranci Argentina ta doke Ingila da ci 2-1, inda ya ci kwallaye biyu da suka shiga tarihi.
Ta farko ita ce wadda ya ci da hannu da ake kira da "Hand of God", sannan ya zura abin da ake kira "Goal of the Century" bayan da ya yanke kusan rabin ƴan wasan Ingila kafin ya zura ƙwallo a raga.
Faransa 1998
A zagayen ƴan 16, ƙasashen biyu sun buga ɗaya daga cikin wasannin da suka fi kayatarwa a tarihin Kofin Duniya.
Matashi, Michael Owen ya ci ƙwallo mai ƙyaun gani, amma wasan ya ƙare 2-2. Daga baya David Beckham ya samu jan kati bayan saɓani tsakaninsa da Diego Simeone.
Argentina ta yi nasara a bugun fanareti, saboda Paul Ince da David Batty sun kasa cin bugun fenariti.
Koriya da Japan 2002
Sun sake haɗuwa a matakin rukuni. A wannan karon, David Beckham ya rama takaicin abin da ya faru a haduwarsa a 1998 ta hanyar cin bugun fanariti wanda ya zama ƙwallo da aka zura a raga a wasan, kenan Ingila ta yi nasara da ci 1-0.
Wannan sakamakon ya taimaka mata wajen fitar da Argentina daga matakin rukuni karo na farko cikin shekara 40, yayin da Ingila ta kai kwata-fainal kafin Brazil ta fitar da ita daga gasar.
Muhimman Kididdiga
- Jimillar haduwar Kofin Duniya: Biyar.
- Nasarorin Ingila: Uku.
- Nasarorin Argentina: Ɗaya
- Mafi shahararren ɗan wasa a wannan hamayya: Diego Maradona
- Wasan 1998 na daga cikin mafi armashi a tarihin Kofin Duniya.
Ƴan wasan da ake sa ran za a fara karawar da su
Ƴan wasan Ingila 11 da ake sa ran za a fara wasan da su:
Pickford; James, Konsa, Guehi, O'Reilly; Anderson, Rice; Saka, Bellingham, Gordon; Kane
Ƴan ƙwallon Argentina da za a fara karawar da su:
Emi Martinez; Molina, Romero, Lisandro Martinez, Tagliafico; De Paul, Paredes, Mac Allister, Fernandez; Messi, Alvarez
Filin wasa na Atlanta da za a buga karawar
Kafin a buga wannan babban wasan tsakanin Ingila da Argentina, filin wasa na Atlanta ya riga ya zama ɗaya daga cikin wuraren da suka fi ɗaukar hankali a Gasar Kofin Duniya a 2026.
Wannan filin yana da tsayin sama da ƙafa 300, tare da rufin da ake iya buɗewa da rufe shi, da kuma babban allon bidiyo mai zagayawa digiri 360.
Haka kuma ana yaba wa filin a matsayin ɗaya daga cikin mafi kula da kare muhalli a duniya.
Wannan ne wasa na takwas kuma na ƙarshe da filin Atlanta zai karɓi bukunci a gasar.
A cikin wasannin da suka fi ɗaukar hankali a filin sun haɗa da karawar da Cape Verde ta tashi ba ci da Sifaniya da wanda Morocco ta doke Haiti 4-2 da kuma nasarar da Congo DR ta yi a kan Uzbekistan.
Abin sha'awa shi ne Ingila da Argentina sun buga wasa a wannan filin a wannan gasa , kuma kowacce ta yi nasarar karawar da ta yi.
Ingila ta doke Congo DR da ci 2-1 a zagayen ƴan 32, yayin da Argentina ta yi nasara a kan Masar da ci 3-2 a zagayen ƴan 16.
Atlanta United mai buga gasar ƙwallon kafar Amurka, MLS da kuma Atlanta Falcons ta NFL ne ke amfani da wannan filin a matsayin gida.
Tun bayan buɗe shi a shekara ta 2017, an buga manyan wasannin Amurka da suka haɗa da MLS All-Star Game da College Football Playoff National Championship da Super Bowl LIII da kuma FIFA Club World Cup.

