Rufewa
Masu bin shafin BBC Hausa nan muka kawo ƙarshen wannan shafi namu na yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 13/11/2025.
Umar Mikail, A'isha Aliyu Jaafar, Muhammad Annur
Masu bin shafin BBC Hausa nan muka kawo ƙarshen wannan shafi namu na yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu
China ta buƙaci Firaministar Japan, Sanae Takaichi da ta janye kalamanta na baya-bayan nan akan Taiwan ko ta fuskanci maratani daga gare ta.
A makon da ya gabata dai ne Mis Takaichi ta shaidawa 'yan majalisar dokokin kasar cewa harin China akan Taiwan na iya haifar da martanin soji daga Japan.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen China Lin Jian ya ce kalaman Firaministar Japan akan China ba su yi wa China dadi ba.
China dai ta ce hakan zai iya lalata dangantakar diflomasiyya tsakaninsu.
Tun da jimawa dai China ke son yin amfani da ƙarfi domin ƙwace iko da yankin Taiwan da ta daɗe tana ikirarin mallakinta ne.
Isra'ila ta ce ta karɓi ƙarin gawa ɗaya na mutanen da aka yi garkuwa da su daga Gaza.
A yanzu za a soma gudanar da bincike domin gano ko gawar wane ne.
Idan binciken kimiyya ya tabbatar da gawar, zai kasance saura gawarwaki uku kenan da suka rage a dawo da su Isra'ila a matakin farko na yarjejeniyar tsagaita wuta.
Wannan ce gawa ta farko da aka miƙa wa Isra'ila a wannan makon.
Akwai hasashen cewa sauran gawarwakin mutanen da aka yi garkuwa da su za su yi wahalar gano wa.
Mazauna birnin Legas da ke kudancin Najeriya na kokawa kan tsadar dafaffen abinci da ake siyarwa a shaguna da kuma gefen titunan jihar.
A baya bayan nan ne masu sayar da abincin suka kara farashin farantin shinkafa da tuwo da nama da sauransu daga N300 zuwa N500 sai kuma na N800 zuwa N1,200.
Duk da sauƙin farashin da aka samu na kayayyakin cimaka kamar shinkafa da gero da dawa da masara da sauransu, idan aka zo ga dafaffen abinci ana samun tazarar mai yawa.
To sai dai masu siyar da abinci sun kare kansu inda suke cewa duk da faɗuwar farashin ɗanyen abinci to amma kayan miya da man gyada da biyan kuɗin haya da haraje-haraje na tilasta musu ƙara farashin abincin.
An buƙaci ofisoshin jakadancin Amurka da su duba yiwuwar hana yan ƙasashen waje masu ƙiba fiye da ƙima ko wani rashin lafiya mai tsanani biza na tsawon lokaci.
A wani saƙo da ya aikewa ofisoshin jakadancin Amurka da ke faɗin duniya, Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya ce wajibi ne a yi la'akari da lafiyar mutum, saboda wasu rashin lafiyar na buƙatar dubban ɗaruruwan daloli domin kula da marasa lafiyar.
Fadar gwamnatin Amurkar ta ce tun a baya ma'aikatar harkokin wajen ƙasar na da wani tsari na kin bayar da biza ga mutunen da ake ganin za su iya zama nauyi ga hukumomi idan suka je ƙasar.
A karo na biyu an sake zargin BBC da gyara wani ɓangare na jawabin shugaban Amurka Donald ranar da aka yi zanga-zanga a majalisar dokokin ƙasar da nufin karkatar da hankalin jama'a.
Wannan sabon zargin ya shafi shirin labaran dare na BBC mai suna Newsnight da aka gabatar a shekarar 2022, shekaru biyu kenan kafin zargin da aka yi a kan shirin Panorama, wanda ya yi sanadiyyar ajiye aikin babban daraktan BBC a wannan makon.
Tuni dai BBC ta nemi afuwa a kan kuskuren da aka yi game da shirin na Panorama.
Sai dai lauyoyin shugaba Trump na ci gaba da yin barazanar shigar da BBC ƙara tare da neman diyyar dala biliyan daya sakamakon zargin ɓata masa suna.
Mai magana da yawun BBC ya ce suna ci gaba da nazari a kan sabon lamarin.
Ministan babban birnin Najeriya Abuja, Nyesom Wike ya musanta raɗe-raɗin cewa ya na da wata matsala da sojoji, inda ya ce ya daɗe ya na taimaka wa sojoji tun ya na gwamna.
Ministan ya yi bayanin ne bayan wata sa-in-sa da ya yi da wani jami'in soji a yayin da shi da ma'aikatansa su ka je duba wasu filaye da ya ce an mallaka ba bisa ƙai'da ba, a birnin Abuja, ranar Talata.
A cewar sa "babu wani gwamnan da zai ce ya bai wa sojoji goyon baya kamar ni".
A hirar da ya yi da manema labarai a yau alhamis, Ministan ya kuma koka kan yadda ake cin zarafin ma'aikata idan an tura su duba irin waɗannan filayen da ake zargin an mallaka ba bisa ƙa'ida ba.
A cewar sa, babu yadda za a yi ya zauna shiru a matsayinsa na Minista alhali ana kai wa ma'aikatan gwamnati hari, ''Ana dukan manyan jami'an gwamnati da suka kai matsayin darakta, ta ya za a yi su yi aikinsu bayan sun san ni ina can zaune a Office ba zan iya kare su ba'' in ji shi.
Wike ya kuma bayar da misalin yadda wasu manyan sojoji da suka yi ritaya kamar tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo, suka samu matsalar fili, kuma su ka kira shi ya warware musu matsalar ba tare da sun tura sojoji su yi barazana ba.
Sai dai ya ce bai kamata wani ɗan ƙasa, da ya san ya yi ba daidai ba, saboda ya na da alaka da sojoji, ya hana gwamnati yin aikinta.
Ƴansanda a Sifaniya sun ce sun ruguza wani gungun masu aikata laifuka tsakanin ƙasa da ƙasa da ake zargi da safarar ƙananan yara daga tsibirin Canary zuwa Faransa, tare da kama mutane 11.
A wata sanarwa da suka fitar, ƴan sandan sun ce an tsare mutum huɗu daga cikin waɗanda ake zargi kan laifin da ke da alaƙa da kitsa laifuka, da samar da takardun bogi da kuma tattara hotunan batsa na yara.
An soma binciken ne bayan ɓacewar wasu yara 14 daga wasu cibiyoyin gwamnati a tibirin Canary tsakanin ƙarshen 2024 zuwa tsakiyar 2025.
Masu binciken sun ce ƙungiyar na amfani da hanyoyi da mutane a Morocco da Ivory Coast da Sipaniya domin safarar yaran, tare da samar musu da takarun bogi domin kai su Faransa.
Majalisar wakilan Najeriya ta yi kira ga gwamnatin ƙasar ta dakatar da shirin da hukumar shirya jarrabawar kammala sakadire ta WAEC ke yi na soma amfani da kwamfuta a jarrabawar shekarar 2026, inda ta yi gargaɗin za a iya samun dalibai da dama da za su yi rashin nasara.
Hakan ya biyo wani kuduri da ɗan majalisa Kelechi Nworgu ya gabatar, inda ya buƙaci majalisar ta shiga tsakani kan abin da ya ce zai iya zama barazana ga fannin ilimi.
Ya ce duk da dai ana amfani da kwamfuta a jarrabawar JAMB, halin da akasarin makarantun sakandire ke ciki a faɗin kasar ya sa ya ke ganin sauyawa zuwa kwamfuta a jarrabawar 2026 ya yi wuri.
''Da yawa daga cikin makarantu dubu 25,500 da ke ƙasar, musamman na karkara, ba su da naurorin kwamfuta da ke aiki, ko ƙwarrarun malaman koyar da ilimin ƙwanfuta. Da dama daga cikinsu ma ba su taɓa yin amfani da kwamfuta ba, gashi kuma ana ƙoƙarin tilasta musu zana jarrabawar da kwamfuta, in ji shi.
Dan majalisar ya bukaci ma'aikatar ilimi da hukumar shirya jarrabawar ta WAEC su ɗage fara amfani da kwamfuta na tsawon shekaru uku, kafin nan an ɗauki matakan da su ka dace tare da samar da kayayyakin aiki.
Rahotanni daga Eritrea na cewa an harbo wani jirgi mara matuƙi na ƙasar Habasha a yankin kudu masu gabashin ƙasar kusa da tashar jirgin ruwa ta Assab.
Hakan na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da zaman tankiya tsakanin ƙasashen biyu da ke makwaftaka da juna sakamakon kokarin Habasha na yin iko da tekun Maliya.
Rahotanni sun bayyana cewa jirgi mara matukin na aikin tattara bayanai ne a kusa da birnin Bure, wurin da yaƙin da aka yi kan iyaka a 1998 zuwa 2000 ya fi ƙamari, kuma ya kai ga mutuwar mutane fiye da dubu ɗari.
Akwai kuma rahotannin cewa Eritrea ta sanya wasu ma'urorin da ke hana jirage marasa matuka yin aiki tun a farkon wannan shekarar a muhimman wurare.
Zuwa yanzu gwamnatocin ƙasashen ba su ce uffan ba.
A Faransa, ana ci gaba da gudanar da bukukuwan tunawa da wani harin da masu ikirarin jihadi suka kai a birnin Paris shekaru goma da suka gabata.
Harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 130 tare da jikkata ɗaruruwa.
Shugaban Faransar Emannuel Macron ne ya jagoranci bukin jimamin.
An kuma ajiye furannin girmamawa a harabar wuraren sayar da abinci da mashaya da harabar babban filin kwallon kafa na Tade de France inda nan ma an kai wani harin ƙunar bakin wake.
"Shekaru shekaru 10 da suka gabata ma iya cewa 'yan ta'addar ba su yi nasara ba, amma shekaru 10 kenan da Faransa ke cikin alhini, kuma duk da haka ba mu karaya ba," in ji Magajin garin birnin Saint-Denis, Matiyu Hanotin, da ya yi jawabi a wurin.
Gwamnatin Sojin Sudan ta ce ta daƙile wani harin da mayakan RSF suka kai mata da jirage marasa matuƙa a garin Merowe da ke Arewacin ƙasar.
Rundunar sojin ta ce an yi ƙokarin kai harin ne akan hedikwatar tsaron ƙasar da filin jirgin sama da kuma wata madatsar ruwa.
Shaidun gani da ido sun ce sun ji fashe-fashe masu ƙarfi a daren Laraba a nisan kimanin kilomita 300 daga Arewacin birnin Khartoum.
Dakarun RSF da a yanzu suka amince da yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ke jagoranta har na tsawon watanni uku, na ci gaba da amfani da jirage marasa matuka daidai lokacin da yaƙi tsakaninsu da sojojin Sudan ke ƙara ƙamari.
Ƙaramin ministan tsaro na Najeriya, Bello Matawalle ya ce babu buƙatar yin sa-in-sar da aka samu tsakanin ministan Abuja, Nyesom Wike da sojan ruwa, AM Yerima.
A wata hira da kafar DCL, Matawalle ya ce ya kamata a magance matsalar da ta haifar da cece-kucen ta hanyar tattaunawa maimakon yin sa-insa a bainar jama'a.
Mr Wike dai ya umarci sojoji da ke gadin wani fili su kauce domin bari shi da jami'ansa su shiga filin, amma jami'an sojin a ƙarƙashin jagorancin wani matashin hafsan sojin ruwa suka jajirce cewa umarni aka ba su kuma ba za su bari a yi akasin umarnin da suke aiki a kai ba.
Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki ya buƙaci jam'iyyar PDP da ta ɗage babban taronta da ta shirya yi tsakanin ranakun 15 da 16 ga watan nan na Nuwamba, a birnin Ibadan na jihar Oyo.
Ya ce ci gaba da shirin gudanar da taron duk da irin wasiƙun dakatarwa da kotuna suka bayar zai ƙara ta'azzara rikicin jam'iyyar sannan ya jefa ta cikin matsaloli a nan gaba.
Bukola Saraki ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, bayan karɓar baƙuncin ƴan kwamitin amintattun jam'iyyar ƙarƙashin shugabancin Ambasada Hassan Adamu, a gidansa.
Tawagar dai ta ziyarci Bukolan ne domin neman tabarrukinsa da shawarwari kan yadda za a cimma haɗin kai a jam'iyyar da ta samu rarrabuwar kai.
Gwamnan jihar California ya caccaki Amurka kan munanan hare-haren da kasar ke kai wa kan jiragen ruwa da take zargin ana fataucin miyagun ƙwayoyi a yankin Caribbean.
Da yake magana a taron Sauyin yanayi na COP30 a Brazil, Mr Newsom ya ce abin takaici ne ganin yadda Amurka take kai hari kan jiragen ruwa ba tare amincewar majalisa ba.
Amurka yanzu ta kai hari kan jiragen ruwa 19, tare da kashe mutum 80. A ranar Talata ne wani babban jirgin ruwan yakin Amurka ya isa yankin.
Shugaban Colombia Gustavo Petro ya ce ya bayar da umarnin dakatar da musayar bayanan sirri tsakanin kasarsa da Amurka, yayin da Amurka ke ci gaba da luguden wuta
Shugaba Trump ya sake nanata aniyarsa ta maka BBC a kotu a kan wani shiri game da abubuwan da suka faru na tarzomar ginin majalisa a 2021.
Mista Trump kenan ke cewa ya kamata ya yi hakan tare da zargin BBC da yaudarar jama'a.
Tun da farko ya yi barazanar shigar da BBC kara tare da neman diyyar dala biliyan daya.
Tuni babban daraktan BBC da kuma shugabar kula da bangaren labaran BBC suka yi murabus.
Sun dai yi murabus ɗin ne bayan tabbatar da sauya wasu bangarori biyu na jawabin Mr Trump, wanda hakan ke nuna ya karfafa tarzomar ta ranar 6 ga Janairu
Rundunar sojan Najeriya ta ce ta yi nasarar ceto wasu matasa masu yi wa ƙasa hidima 74 a jihar Borno daga yunƙurin yin garkuwa da su.
Mai magana da yawun rundunar Operation Hadin Kai, Sani Uba, ya ce sun ceto mutanen a kan titin Buratai–Kamuya da misalin ƙarfe 9:05 na dare ranar Talata bayan motar da suke ciki ta lalace.
"Bayan dakaru sun isa wurin sun tarar da 'yan hidimar ƙasa...Nan take suka kwashe su domin kauce wa yin garkuwa da su daga mayaƙan Boko Haram ko Iswap da ke karakaina a yankin," a cewar sanarwar.
'Yan hidimar ƙasar da lamarin ya ritsa da su sun ƙunshi maza 36 da mata 38, a cewar rundunar.
Gwamnatin Kenya ta ce akwai yiwuwar 'yan ƙasarta kusan 200 sun shiga rundunar sojin Rasha domin taya ta yaƙi a Ukraine.
Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta ce wasu daga cikinsu tsofaffin sojan Kenya ne. Ofishin jakadancin Kenya a birnin Moscow ya ce akwai wasu da suka ji raunuka da waɗanda suka maƙale a Rasha bayan sun kasa samun gurbi a rundunar sojan.
Ma'aikatar ta kuma ce akwai wakilai na bogi da ke yi wa mutane alƙawuran samun dubban daloli ba tare da sun bayyana nau'in aikin da za a yi ba.
Rundunar 'yansandan Kenya ma ta ce akwai wasu da yawa da suka koma gida da raunuka a jikinsu, ko kuma cikin kiɗimewa.
A watan Satumba ne jami'an tsaro suka bankaɗo da wani gida da ake tara mutanen da ke shirin tafiya Rasha.
Rundunar sojan Mali ta ce ta kashe wani babban kwamandan ƙungiyar Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) mai alaƙa da al-Qaeda a ƙauyen Soumpi da ke arewacin birnin Timbuktu.
Shafin jaridar Les Echos Medias ya ruwaito cewa kisan Abou Salam Oumarou babbar nasara ce ga sojojin Mali amma ba ta bayar da ƙarin bayani kan lokacin da aka kashe shi ba.
"Yayin da ƙasashen waje suka saka ladan dala miliyan 18 a kan sa, sojojinmu ne suka yi nasarar kashe shi a Soumpi ba tare da samun wani lada ba," a cewar rahoton.
A ranar 7 ga watan Nuwamba ƙungiyar ta yi iƙirarin kashe sojoji 48 da kuma raunata wasu 100 yayin wasu hare-hare da ta kai kan sansanonin soji a garin.
Rahoton kisan na zuwa ne a daidai lokacin da Mali ke ci gaba da lalubo hanyoyin magance matsalar fetur da mayaƙan suka jefa ta sakamakon toshe hanyoyin sufurin kayayyaki da suka yi.
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki ya shawarci jam'iyyarsu ta PDP mai adawa ta dakatar da shirin gudanar da babban taronta na ƙasa a jihar Oyo saboda umarnin kotuna kan hakan.
Saraki ya bayar da shawarar cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na dandalin X ranar Laraba bayan wata ganawa da kwamatin sasanta 'ya'yan jam'iyyar ƙarƙashin jagoracin Hassan Adamu.
Tsohon shugaban da ya jagoranci majalisa daga 2015 zuwa 2019 ya ce umarnin kotuna kusan huɗu masu karo da juna game da babban taron zai iya jawo matsala game da halaccin duk wani mataki da ya biyo bayan taron.
Zuwa yanzu, akwai ƙararraki uku a gaban kotuna daban-daban waɗanda suka bayar da umarnin a dakata da shirin taron da kuma akasin haka, yayin da PDP ta ce tana ci gaba da shirin gudanar da shi a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamban nan.
Ministan Abuja Nyesom Wike, da tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido na cikin waɗanda suka kai jam'iyyar kotu kan taron.