Hukumomi a jihar Sokoto sun tabbatar da cewa aƙalla ƙauyuka sama da 28 sun zama kufai sakamakon ci gaba da hare-haren ƴan bindiga, musamman a yankunan da ake dangantawa da fitaccen jagoran ƴan bindiga Bello Turji, a yankinTidibale da wasu wurare da ke kewaye da shi a ƙaramar hukumar Isa.
Majiyoyi sun bayyana cewa mazauna ƙauyukan sun tsere ne bayan wani gargaɗi da ake zargin Bello Turji ya yi, inda ya umarci al’umma da su fice daga ƙauyukansu ko kuma su fuskanci kisa.
Ana danganta Turji da kisan mutane da dama da hare-hare masu muni kan fararen hula da jami’an tsaro a jihohin Sokoto da Zamfara.
Bayanan da BBC ta tattaro sun nuna cewa ƴan gudun hijra da suka fito daga yankin da lamarin ya shafa na cikin zullumi da fargaba, bayan rasa matsugunnansu.
Yawancinsu sun nemi mafaka ne a makarantun gwamnati a ƙaramar hukumar Isa da wasu ƙananan hukumomi makwabta.
Wani ɗan gudun hijra da ke sansani ya shaida wa BBC cewa,
“Sun kashe wasu, sun tafi da wasu, sannan suka yi mana gargaɗi cewa idan suka dawo suka tarar da mu, za su kashe kowa.”
Shugaban rundunar Adalci ta Ƙasa reshen jihar Sokoto, Bashar Altine Guyawa, ya ce yayin gargaɗin da Bello Turji ya yi wa mutanen Tidibale, an kashe mutum biyu da suka yi masa gardama.
“A lokacin da ƙaramar hukumar mulki ta samu labarin faruwar lamarin, nan take ta aike da motoci domin kwashe al’ummomin yankin zuwa cikin garin Isa,” in ji shi.
A nasa ɓangaren, mai bai wa gwamnan Sokoto shawara kan harkokin tsaro, Kanal Ahmad Abdul Usman (mai ritaya), ya ce gwamnatin jihar ta samu labarin abin da ya faru, amma har yanzu tana jiran cikakken rahoto daga jami’an tsaro da ke aiki a yankin tun bayan faruwar lamarin.
Jihar Sokoto dai ta daɗe tana fama da hare-haren ƴan bindiga, inda Bello Turji ke ci gaba da zama babban barazana ga tsaron jihar da ma jihohin da ke maƙwabtaka da ita a yankin arewa maso yammacin Najeriya.