Dan takarar LP, Olorunfemi ya kaɗa ƙuri'arsa
Dan takarar gwamnan na jam'iyyar LP, Festus Ayo Olorunfemi ya kaɗa ƙuri'arsa.
Olorunfemi ya kaɗa ƙuri'arsa a rumfar zaɓe mai lamba 8, a ƙaramar hukumar Akoko North West da ke jihar.
A ranar Juma'a ne hukumar zaɓen ƙasar INEC ta sanya sunansa cikin jerin 'yan takara bayan hukuncin wata kotu da ya buƙaci a sauya Olusola Ebiseni.