Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/07/2024

Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/07/2024

Taƙaitattu

  • NATO ta ce za ta ci gaba da tallafa wa Ukraine don ta zama mamba
  • Kotun Ƙolin Najeriya za ta yanke hukunci kan 'yancin ƙananan hukumomi
  • Isra'ila ta umarci 'duka mazauna birnin Gaza' su fice daga birnin
  • Ƙungiyoyin ƙwadago na duba yiwuwar amsa gayyatar Tinubu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Aisha Idris

  1. Ƙasashen Turai sun sanar da shirin murƙushe hare-haren Rasha

    Ƙasashen Turai sun sanar da shirye-shiryensu na murƙushe hare-haren Rasha a nahiyar.

    A rana ta uku na taron Nato a Washington, Faransa da Jamus da Italiya da Poland sun ce za su ƙirƙiri makamai masu linzami da ake harbawa daga ƙasa waɗanda za su iya tafiyar sama da kilomita ɗari biyar.

    Sun ce makaman za su cike giɓin da aka samu a tsaron ƙasashen Turai sakamakon mamayar Rasha a Ukraine.

    Romaniya da Bulgariya da Girka sun sa hannu kan wata yarjejeniya da za ta bai wa sojoji da makamai damar yin zirga-zirga cikin hanzari a sassan iyakokinsu.

    Rasha ta yi martani mai zafi ga alƙawuran ƙara samar wa Ukraine tallafin makamai, wani abu da ta ce babbar barazana ce ga tsaronta.

  2. Gwamnatin Zamfara ta taƙaita zirga-zirgar babur a faɗin jihar

    Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare ya sanya hannu kan dokar taƙaita zarga-zirgar babura a faɗin ƙasar saboda dalilai na tsaro.

    Gwamnan ya amince da matakin ne bayan shawarar majalisar tsaron jihar, kamar yadda sanarwar da mai magana da yawunsa Sulaiman Bala Idris ya fitar ranar Alhamis ta bayyana.

    "Dokar da gwamnan ya sanya wa hannu ta taƙaita zirga-zirgar babura daga ƙarfe 8 na dare zuwa 6 na safe."

    "An umarci jami'an tsaro su hukunta duk wanda aka kama ya saɓa wa dokar," a cewar sanarwar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa an ɗauki matakin ne domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma da kuma magance ƙalubalen tsaro da jihar ke fuskanta.

  3. An yi jana'izar sojojin Nijar da aka kashe a kwanton ɓauna

    An yi jana'izar dakarun Nijar da suka rasa rayukansu a wani harin kwanton ɓauna da wasu mahara dauke da makamai suka kai da yammacin jiya Talata a yankin Tahoua mai iyaka da kasar Mali.

    Wannan dai shi ne karo na biyu a cikin wannan mako da dakarun kasar ke fadawa tarkon maharan.

    Sai dai babu wata sanarwa da ta fito daga gwamnatin mulkin sojan kasar.

    Maharan sun kai harin ne a lokacin da sojojin ke sintiri a yankin kudu maso yammacin Nijar inda mazauna yankin suka ce an raunata wasu da dama.

    Tun 2012 Nijar ke fama da hare-haren ƴanbindiga masu da'awar jihadi, musamman yankin Tillaberi da ke kan iyakar kasar da Mali da Burkina Faso.

  4. Kotun Kano za ta ci gaba da shari’ar Ganduje

    Wata babbar kotu a jihar Kano ta yanke hukuncin cewa za ta ci gaba da sauraren shari’ar zargin almundahanar da ake yi wa shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje da matarsa Hafsat da wasu mutum shida duk da kasancewar ba su bayyana a kotun ba.

    Gwamnatin Kano ce ta shigar da karar tsohon gwamnan jihar inda take zarginsa da abubuwa da dama ciki har da cin hanci da rashawa, sai dai tun watan Mayun shekarar nan da aka shigar da karar mutum guda ne kadai cikin wadanda ake karar ya bayyana a kotun.

    Lauyan gwamnatin Kano, Adeola Adedife, ya gabatar da bukatu uku a gaban kotun, kasancewar wadanda ake karar ba su bayyana kotu ba.

    Bukatar farko da Adeola ya nema ita ce, kotu ta bayar da odar a kamo wadanda ake karar a kawo su gaban kotun tun da an wallafa takardar sammaci a jaridu kuma ba su bayyana a kotu ba.

    Ya kuma nemi a basu rana su fara gabatar da shaidu.

    Sai dai lauyan kamfanin Lamash Properties Limited Nuraini Jimoh ya soki wadannan bukatu, inda ya shaida wa kotun a madadin sauran wadanda ake karar cewa ai ba a basu takardar sammaci ba, sannan kuma ya soki takardar sammacin da aka baiwa kamfanin da ya wakilta.

    Ya shaidawa kotun cewa sun shigar da sukar cewa kotun bata da hurumin sauraron shari'ar inda ya nemi a fara sauraron bukatunkafin a saurari komai a zama na gaba.

    Sannan ya nemi kotun ta yi watsi da bukatun masu kara yana mai cewa za a fara sauraron gundarin shari'ar amma a cewarsa masu kara ba su nuna cewa a shirye suke ba.

    Daga nan ne kuma mai shari'a Amina Adamu Aliyu ta dage zaman tare da cewa sai karfe biyu za ta yi kwarya-kwaryar hukunci a kan bukatun da banagrorin suka gabatar, sannan kuma ta bayar da umarnin cewa kada lauyoyi su yi magana da 'yan jarida.

    Bayan mai shari'a ta dawo ne sai ta yi hukuncin cewa ta amince da bukatar masu kara na ci gaba da shari'ar tare da ayyana cewa tamkar an karantawa wadanda ake karar tuhume-tuhume ba su amince ba tare da fara gabatar da shaidu.

    Sai dai mai shari’ar bata amince da rokon a kamo wadanda ake karar ba. Sannan kuma kotun tace Nuraini Jimoh ba shi da hurumin yin magana a madadin wadanda basu bayyana a kotun ba tun da yana wakiltar wanda ake kara ne wato na shida kadai.

    Sai dai mai shari'a Amina Adamu Aliyu ta amince da bukatar da Nuraini Jimoh ya nemi na fara sauraron sukar da ya yi cewa kotun ba ta da hurumin sauraron shari'ar kafin kotu ta saurari komai tukuna.

    Mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta dage zaman kotun zuwa 23 da 24 ga watan Oktoban shekarar nan don fara sauraron gundarin shari’ar.

  5. Hukuncin Kotun Ƙoli kan ƙananan hukumomi babbar nasara ce - Atiku

    Jagoran adawa a Najeriya kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya ce hukuncin da Kotun ƙoli ta zartar kan tabbatar da ƴancin ƙananan hukumomi babbar nasara ce ga ƴan Najeriya.

    Atiku ya yaba da hukuncin ne a bayanin da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis.

    Atiku ya ce hukuncin Kotun Ƙoli mataki ne a tafarkin da ya dace kuma babban gyara ne ga tabbatar da ci gaba a sassan ƙasar.

    Jagoran adawar ya ce matakin haɗa kason kuɗaɗen jiha da na ƙananan hukumomi ya samo asali ne daga son rai na siyasa.

    "Na goyi bayan matakin Kotun Ƙoli cewa tsarin gwamnati ya kafu ne a mataki uku, kuma ƙananan hukumomi ne ya kamata su kasance cibiyar tabbatar da ci gaba," a cewar Atiku.

    Ya ƙara da cewa hatta kuɗaɗen shiga da ƙananan hukumomin ke samarwa su kasance sun tafi kai-tsaye zuwa asusunsu

  6. Hamas ta ce ta gano gawawwakin mutum 60 a Gaza

    Hukumar tsaro ta civil defence da ƙungiyar Hamas ke tafiyar da ita a Gaza ta ce ta gano gawawwaki kusan sittin a lardin Shujaiya bayan janyewar dakarun Isra'ila.

    Ana tunanin akwai ƙarin gawawwakin da ƙasa ta danne bayan da gine-gine suka ruguje.

    Rundunar sojin Isra'ila wadda ba ta ce komi ba kan iƙirarin, a ranar Laraba, ta ce ta kawo ƙarshen ayyukanta a Shujaiya amma tana ci gana da kai farmaki a wasu sassan na Gaza bayan umartar jama'a su fice.

    Masu shiga tsakani domin ganin Isra'ila ta tsagaita wuta na gab da zuwa birnin Alƙahira domin ci gaba da tattaunawa bayan dawowarsu daga wata tattaunawar a Qatar.

  7. Tinubu ya yaba da hukuncin Kotun Ƙoli kan ƴancin ƙananan hukumomi

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yaba da hukuncin Kotun ƙoli da ta tabbatar da ƴancin ƙananan hukumomi.

    A sanarwar da fadar shugaban ta fitar bayan hukuncin a ranar Alhamis, shugaban ya ce hukuncin tamkar jaddada matsayin ƙaramar hukuma ne a kundin tsarin mulki.

    A hukuncinta na ranar Alhamis, Kotun Ƙolin Najeriya ta ce iko da kuɗaɗen ƙananan hukumomi da gwamnoni ke yi ya saɓa wa kundin tsarin mulki.

    Alƙalin da ya jagoranci hukuncin Emmanuel Agim ya ce ƙananan hukumomi 774 na Najeriya su ke da haƙƙin tafiyar da kuɗaɗensu da suke samu daga kason tarayya.

    Shugaba Tinubu ya ce wannan mataki ne da ya tabbatar da matsayin ƙaramar hukuma a matsayin ɓangare na gwamnati da kuma tabbatar da shugabanci nagari.

    Ya ce rashin sakin mara ga ƙananan hukumomi babbar matsala ce ga ci gaban ƙasa musamman yadda ba a jin tasirin gwamnati a karkara.

  8. Tinubu ya gana da shugabannin kwadago

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago a fadarsa a Abuja.

    Shugaban ya ce yana buƙatar lokaci kafin ya aika da ƙudirin neman ƙarin albashi mafi ƙanƙanta zuwa Majalisar Tarayya.

    Sai dai bayan ganawar, shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC Joe Ajaero, ya ce suna nan kan bakarsu ta neman N250,000 a matsayin albashi mafi ƙanƙanta ga ma'aikatan Najeriya.

    Ya ce tattaunawa suka yi da shugaban amma ba sasanci ba kan batun ƙarin albashin.

    "Mun amince mu koma mu yi nazari kafin makon gobe," in Kwamred Ajaero.

    Da aka tambaye shi game da matsayarsu kan N250,000 sai ya ce "ba mun tafi ba ne mu yi ciniki amma muna nan kan bakarmu har sai mun kammala tattaunawa.

    Sai dai karamar ministan ƙwadago Nkeiruka Onyejeocha ta ce an yi tattaunawa mai ma'ana tsakanin shugaban ƙasa da kuma shugabannin na ƙwadago.

    Ta bayyana fatan za a daidaita nan ba da jimawa ba.

  9. Shin ƙirƙirarriyar basirar AI za ta ƙwace wa mutanen Afirka aiki?

    Wasu na kallon ƙirƙirarriyar basira a matsayin wani abin tsoro, wadda za ta sanya na'ura ta ƙwace wa ɗan'adam aiki da kuma ƙwace harkar tafiyar da lamurran duniya.

    Mece ce gaskiyar hakan? Shin akwai yiwuwar basirar AI za ta iya warware wasu matsaloli da kuma ƙarfafa matasa?

  10. Shugabannin ƙwadago sun isa fadar shugaban ƙasa don ganawa da Tinubu

    Shugabanin gamayyar ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya sun isa fadar gwamnatin ƙasar, domin ganawa da shugaban ƙasar Bola Tinubu.

    Shugaban ƙasar ne dai ya gayyaci jagororin gamayyar ƙungiyoyar ƙwadagon zuwa fadarsa domin tattaunawa kan batun mafi ƙanƙantar albashi da aka kasa cimma matsaya akai.

    Ƙungiyoyin ƙwadagon da gwamnatin Najeriya dai sun jima suna kai ruwa rana kan mafi ƙanƙantar albashin ma'aikata a ƙasar.

    Tun da farko dai gwamnatin Najeriya ta yi wa kungiyar ƙwadagon tayin naira 62,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi, yayin da kungiyoyi ƙwadago suka ce suna buƙatar gwamnati ta biya naira 250,000.

  11. Rasha ta yi kakkausan gargaɗi kan ƙudurin Nato na tallafa wa Ukraine

    Rasha ta mayar da martani mai zafi kan alƙawarin da ƙungiyar tsaro ta Nato ta yi a taronta da ke gudana na samar wa Ukraine tallafin makamai.

    Kakakin Fadar Kremlin, Dmitry Pescov ya shaida wa manema labarai cewa matakin babban barazana ne ga tsaron Rasha, yana mai cewa Moscow za ta mayar da martani ta hanyar abin da ya kira ''ɗaukar matakan da suka dace'' domin daƙile duk wata barazana.

    Mista Pescov ya yi gargaɗi kan jigilar kayayyakin aikin sojin da Nato ke yi a kusa da kan iyakokin Rasha.

    Shi ma tsohon shugaban ƙasar Rasha, ya yi kakkausan gargaɗi kan matakin shigar da Ukriane cikin NATO, yana mai cewa hakan ba yi wa Ukraine da Naton daɗi ba.

  12. Shugaban Kenya ya kori ministocinsa

    Shugaban ƙasar Kenya, William Ruto ya rusa majalisar zartarwarsa, in ban da mataimakin shugaban ƙasa, Rigathi Gachagua da sakataren majalisar Musalia Mudavadi.

    Mista Ruto ya ce ya ɗauki matakin ne bayan abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, da suka sa shugaban ya janye ƙudurin ƙarin kuɗin haraji.

    Ƙudurin harajin dai ya janyo zazzafar zanga-zanga da ta haddasa mutuwar fiye da mutum 20.

  13. Burkina Faso ta haramta auren jinsi

    Burkina Faso ta kasance ƙasar Afirka ta baya-bayan nan da ta haramta auren jinsi.

    Gwamnatin mulkin sojin ƙasar ce ta sanya hannu kan dokar a lokacin taron majalisar zartaswar ƙasar.

    Ministan shari'a na ƙasar Edasso Rodrigue Bayala ya ce sabuwar dokar ta amince ne da auren al'ada da na addini kawai cikin kundinta.

    Za a miƙa dokar ga majalisar ƙasar domin saka hannu kafin shugaban mulkin sojin ƙasar, Kaftin Ibrahim Traore ya tabbatar da ita.

    A watan Mayun shekarar da ta gabata ne, Uganda ta zama ƙasar Afirka ta baya-bayan nan da ta ɓullo da ɗaya daga cikin dokoki mafiya tsauri kan auren jinsi a duniya.

  14. Kotun ta yanke wa ɗan TikTok hukuncin shekara shida kan zagin shugaban ƙasa a Uganda

    Wata kotu a Uganda ta yanke wa wani matashi mai shekara 24, hukuncin ɗaurin shekara shida bayan samunsa da laifin zagin shugaban ƙasar da iyalansa a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na TikTok.

    An kama Edward Awebwa da laifin furta kalaman ƙiyayya tare da yaɗa bayanan da ba na gaskiya ba, da ke ɓata sunan shugaban ƙasar Yoweri Museveni da matarsa Janet Museveni da kuma ɗansu Muhoozi Kainerugaba wanda shi ne shugaban rundunar sojin ƙasar.

    Haka kuma kotun ta samu bayanan cewa Awebwa ya yaɗa bayanan cin fuska, inda yake cewa za a samu ƙarin kuɗin haraji ƙarƙashin mulkin shugaba Museveni.

    Mista Awebwa ya amsa laifin, tare da neman afuwa a gaban kotun.

    To sai dai alƙalin kotun ya ce duk da matashin ya nemi afuwa, yanayinsa bai nuna ya yi nadamar abin da ya aikata ba kuma kalaman da ya yi amfani da su babu ɗa'a a ciki.

    "Wanda ake zargi ya cancanci hukuncin don kauce wa aikata irin wannan laifi na rashin nuna girma ga shugaban ƙasar da mai ɗakinsa a nan gaba ba.

  15. Abin da za ku yi don cin ribar yawan al'ummar duniya

    A wani ɓangare na Ranar Yawan Al'umma ta Duniya, mun yi nazari kan gudunmawar da kowa zai iya bayarwa don ganin yawanmu a duniya ya zama mai amfani da kyautata rayuwa.

    Akan tuna da ranar ne a duk 11 ga watan Yuli, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ware.

    Zuwa yanzu, MDD ta yi ƙiyasin mutanen duniya sun kai biliyan 8,120,886,000.

  16. Kotun Koli ta hana gwamnonin Najeriya rusa shugabannin ƙananan hukumomi

    Kotun Ƙolin Najeriya ta haramta wa gwamnonin jihohin ƙasar rusa zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi a faɗin ƙasar.

    A hukuncin da ta yanke ranar Alhamis kotun ta ce rusa zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar.

    Ministan shari'ar ƙasar ne ya shigar da ƙara a gaban kotun a madadin gwamnatin tarayya, inda ya buƙaci kotun ta hana gwamnonin jihohin rusa zaɓaɓɓun shugabannin ƙanann hukumomin.

    Tun da farko, gwamnonin jihohin ƙasar 36, sun nuna adawa da ƙarar da gwamnatin tarayyar ta shigar.

  17. Kotu ta samu gwamnatin Najeriya da laifin take haƙƙin bil-adama lokacin zanga-zangar EndSars

    Kotun ECOWAS ta samu gwamnatin Najeriya da laifin take haƙkin wasu mutum uku a lokacin zanga-zangar lumana ta EndSar a 2020 a birnin Legas.

    Kotun ta cegwamnatin Najeriya ta saɓa wa sashe na 1 da 4 da 6 da 9 da goma na kundin kare haƙƙin bil'adama na Afrika, musamman kan ƴancin rayuwa da kariya da faɗin albarkacin baki da na rayuwa da hana azabtarwa.

    Masu shigar da ƙarar da suka haɗa da Obianuju Udeh da Perpetual Kamsi da Dabiraoluwa sun zargi jami'an tsaron gwamnatin Najeriya da take haƙƙinsu a lokacin zanga-zangar lumana ta EndSars a babbar gadar Lekki da ke birnin legas a ranar 20 ga watan Oktoban 20220.

    To sai dai alƙalin kotun, Mai Shari'a Koroma Sengu ya yi watsi da zargin take ƴancin rayuwa na masu shigar da ƙarar.

    Amma ya ce dole ne gwamnatin Najeriya ta biya kowanne a cikinsu naira miliyan 2 a matsayin diyyar take ƴancinsu na kariya da azabtarwa da na faɗin albarkacin baki da sauran 'yancinsu.

    Haka kuma alƙalin ya ƙara da cewa, dole ne gwamnatin ƙasar kamar yanda kundin kare haƙƙin bil'adama na Afrika ya tanadar ta yi bincike tare da hukunta jami'anta da ke da hannu a cin zarafin tare da kawo wa katu rahoton yadda ta aiwatar da hukuncin da kotun ta zartar a watanni shida masu zuwa.

    Masu shigar da ƙarar sun zargin cewa a lokacin zanga zangar lumana - don kawo ƙarshen cin zarafin da jami'an 'yan sandan SARS a babbar gadar Lekki a ranar 20 da kuma 21 ga watan Oktobar 2020 - waɗanda ake ƙarar sun aikata laifukan take haƙƙin bil'adama da dama.

  18. Kotun Ƙolin Najeriya ta ce gwamnoni su daina riƙe kuɗin ƙananan hukumomi

    Kotun Ƙolin Najeriya ta ce riƙe kuɗin ƙananan hukumomi da gwamnaonin jihohin ƙasar ke yi ya saɓa wa kundin tsarin mulki.

    Cikin hukuncin da ta yanke kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Emmanuel Agim, ya ce kotun ta fahimci cewa gwamnatocin jihohin ƙasar sun shafe fiye da shekara 20 ba tare da sakar wa ƙananan hukumomin mara ta fuskar kuɗaɗensu ba.

    Alƙalin kotun ya ci gaba da cewa tun tsawon wanan lokaci, ƙananan hukumomin ba sa samun kuɗaɗen da ya kamata su samu daga gwamnonin jihohin ba, waɗanda ke kashe kuɗin ta hanyar yin ayyuka a madadin ƙananan hukukomin.

    Mai shari'a Agim ya ce dole ne ƙananan hukumomin ƙasar 774 su riƙa amfani da kuɗaɗensu da kansu ba tare da sa katsalandan daga gwamnonin jihohi ba.

    Haka kuma alƙalin ya yi watsin da ƙorafin da gwamnonin suka yi ta bakin lauyoyinsu.

    Gwamnatin tarayyar ta kuma buƙaci kotun ta dakatar da gwamnonin jihohin ƙasar, daga rushe zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin.

  19. Biden na ci gaba da shan matsin lamba don ya haƙura da takara

    Wani ɗan majalisar dattawan Amurka ya bi sahun ƙarin ‘yan jam’iyyar Democrat a majalisar wakilan ƙasar da ke kira ga Shugaba Joe Biden ya haƙura da takarar shugabancin ƙasar.

    A wani rubutu da ya yi a jaridar Washington Post , Peter Welch, wanda ya fito daga jihar Vermont ya ce kamata ya yi Mista Biden ya janye daga takarar domin amfanin ƙasar.

    Ya yi kiran ne ‘yan sa’o’i bayan da ɗaya daga cikin manyan masu bai wa jam’iyyar Democrat tallafin kuɗi ya yi makamancin kiran.

    Peter Welch shi ne ɗan majalisar dattawa na farko kuma ɗan majalisar dokokin Amurka na goma daga jamiyyar Democrat da ya fito fili ya buƙaci Shugaba Biden da ya janye daga takarar.

    Duk da ya yi nuni ga irin girmamawa da mutunci da kima da ya ce yana gani na shugaban, to amma kuma ya yi nuni ga irin rashin katabus da shi ma yake ganin, Mista Biden ya yi a lokacin muhawararsu da abokin hamayyarsa Donald Trump.

    Yana mai cewa abu ne da Amurka ba za su kasa gani ba – kuma masu kaɗa ƙuri’a ba za su iya kawar da kai ko watsi da abin da ya fito ƙarara a wannan dare ba.

    Sanatan ya ce, ‘yan jam’iyyar Democrat za su fuskanci ta’annatin siyasa a watan Nuwamba, idan Biden ya ci gaba da zama dan takararsu.

    Mista Welch ya ƙara da cewa yana ganin mataimakiyar shugaban kasar Kamala Harris za ta dace da shugabancin.

    Tun da farko tauraron fim ɗin nan kuma darakta a fina-finan Amurka - wanda kuma babban mai bai wa jamiyyar Democrat tallafin kudi ne - George Clooney shi ma ya yi gargaɗin cewa jam’iyyar ba za ta iya cin zaɓe ba, matsawar Biden ne ɗan takarar a watan Nuwamba.

    A wani taron tara wa jamiyyar kuɗi da aka yi kwanan nan, mista Clooney ya ce, shugaban ya sauya daga ɗan siyasa mai karsashi da kuzari da yake a da, yanzu yana nan kamar yadda ya kasance a lokacin muhawara da Donald Trump, lamarin da ya janyo ake nuna damuwa a kan shekarunsa.

    Tauraron fim ɗin ya ƙara dacewa duk wani ɗan majalisar dokoki da ya yi magana da shi ya yarda da abin da ya ce, ko ma me shi ɗan majalisar yake faɗa a bainar jama’a.

    Ita ma dai tsohuwar shugabar majalisar wakilan Amurka, Nancy Pelosi kusan ta fara dawowa daga rakiyar Mista Biden a fakaice, tana karkata ga masu ra’ayin ya haƙura da takarar.

    A wata hira da tashar talabijin ta MSNBC ta yi da ita, ta ce ya rage wa Shugaban ya yanke shawarar abin da ya kamata ya yi, saboda lokaci na ƙurewa.’

  20. Ƙungiyoyin ƙwadago na duba yiwuwar amsa gayyatar Tinubu

    Shugabannin haɗakar ƙungiyoyin kwadago a Najeriya na duba yiyuwar amsa gayyatar da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya yi musu zuwa fadarsa don tattauna batun mafi ƙanƙantar albashi.

    Tun da farko shugaban ƙasar, Bola Tinubu ne ya aike wa shugabannin ƙungiyoyin wasiƙa buƙatar tattaunawa da su a fadarsa a yau Alhamis kan mafi ƙanƙantar albashin ma'aikata da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a ƙasar.

    To sai dai wata majiya daga ƙungiyar NLC ta shaida wa BBC cewa ƙungiyoyin ƙwadagon sun samu gayyatar da shugaban ƙasar ya yi musu, kuma shugabanninsu za su zauna domin yin nazarin wasiƙar gayyatar da shugaban ƙasar ya yi musu.

    Majiyar NLCn ta ce idan shugabannin nata suka zauna za su tattauna tare da yin nazarin wasiƙar shugaban ƙasar, domin duba yiyuwar amsa gayyatar ko akasin hakan.

    Ƙungiyoyin ƙwadagon da gwamnatin Najeriya dai sun jima suna kai ruwa rana kan mafi ƙanƙantar albashin ma'aikata a ƙasar.

    Ita dai gwamnatin Najeriya ta yi wa NLC tayin biyan naira 62,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashin, yayin da ita kuma NLC ke buƙatar gwamnatin ta biya naira 250,000.