Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

AFCON 2025: Najeriya 2-1 Tanzaniya

Wannan shafi ne da ya kawo muku bayanai kan wasan Najeriya da Tanzaniya a gasar kofin nahiyar Afirka ta 2025 da ake yi a Moroko.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Ibrahim Mohammed, Isiyaku Muhammed

  1. Ana zabga ruwa a filin wasa, Najeriya 1-0 Tanzaniya

    Ana zagba ruwan sama a filin wasan da Najeriya ke karawa da Tanzaniya, lamarin da ya sanya wasu masu kallo suka tashi daga gaba-gaba, suka koma neman wurin da za su fake wa ruwa.

    Sai dai ƙwallon da Najeriya ta zura ta fi musu dukan ruwan, inda wasu suka tsaya a cikin ruwa suna rawa suna kaɗa tutar Najeriya da ta Moroko.

  2. Goaaaal! Najeriya ta zura ƙwallo, Najeriya 1 - 0 Tanzaniya

    Najeriya ta zura ƙwallo a ragar Tanzaniya a minti 35 da take wasa.

    Ɗan wasan baya na Najeriya da ke taka leda a ƙungiyar Hull City da ke Ingila Semuel Ajayi ya zura ƙwallon da kai, kamar rago!

    Wannan ita ce ƙwallo ta 147 da Najeriya ta zura a gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta Afirka, a tarihi.

    Tun da farko, Osimhen ya zagaye gola, sannan ya yi yunƙurin zura ƙwallon, amma ɗan wasa bayan Tanzania ya tare.

  3. , Nigeria 0-0 Tanzaniya

    Ademola Lookman na ƙungiyar Atalanta ya ɗauki bugun tazara wadda ta fice daga fili.

    Victor Osimhen ne ya samo bugun ta ɓangaren hannun dama bayan wuce tsakiya a ɓarayin Tanzaniya.

  4. Tanzaniya na dannawa, Nigeria 0-0 Tanzaniya

    Sunday Oliseh ya ce:

    A bayyana take Tanzaniya na so su yi wa Najeriya tsiya.

    Suna tattaɓawa ba laifi, suna matsawa gaba.

    Suna amfani da salon 4-4-2, lamarin da ya sa suke iya taka wasa a natse.

  5. , Nigeria 0-0 Tanzaniya

    Victor Osimhen ya sharara wani shot da nufin zura ƙwallo sai dai ƙwallon ta bauɗe nesa da raga ta hannun dama.

    Osimhen da Ademola Lookman su ne suka fi kowa zura ƙwallo tsakanin ƴan wasan Najeriya a lokacin neman gurbi, kowannensu ya zura ƙwallo bibbiyu.

  6. ƘIRIS!, Nigeria 0-0 TanzaniYa

    Ɗan wasan Najeriya Akor Adams ya kusa zura ƙwallo bayan samun fasin daga Samuel Chukwueze.

    Amma golan Tanzaniya Zuberi Foba ya hana ƙwallon shiga raga.

  7. , Nigeria 0-0 Tanzaniya

    Tanzaniya ta samu damar yin barazana bayan ta samu bugun tazara a bakin gidan Najeriya sanadiyyar fawul ɗin da Calvin Bassey ya haifar.

    Amma mai tsaron gidan Najeriya Stanley Nwabali ya cafke ƙwallon, caraf.

  8. An fara wasa, Najeriya 0-0 Tanzaniya

    Tsohon ɗan wasan Najeriya kuma tsohon mai horas da tawagar Super Eagles Sunday Oliseh ya ce wannan wasa na da matuƙar muhimmanci ga Najeriya.

    "Dole ne mu yi wasan. Dole ne mu tabbatar mun yi nasara.

  9. Najeriya da Tanzaniya

    • Najeriya da Tanzaniya sun taɓa karawa a gasar cin kofin Nahiyar Afirka a shekarar 1980, inda Najeriya ta yi nasara 3-1 a karawar farko ta gasara a birnin Legas
    • Ƙwallon ɗaya tilo da Tanzaniya ta ci a wasan ta ƙafar ɗan wasa Juma Mkambi ita ce ta farko da ƙasar ta fara ci a gasar Afcon a tarihi
    • Najeriya ta yi nasara a wasanni 13 cikin karawa 20 na farko a gasar Afcon da ta buga a baya, inda ta yi rashin nasara sau 5.
  10. Me magoya bayan Najeriya ke cewa?

    BBC ta tattauna da wasu masoya ƙwallon ƙafa a bakin filin wasan sa Najeriya za ta kara da Tanzaniya.

  11. Barka da warhaka!

    Barkan ku da zuwa shafinmu wanda zai kawo muku yadda take kasancewa a karawar Najeriya ta farko a gasar cin kofin Afirka na 2025 da ke gudana a ƙasar Moroko.

    Karawar yau tsakanin Najeriya da Tanzaniya za ta gudana ne a birnin Fes.

    Shin Najeriya za ta doke Tanzaniya ko Tanzaniya za ta bai wa Super Eagles mamaki?

    Nawa kuke ganin za a tashi a yau?

    Da fatan za ku kasance da mu daga farko har ƙarshe domin ganin yadda za ta kaya.