Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 13/11/2025.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail, A'isha Aliyu Jaafar, Muhammad Annur

  1. 'Yan hamayya sun kwarmata saƙonnin da suka shafi alaƙar Trump da Epstein

    'Yansiyasar Amurka na jam'iyyar Democrat mai adawa sun fitar da wasu sakonnin imel da suka ce suna da alaka da masaniyar Shugaban Ƙasa Donald Trump kan laifin cin zarafi ta hanyar lalata da Jefferey Epstein ya aikata.

    Ɗaya daga cikin sakonnin da Epstein ya aika ya ce shugaban ya san 'yanmatan, amma ba a yi cikakken bayani a kai ba.

    Fadar gwamnatin Amurka ta zargi 'yan Democrat da yunƙurin ɓullo da bayanan ƙarya.

    Mista Trump ya sha nanata cewa bai aikata komai ba kuma ba shi da wata alaƙa da Epstein.

  2. Gwamnatin Najeriya ta dakatar da fara karɓar harajin man fetur

    Hukumar kula da harkokin man fetur a Najeriya ta ce ta dakatar da shirin fara karɓar harajin kashi 15 cikin 100 kan albarkatun man fetur ɗin da ake shigarwa ƙasar daga ƙasashen waje.

    Mai magana da yawun hukumar Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA), George Ene-Ita, ya faɗa cikin wata sanarwa a ranar Alhamis cewa ya kamata 'yan Najeriya su daina fargaba.

    A ranar 29 ga watan Oktoba ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da saka harajin kan man fetur da dizel, wanda zai ƙara farashin man da ake saukewa a defo-defo, kuma ɗaya daga cikin manufarta shi ne ƙarfafa matatun mai na cikin gida.

    Gwamnatin Najeriya ta tsara fara aiki da harajin daga ranar 21 ga watan Nuwamban nan, kafin matakin da NMDPRA ta sanar.

    Duk da manufar ƙarfafa matatun mai na cikin gida da harajin zai yi, zai kuma iya jawo hauhawar farashin a gidajen mai kasancewar har yanzu Najeriya na shigar da fetur mai yawa daga ƙasashen waje.

  3. Gwamnatin Trump ta samu kasafin kuɗi bayan kwana 43

    Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan wani kudirin doka da zai kawo karshen kwana 43 da aka shafe ana dakatar da ayyukan gwamnati a kasar bayan da majalisar wakilai ta amince da shi.

    Shugaba Trump ya ce "da sanya hannuna yanzu gwamnatin tarayyar za ta koma aiki kamar a baya, sannan kuma gwamnati ma za ta ci gaba da ayyukan da take".

    Da yake maraba da matakin, Mista Trump ya soki 'yan jam'iyyar Democrats sannan kuma ya ce ba za a ƙara dakatar da ayyukan gwamnati ba a kasar.

    'Yan jam'iyyar ta Democrats sun ki amincewa a bude ayyukan gwamnatin har sai shugaba Trump ya amince da karin kudaden tallafin inshorar lafiya. Dakatar da ayyukan gwamnati dai ya janyo an ki biyan dubban ma'aikatan gwamnati albashi.

  4. Barka

    Barkanmu da hantsin Alhamis, barka da shigowa shafin labarai kai-tsaye.

    Za mu karaɗa sassan duniya domin kawo rahotonni kan abubuwan da ke faruwa.