Isra'ila ta umarci 'duka mazauna birnin Gaza' su fice daga birnin
Sojojin Isra'ila sun buƙaci mazauna birnin Gaza su fice daga yankin kudanci zuwa tsakiyar Zirin Gaza, yayin da suke ci gaba da kai hare-hare a arewacin yankin.
Wasu takardu da jirgin sama ya sako cikin birnin sun buƙaci duk wanɗanda ke zama a birnin Gaza su bar wurin da suka kira 'sansanin yaƙi mai haɗari' ta hanayr bin wasu tituna biyu da suka ce masu tsaro ne da za su kai mutanen yankin zuwa garuruwan Deir al-Balah da al-Zawaida.
Majalisar ɗinkin duniya ta bayyana damuwarta kan umarnin barin birnin da aka bayar kasancewar wannan ne karo na biyu da aka ɓukaci hakan tun fara yaƙin, inda ake buƙatar kowa ya fice.
Cikin mako biyu da suka gabata ne sojojin Isra'ila suka ƙara kunna kai cikin unguwanni da dama da suke ganin a nan ne mayaƙan Hamas da ƙungiyoyin Falasɗinawa masu ikirrain jihadi ke taruwa tun farkon shekarar nan.
Ƙungiyar Hamas ta ce sake ƙaddamar da hare-hare a birnin na barazana ga tattaunawar sulhu da aka fara ranar Laraba a Qatar domin tsgaita wuta da kuma batun sakin Isra'ilawan da take garkuwa da su.
Shugabannin hukumomin leƙen asirin ƙasashen Amurka da Masar da kuma Isra'ila da Firaministan Qatar na daga cikin masu halartar tarun sulhun.
Wani babban jami'in Hamas Hossam Badran ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa Isra'ila "na ƙoƙarin saka matsi kan yarjejeniyar ta hanyar kai hare-hare da ɗaiɗaita Falasɗinawa tare da aikata kisan kiyashi".
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya tabbatar da goyon bayan Isra'ila kan cimma yarjejeniyar, matuƙar ba a saɓa wa ƙa'idojinta a.